AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Insha ALLAH yanxun inmunyi la’asar zamuje adakkota tana gd”cewar Abba Yana duk’ar da Kai sbd ganin yadda mom ke jifansa da kallon tuhuma”
Gyaran murya Dr naja’at ta yi hade da cewa inada shawara Alh!
Abba yadubeta ya ce miye shawarar likita?
Gsky ciwon danku bana asibiti bane,ayadda na fahimta,ciwonsa na….ah ah dakata bamasan Jaye Jaye tunda kun kasa gane abinda ke damunsa inkun sallamesa zamu can za hospital ko mufitar dashi waje..cewar mom tana tashi tsaye.
Murmushi Dr naja’at ta yi domin yanxun ta lura mom ta daina Mata kallon sani,Kuma itama bazata nuna ta Santana,sai kawai tace to shikenan hjy ALLAH yasa adace” cikin Shan k’amshi mom ta ce Amin”sbd azatonta k’ila Dr naja’at ta ji shakkuntane…
Atare mom da Abba suka fice dg office d’in Dr naja’at.
Hafiz dke cikin toilet d’in office d’in yyi ajiyar zuciya sbd yaji komai ,ya fito zuciyar sa cike da tausayin abokin nasa.
Saurin dubarsa ammi tayi had’e da hararan sa tace har kabani tsoro,miye anfanin hakan kamana labe?
Murmushi Hafiz yyi had’e da cewa yi hkri ammi inason jin abinda ke damun AK ne”
Ok to kaje gd hakan nan tunda kaji,tun safe kake nan ,itama fiddausi yakama ta kaduba kaga halin datake ciki”
Zan tafi ammi Amma Dan ALLAH Zan tambayeki?”
Ina jinka “miye tsakanunku d hjy hafsat (mom) mahaifiyar Abdallah?”
Murmushi ammi tayi had’e da cewa meyasa kamun wannan tambayar?
Nan yashiga sanar Mata yadda mom ta tambayesa akan ta…..ajiyar zuciya ammi tayi had’e da cewa Zan sanar dakai wacece HASSU TSIYA TSABA! amma ba yanxunba ,abinda nikeso dakai kada ka nuna Mata cewa nice naja’at Musa,kanajiko?”eh ammi
Ok zaka iya tafiya…
*******
Abba d mom na fita takama balbalesa da masifa akan wane dalili zai ce Abdallah nada iyaline?”
Girgiza Kai yyi Kai tsaye yace basa abinci ,wanka , alwalla,kulada abinda yashafi tsiraicinsa ke Zaki kula Masa da sune?”
Tabe baki mom tayi had’e da cewa eh hakane muje to sai akawota nan d’in”ta fad’a. Cike da mamakin Wai yau Abba ke gaya Mata mgn a tsaye lallai da sake….
Saida suka sake zuwa d’akin da akaje Abdallah ,suka samu Yana bacci ga drip an d’aura masa
Kafin su fice dg room d’in sukabar ya’u direba agunsa….
Byn Abba yyi Sallah suka nufi gd shida mom…
Byn mom tayi wanka tasaka zulfa ayi Mata Kiran riyan.
????????????????????????????????????????
???? AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????
Story & written
by mmn fareesa
Not edited
p 26
Riyan na zaune kan abin Sallah yana azkar,byn ta idar da sallar la’asar wacce ta dad’e tanama Abdallah addua ,kafin ta soma azkar yyinda k’asan zuciyarta ke tunanin Yaya jikin Abdallah da sauk’i ko bbu?”
Knocking d’in da taji ne yasaka cewa ashigo…byn zulfa ta shigo tasanar da ita Aiken mom kafin ta fice…
Tab’e baki Riyan tayi had’e da tashi ta ajiye cazbaza d’in,kafin ta fice ta nufi part d’in mom.”,,,,,
Fuska bbu yabo bbu fallasa tayi sallama had’e da Zama kan carpet tace ganiiii!
Cike da mamaki mom ke dubarta sbd ta lura dg yau da safe zuwa yanzun wani hayak’in rashin kunya ko me Riyan keji,Amma sai Bata nuna mamakin ta,tadaiyi kwafa azuciyarta sbd gab riyan din take da barin gdn…
Ayatsine tace abinda Zan gaya Miki shine kishirya yanzun ki dauki abinda zaku iya bukata keda my son” acikin driver’s din my son wani zai kaiki hospital gurnsa ki kula dashi kafin muzo anjima nida abbansa!
To insha ALLAH”riyan ta fad’a had’e da tashi ta fice”mom ta rakata da harara…
Bbu bata lokaci riyan ta shirya cikin doguwar riga ta amfa red tasaka hijab red,kafin ta fito taje bed room d’in Abdallah ta fito Masa da kayansa irinsu vest boxers jallabiya sbd tasan be wuce su mom take nufi ta fito Masa dashiba…. sannan ta Kira Hafiz tasanar Masa su had’u a asibiti “yace to…
Basu iso abitinba sai kusan 5:12pm "har room d'in da Abdallah ya ke driver d'in yanunama riyan , sannan ya tafi"cikin faduwar gaba ta murd'a kofar tashiga,bakin ta d'auke da sallama.... Hafiz ya amsa Yana kallon ta "byn sun gaisa ta ce yamai jikin?Yadubi Abdallah dake jingine da pillow bisa gado yace da sauk'i...
Matsowa tayi jikin gadon tana kallonsa tace yajikin?” ALLAH ya baka lfy” k’uri da ido yyi Mata Yana hongo tsantsar tausayinsa acikin k’wayar idonta,Wanda be tsammaci hakanba,azatonsa k’ila ma tace dole sai yasaketa Amma gashi ita rashin lafiyarsa tadameta….Yaya Hafiz ya ci abinci kuwa da wanka da Sallah???
Tambayar da riyan tayi ta sakashi dawowa tunaninsa,yanadaita aikin kallonsu..
“Ahankali Hafiz yace ah ah be jima da falkawaba ai”dama fresh milk ce da tea akace mu basa to komai dai akwai shi”to bara na had’a Masa tea din sai yyi Sallah da wanka.
Ok toshiken, Hafiz ya fad’a had’e da matsawa kusada Abdallah sbd byn farfadowarsa Yana Masa nasiha akan ya rungumi k’addararsa,dadai nasiha anan yafahimci yanajin mgn ,bede iyayinta”
Ahankali yace my man inason in sanar da Kai wata shawara Dan ALLAH inbacin nida riyan kada ka nunawa kowa kanajin mgn,inafatan kagane?”
Da ido Abdallah yace sbd me?
Hafiz yace Zan fad’a maka Amma da sauran lokaci… adedenan riyan ta iso da cup d’in tea mai kauri a hannunta ta dubi Hafiz tace gashito”
Gira ad’age yace nayime dashi?”
Kabashi yasha Mana”
Ke Kuma kiyi me Inna basa?”haba riyan! aike yakamata kibasa kinji”
Batace komaiba,taja kujerar roba Fara dake cikin d’akin ta matsa sosai kusada Abdallah dukda tanajin faduwar gaba ,haka ta daure, Hafiz ya d’ago kansa”had’e da bud’e Masa Baki har ya shanye duka Yana kallonsu da ido,kafin ta sake fito da fresh milk itama ta dura nasa , sannan ta basa ruwa yasha …
Byn kamar minti12 , Hafiz ya fice dg room d’in”
Bbu jumawa yadawo shida wani doctor da keke me kujera suka Kama Abdallah suka aza akai”Hafiz ya shige dashi toilet sbd yyi arwala ya Rama sallolin dake akansa tunda Yana a haiyacinsa.
Bayan shigarsu riyan ta gyare gadon had’e da share room d’in sbd tasan Abdallah bayason k’azanta.
Bata jima da gamawaba suka fito, Hafiz ya saitashi ga alk’ibla yaga batarda Sallah dg zaune sbd lalurarsa…
Bayn ya idar ne Hafiz ya turasa acikin toilet , yafito Yadubi riyan yace kije kiyi Masa wanka”Amma kibi ahankali kada yashaki sabili inkin gama Masa ki fito ,sai nazo na fito da shi”
Zaro ido riyan tayi had’e da cewa wankafa?”girgiza Kai Hafiz yyi had’e da cewa eh riyan ai mijinkine ko?”Kuma akwai boxer ajikinsa….batasan sadda tasaki ajiyar zuciya ba.
Duk anacikin wani hali Saida hafis ya murmusa.
Kafin ta shige toilet d’in atsorace.
Zaune yake kan keken idonsa arufe,sbd jin k’arar bud’e kofar yasan itace saiyai maza ya rufe idonsa,dukda yasan akwai boxer ajikinsa sai yaji nauyin tagansa ahaka musammun sai yadda tayi dashi….wani imani yaji yasake shigarsa lallai rayuwa abun tsoroce “Wai ita wace irin mutumce yanxun duk rashin kwautatawar da yyimata ,bazaisa ta cusguna masaba kota goranta Masa sbd yanzun Yana k’asa..
Wata zuciyar tace sbd ita daban take”Kuma zuciyarta tsarkakakkace tasan ko ita Bata wuce ALLAH ya jarabetaba…..tunaninsa ya tsaya cak sbd jin hannunta da soso ajinsa tana murzawa….
Kofar toilet d’in aka Fara budewa ,kafin ta turosa akan keken,da Abba suka hade ido yyi tagumi cike da tausayi yake dubarsu…
Hafis ne yatashi yataimaka Mata suka saukeshi dg kan keken suka aza kan bed.
Kafin Abba yadubeta fuska asake yace sannu !kinji ALLAH yyimiki albarka yabaki ladar”
Fuska aduke tace Amin.
Abba ya matsa kusada da Abdallah ya rungumesa Yana Masa adduar samun lfy had’e da nasiha akan ya yadda da k’addara “
Kallon sa Abdallah keyi yanason yace Masa Ina mom?”ai azatonsa bazata iya yin nesa dashi Kona na 1minit ba Yana cikin wannan halin”ALLAH sarki riyan ! yarinyar dayake wulakantawa gashi ita tafimasa mahaifiyarsa,sai yanzun ya tunada da nasihar Hafiz agaresa daya ke Masa fadan yadaina wulakanta riyan sbd D’an Adam darajace dashi bakasan Wanda zai maka Rana ba!gashi yagani ya wulakanta ita Kuma ta taimakaesa…. lallai bazai tab’a mantawa da Hafiz da riyan arayuwarsaba , wadanda yatabbatar bbu wad’anda mahaifiyar sa ta tsana sama dasu arayuwarta… wasu hawayene masu zafi na tausayin kansa suka Fara ziraromasa agefen ido….