AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin dubara Hafiz ya goge Masa sbd kada Abba yagani.

Da taimakon Abba da Hafiz aka shirya Abdallah cikin t shirt da wanso 3 quarter…

Gab da magrib ,Abba da Hafiz suka fice zuwa masjid,sukabar Riyan agunsa ita kadai.

Itama alwarlal tayi bayn ta saita Abdallah dake kan keke a alk’ibla.

Bayan sun idar ,riyan na kan abin Sallah tana lazimi kafin lokacin isha’i yyi.

Afusace aka banko kofar ,bbu ko sallama.

Da sauri riyan ta d’ago kanta Dan ganin su wayene.

Zeenat ce da hjy ikilima,suna jifar riyan da mugun kallo.

Wani faduwar gaba riyan ta ji Amma saita dake.

Abdallah na…..

Share

BY
MMN FAREESA.
????????????????????????????????????????

????AUREN WATA SHIDDA????

????????????????????????????????????????

Story & written by
Mmn fareesa

Wannan shafin nakune y’an team d’in HASSU TSIYA TSABA….lolx..????????

Not edited❌

P 27

Abdallah na kallonsu “Yana jiran jin meyakawo ne”yyinda riyan ta maida Kai tacigaba da abinta take batace uffanba….hmmm dole ki sunkuyar dakai Mana marar kunya”ko kinmanta ranar da kikamun gwalo sbd wannan nakashashshan mjin naki”?ok na mantafa Ashe auren contract nefa…cewar zeenat tana nuna Abdallah dake sauronsu yyi jigum tamkar gunki.
Hjy ikilima ta karbe zancen da cewa ai gara dabaki auresaba wlh “dayanzun anbarki da jinya ,yazamana Baki amfana da komaiba a auren nasa dakikayi…. ALLAH ya tsareni mom da Zama da nakashashshe,ai wlh ko ya aureni yazama haka dole yarabu Dani,dama inasonsane sbd kyau, aji.dakuma nassaba,to Kuma yanzun bbushi…hmmm yo insuke ai inhar basu yi sannuba abinda suka mallaka sai yakare gun neman magani…cewar hjy ikilima tana murmushin mugunta, had’e da cewa dubesa shida gawa duk days suke banbancinsu guda 2 shine numfashi d gani mutane kawai,Amma bayaji baya mgn “dayanaji saina gaya Masa abinda zaisa zuciyar sa bugawa,domin ni hjy ikilima nafi k’arfin aja Dani ko a wulakanta mun y’a daya Dana mallaka aduniya gashi kaga aya dg yau inkaji wani zai wulakanta wata ka mishi mgn yabari….
Riyan ta d’ago cikin tsantsar bacin rai had’e da tausayin Abdallah sbd ana ci Masa fuska Dan ALLAH yajarabesa,sbd azatonta bejin mgn da gske”

Salamu alaikum!bara namuku sallama sbd naga da alama dg y’ar har uwar bbu Wanda yasan darajan yin sallama ko amsata…keeeeeee k’aramar mar kunya….cewar zeenat tana nufar riyan tamkar zata daketa..
Murmushn takaici riyan tayi dukda tad’an tsorata tace hmmm ALLAH ya Baki saa kikawo hannunki jikina wlh ,Dana nunamiki ke danbace!Kuma JAHILA”nikike cewa jahila?”

Eh”ance jahila mezaki iyane?”

Inbacin jahilci Taya zakixo gun bawan ALLAN da ubangiji yajarabta da lalura kima Masa ba’a kosan goranta Masa…iyeeeee! tafad’a cikin tsawar dabatan ta iyataba….saurin janye zeenat hjy ikilima ta yi sbd taganin kamar riyan zata iya bige zeenat d’in sbd taji ance abin ba ajiki bane “zuciyace .
Mom rabu Dani naci uwarta wlh….hhhhhhh…kinadai zagin takusa dake batawaba”sannan kisani dama Abdallah yasha fad’a mun bayasonki ko kad’an hasalima cusa masake akayi…kutumar ubancan,cewar zeenat azafafe…ita kuwa riyan abad’ini Abdallah bece Mata hakaba tafad’a ne sbd zeenat taji haushi ,gashi Kuma ta ji haushin..

Yyinda Abdallah tun farkon Fara yab’a Masa mgn yakejin zuciyarsa na zafi had’e da k’una…Amma jin kalaman riyan sai yaji tamkar anyaye Masa abinda yakeji sbd shima ya fahimci riyan batasan yanajin mgn ba…

Hjy ikilima ta ja hannun zeenat had’e da cewa muje kibarta kawai zata ga abinda zai faru d ita… sannan Wanda takeyi danshi batada daraja agunsa sbd ai itama dama aka Bata ta auresa bashi yace yanasoba….hmmm hjy kenan ai Ni bandamu yasoni ko kar yasoniba !mijina ne ko auren me mukayi Zan Kuma kula dashi tsakani da ALLAH sabanin y’ar ki sake sonsa sbd wasu abubuwa, wad’anda mutum ke kuskure yace zai so Dan uwansa sbd su,ke kuwa Abu gudane yasaka Abdallah rashin kaunarki,shine rashin tarbiyya,dukda inazaton gadon hakan kikayi….Dan ALLAH momi kisakeni na lallasa yarinyar nan…

Hmmm kisaketa Mana!

Sannan inaso kusani keda ita sbd da alama bakuje islamiya duk abinda zai Sami bawa mai kyau ko marar kyau to yanada ga k’addararsa ne,sbd haka baku isa kumin komaiba suk abinda yasameni nayi imanin dg ubangijina ne.

Hmmmm haka kikace?”

Eh “basaina maimaita Miki ba,cewar riyan adake.

Kwafa hjy ikilima tayi had’e da cewa zakisan wacece Ni wlh,dg yau zuwa gobe Zaki fita dg rayuwar Abdallah Dan zansaka mahaifiyar sa tace yasakeki kota tsine Masa…

Kisaka niya Dan ALLAH tunda Bata lfy Yar sa kukeba ,to kisaka hartace zata tsine Masa ,kisani barazanar ki batayi amfaniba, sannan dg karshe kisani duk mai gsky yanatare da ALLAH,kija akuyar yarki kufice ko nata taramuku jamaa….kafin suyi mgn su Abba sun murd’a kofar sun shigo , kasancewar dawowarsu kenan dg masjid angama isha’i.

Koda Abba yaga hjy ikilima Saida yaji wani iri”sbd dama beson abotarsu da mom,Dan bbu yadda zaiyine kawai.

Fuska bbu yabo bbu fallasa ya amsa gaisuwar ta da jajen datake Masa akan Abdallah.

Wacce ta ke mgn tana karya wuya ita tausayi…

Riyan kuwa batayi mamakin ganin hakan ba,har suka fice itada zeenat.

Mamakine fal da al’ajabi acikin zuciyar Abdallah ,game da hjy ikilima da mom…

Sannan Kuma wani gefen na zuciyar sa cike yake dajin dad’in maganganun da riyan ta fad’a musu,sbd ko shi iya abinda zai fad’a d’in kenan, inda zai iya mgn.

Ya k’udurta aransa ko mom ta ce yarabu da riyan wlh bazai Mata biyayya ba” sai yanxun yagane dalilin dayasa Hafiz ya ce kada yanuna yanajin mgn.

Mgnar da Abba yyice tadawo dashi tunaninsa,Gurin tambayar riyan sunyi isha’i?tace ah ah”nan da toimakonsa Abdallah yyi isha’i yasha abinsha..

Gurin karfe 10:30 Hafiz ya shigo,byn sun gaisa da Abba yace Abba yaka Mata ka koma gd” nida riyan zamu kwana gunsa,anbani wani daki dake kusa Da nan ,ita riyan sai su kwana anan ita dashi..

Abba yace ah ah Hafiz kaga kanada iyali,kaje kawai tunda ga guards nasa awaje….kayi hakuri Abba kada muyi jayayya ,ai tana Gurin ammi(matarsa) can zata kwana,Tama koma can ,sai Naga yadda jikinsa yakasance kafin ta dawo …

Abba cike da jin dad’i,yace to shikenan Hafiz ALLAH yyi maka albarka. Yabarku tare,naji dadin yadda ka dauki Abdallah Dan uwa agareka.
????????????????????????????????????????

????AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????

Story & written by
mmn fareesa

Not edited❌

P 28

….. Hafiz yyi murmushi had’e da cewa Amin,nan abban ya matsa kusada Abdallah ya rungumesa,yyi a ddua yasha famasa ajiki,kafin yyimusu sallama ya fice dg room d’in sbd body guards nasa Dana Abdallah na waje…
Byn fitar Abba riyan daketa gyangyadi ta dubi Hafiz tace Amma Wai Dan ALLAH me ke damunsane?Dan ALLAH! ajiyar zuciya Hafiz yyi had’e da zaiyane Mata abinda doctors sukace,yadora da cewa Amma yanajin abinda ake cewa….be k’arasa ba riyan tayi saurin kallon Abdallah sbd ta tambatar da abinda Hafiz yace,kaddai ace duk abinda yafaru d’azun akunnansa,gashi ta Masa k’arya… tafad’a azuciyarta…. yyinda Abdallah keta aikin kallonta sbd yafahimci abinda take tunani,sai yyi kok’arin kanne Mata ido d’aya…saurin janye idonta tayi ta dubi Hafiz dake cewa bara na je d’akin dake kusa da nan na kwanta har 11:tayi, yafad’a Yana hamma,kafin Yadubi riyan yace inyanason shiga toilet ,ki bud’e kofar body guards nasa na nan kice su kirani…bejira asartaba yanufi kofa…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button