AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Amma Kuma Dan ALLAH nifa….saikuma tayi shiru sbd ganin Abdallah yatsareta da ido.
Hafiz ya juyo yakalli Abdallah wanke Masa alamar yacewa riyan ta kwanta.
Murmushi yyi had’e da cewa to ke kinji both yace ki matsa kusada shi ku kwanta… yafad’a cike da tsokana Yana satar kallon Abdallah dake hararan sa…
Itama riyan murmushn tayi,sbd ta lura Hafiz tsokana ajininsa take.
Tabarma da bargo taja ta shimfid’a ta kwanta,shikuma Hafiz ya gyarawa Abdallah kwanciya kan bed d’in ya fice…
Can cikin dare riyan takasa bacci ,sbd tunanin ciwon Abdallah d a Hafiz ya fad’a Mata Wai doctors since basuga abinda ke damunsa ba”inhasashenta gsky ne to ciwonsa bana asibiti bane na gd ne.
Tashi tayi cikin sand’a ta matsa kusada Abdallah ,Wanda ke kallonta tun farkon tashinta Amma Bata saniba”
Gabansa ta tsaya tayi addioin tsari ta tofa Masa ga jikinsa ,kafin ta koma ta kwanta.
Lumshe ido Abdallah yyi cikin wani bakon yanayi…dg haka bacci yyi gaba da shi.
Washe gari tunda wuri riyan da Hafiz suka shirya Abdallah bacin yaci ya koshi,kafin mom da Abba su shigo tare da doctors.
Tsintar kansa Abdallah yyi da k’inson ganin mom dajin mugun haushinta,sbd haka ko kallonta be yiba ,yanaji tana cewa jiya da masassara ta kwana shiyasa batazoba, yyinda itama riyan ko kallo Bata ishetaba balle ta gaisheta…
Byn doctors sun gama dubasa ,aka sallamesa.
Mom tace dole acanza hospital.
Kai tsaye wata private hospital suka sake zuwa….hmmm saidai abin mamaki da ita d awaccen duk Abu guda suka fad’a gameda Abdallah..
Hakan yasa Abba yace sukoma gd gobe zai saka asama Abdallah biza konan da sati 2 su tafi Cairo ko Egypt adubasa sosai…
Da wanna suka koma gd.
Byn isarsu mom tace awuce da Abdallah part nasa,tasaka angyara d’azun.
Abdallah yyi mamaki kwarai ,azatonsa acan part d’in mom za’a yi jinyarsa.
..
######
Bayan 6 “yau yakama Abdallah kwanan sa 8 kenan acikin wannan lalura tasa,Wanda yakasance dg riyan sai Hafiz da Abba kawai ke kula dashi,Dan mom arana sau2 ta ke lekowa ta gansa ko sau d’aya.hakan yasa zuciyar Abdallah rauni da karaya had’e da wani zato.gefe guda be wuce saura kwana 9-10 afita dashi waje Dan duba lfy yarsa…. sannan kullum riyan namasa adduoi azamzam data saka Hafiz ya kawo Mata tana bashi Yana sha.. sannan anrufe campany d’in Abdallah sai byn yaji sauk’i wannan umarni ne na mom,hakan yatada hankalin mutanen dake aiki campany d’in…
Zaune yake kan keken sa, orange din t shirt ce ajikinsa da wando 3 quarter” riyan na tsaye a gefensa tana basa frash milk “sai aikin kallonta yake”a Dede ban mom ta shigo tana wani yatsina fuska had’e da toshe hanci….cikin al’ajabi Abdallah ke kallonta be ankaraba ya k’ware awahalce yabiyo Masa ta hanci da Baki,gashi baya yin tarin sai rawa bakinsa keyi cike da azaba…hawaye riyan ta ji sbd tausayinsa …da sauri ta saka tissue bbu nuna ko k’yama tafara goge Masa na hancin kafin ta goge na bakin…
Mom ta tab’e baki had’e da cewa ke ki kula adunga gyara Gurin sosai sai wani d’oyi nakeji,bara naje in anjima na dawo ai sai zuciyata ta tashi nayi amai wannan kayan k’azanta haka…ta ida fad’a tana ficewa.
Riyan ko ci kanki batace mataba,ta dubi Abdallah da idanunsa sukayi jajir”yyinda jijiyoyin kansa duk sun tashi Rad’o rad’o”almar ransa yab’aci matuk’a…
Cikin sanyin murya riyan tace kayi hakuri Dan ALLAH,duk tsanani Yana tare da sauk’i…
Rufe ido Abdallah yyi yanajin wani Abu game da riyan,dake kula dashi tsakani da ALLAH Bata hantararsa ko nuna k’yamarsa gashi mahaifiyar sa na gudunsa , wannan wace irin rayuwace haka… lallai sai yanxun yafahimci cewa ciwonsa bana asibiti bane,gsky Yana sakaci gun adduoin neman tsari dukda wani time d’in yanayi,Amma yadauki hakan amatsayin k’addararsa…sai yatuna da hadisin monxon ALLAH (S AW) daya ke cewa TAHARIF I’LALLAHI!YA’A RIFIKA FI SHIDDATI…ma’ana(kasan ALLAH sadda kake cikin yalwa, zai Sanka sadda kake cikin tsanani.) Lallai RIYAN ba abin yadawa bace arayuwarsa gashi tana Masa addua kullum dare d safe Bata gajiya hakan yasakashi shima yanayin adduar azuciyarsa…. Gashi Kuma Yana ganin amfaninta tunda yanxun Yana iya d’a ga kansa ki ya girgiza sa….tabbas in har ALLAH ya bashi lfy bazai tab’a iya rabuwa da itaba dukda yasan batasonsa” Amma shi Yana Mata zazzafan SO”saidai inhar yaga ya jima be warkeba to dole ya hakura kada ya tauye Mata hakki,Amma shi tuni yyi ball yasoke auren contract ,saima fatan ALLAH ya yafemasa sbd yasan bbu kyau irin wannan auren”…. sallamar Hafiz ta katse Masa tunani….
Da misalin karfe 4:47 Hafiz ne ke Jaye da Abdallah dake kan keken sa,suka nufi part d’in mom sbd tunda aka sallamesa dg asibiti yadawo gd kullum sai Abba yasaka guards nasa da Hafiz sun fita dashi Gurin shak’atawa da Gurin hutawa…
Har zasu wuce sai Hafiz yace baradai suje suyi Mata sallama dukda Abdallah beso sun biyanba.
Awaiting parlour suka shiga Bata nan…zulfa ce tace tana parlourn ta…hakan yasaka Hafiz karya kwana da Abdallah suka nufi parlourn mom.
Bayan sun shige corridor d’in da kofar take , Hafiz na kokarin bud’e wa….yyi saurin dakatawa sbd jin muryar mom na mgn arude….kamar haka..
Wlh kawata bbu lfy sbd banjima da dawowa ba dg Gurin boka,wlh kashe yaron nan zanyi sbd gudun abinda zai faru..sbd boka yacemun yaga ana mishi addua zata iya yiwuwa yaji sauk’i “sannan muddin ya warke to ciwon zaidawo ajikina, alokacin zantona ma kaina asirin duk abinda nayi aciki kuwa harda yiwa alhj asirin bin umarnina da rabasa da danginsa,dayiwa mahaifiyar Abdallah kurciya shekara ashirin da ,niyar dasuka wuce,Kuma muddin ya warke karyata ta Kare kenan” meye shawara hjy ikilima?”
Yauwa !hakan za’ai mugama da mitsiyacin mukashesa har lahira ,bana kaunar Abdallah ko kad’an!burina shine nagaje abinda ya mallaka.
Shiyasa nace Miki sakashi yasaki riyan bashine fa’idaba ,gara abarta ,Kinga bayan munga bayansa sai mu korata ta k’ara gaba…shi alhj koni na k’arasashi Nanda wata 6ko7 Kinga sai ace zafin mutuwar D’ansa ce da bak’in ciki yakasheshi…
Yo ai na amso magani gun boka ,yau da dare Zan zuba Masa a frash milk nabawa shegiyar matarsa tabasa zuwa safe ya mace Kinga…da safe sai akaisa kabarin…..ah ah kwfa kamar motsi nakeji bara na duba…..
Da sauri….
Share
BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????
????AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????
Story & written by
Mmn fareesa
Dedicate to all my fans????????
Masumin mgn a pc banmusu reply ba dawasu grps kuyi hakuri mutane sunmin yawa nakaranta comments naku ,naji dad’i sosai tunda akafara wannan novel ba’a tab’a yin comments masu yawa zafafaba. kamar na last page nagode????????????
Not edited
P 29
….Dasauri Hafiz yyi baya had’e da k’ok’arin juyawa da Abdallah”da hanzari Abdallah ya girgiza Masa Kai alamar su shiga kawai…daidaita nutsuwarsa Hafiz yyi had’e da bud’e kofar da sauri… adedenan mom ta iso tana dubarsu….boyayyar ajiyar zuciya tasaki sbd ganin bbu wani tashin hankali akan fuskokinsu “hakan ya tabbatar mata da cewa basujiba kenan….mom basai mun zaunaba gun shak’atawa dama zamuje dashi”shine nace bara muzo miyimiki sallama…gsky ka kyauta Hafiz kaji”nagode sosai d yadda kake kulamun da yaro, ALLAH ya baka ladar….tak’are da cewa ai gara yyi fitar bankwana azuciyarta…
Cikin jarumta had’e da k’arfin hali Hafiz yace to mom bara muje ko….to Hafiz ta fad’a had’e da shafa kan Abdallah Wanda yyi k’asa da ido sbd gudun taga idanunsa sun sauya kala”yyinda zuciyarsa ke bugawa tana sanar da shi mafarki yake….
Cikin dakiya Hafiz yyi Mata sallama suka fito dg parlourn,yasaki wata nauyayyar ajiyar zuciya yacigaba da turo Abdallah har suka baro part d’in mom”
Byn sun fito Hafiz cikin fargaba yace yanxun Ina zamu jene domin samun mafita?”ko muje mu sanar da riyan ne?”
Da sauri Abdallah yad’aga Masa Kai alamar eh”yyinda gumi ya wanke Masa jiki,idanunsa sun yi jajir”har yanzun fata yake ace mafarkine abinda kunnensa yaji…