AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Part d’in Abdallah suka nufa…tun kafin su shiga sukejin muryar yanxuwa dubiya…
Riyan ce zaune da mama zuwaira da Fatima(datazo hutu) tasamu anyi bikin riyan ,shine ta matsa su zo itada mama zuwaira,shine sukazo”riyan ke fad’a musu rashin lafiyar Abdallah suna cikin jajanta Mata suka shigo shida Hafiz…

Kallo d’aya riyan ta musu ta fahimci da akwai matsala”

Byn sun gaisa da su mama zuwaira”sannan sukayi sallama,riyan ta rakasu ,kafin ta dawo cikin parlourn.

Da Abdallah ta had’a ido…da sauri ta janye idanunta sbd ganin yadda nasa sukayi jajir”kafin ta dubi Hafiz had’e da cewa Yaya Hafiz lfy dai ko?”hmmmm riyan bbu lfy ko kad’an “munacikin tsaka mai wuya wlh…INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU’UN! Riyan ta fad’a had’e kallon Abdallah dake hawaye sbd tuna Wai anyiwa mahaifiyar sa kurciya sbd arabata d Abba”
Hafiz ya shiga sanarda riyan k’udirin mom da komai….. murmushi mai ciwo riyan tayi had’e da cewa hmmm Yaya Hafiz kenan aini tun kwanana 2 agdn nan nasan cewa mom ba itace mahaifiyar Abdallah ba…da sauri Hafiz yace da gske?eh wlh cewar riyan ” miyasa Baki fad’a ba to?”
Banida hujja ,Kuma hakan ba hurumina bane, sannan dama nasan kobajima gsky zatayi halinta”
Kwanana 2 da zuwa gdn nan,sai naje parlourn mom Dan intambayeta Zan tafi gd…harzan shiga saina dakata sbd jin tana mgn awaya da aminiyar ta hjy ikilima cewa yanxun ta zubawa Abdallah magani ga abincin sa ,data karb’o gun boka, Abdallah zai mutu inyaci sbd tanason mallakar dukiyarsa….iya nan naji na fito aguje,nafasa zuwa gdn.
Inbaka mantaba arana ta 2 da zuwa gdn nan zakaci abinci na buke hannunka ya zube k’asa ,nace maka tsakace ta fad’a to ai shine wannan abincin…ta fad’a tana kallon Abdallah…da yyi mutuwar zaune sbd ganin abun yake tamkar almara…riyan ta cigaba da cewa bayan na kwashe abincin da niyar na zubar sai a hanya muka had’u da ita ,cikin tsawa tace mun yaci Kobe ciba?”sainace beciba ,yace be ra’ayin cin komai yau(nayi Mata k’arya)sai naga tasaki ajiyar zuciya ta karb’i abincin ta wuce…
To sai Raina yabani k’ila ta canxa shawara ne…

Ajiyar zuciya Hafiz yyi had'e da cewa gsky ne ,nikaina namata wannan zargin naba itace mahaifiyar sa ba, sbd nasha jin suna maganganu masu wuyar fassara Koda zeenat Koda hjy ikilima.

Amma yanzun riyan ki zauna kijiramu ,muje gd gun ammi na neman shawarar yaza ayine…. Yak’are maganar da sanar dasu mom tasan wacece hjy hafsat,dakuma tambayar da mom tayi Masa game da amminsa.

Cikin tausayawa riyan tace to shikenan kuje d’in zanjiraku”ALLAH ya shige Mana gaba,ta fad’a had’e da saka tissue ta goge Masa zufar dayaketa Yi da hawayen dake zuba agefen idonsa….

Cikin minti 15 suka iso gdn ammi.

Koda suka fito parking space ,hafis cewa yyi kada Wanda yabisu bazasu jimaba..

Tana zaune a parlour kan kujera ,kasan cewar yau week end ne bbu zuwa hospital.

Da sauri ta amsa sallamar Hafiz dake Jaye da Abdallah kan kekensa,tana mamakin zuwansu a irin wannan lokacin”

Ko gaisawa Hafiz be Bari sunyiba , yafad’a jikinta yasaki kuka mai cin Rai, sbd d’azun daurewa kawai yyi sbd kada riyan ta damu dakuma jama’ar dake bak’in get na gdn su Abdallah kada su San abinda ke faruwa..

Arude ammi ta d’ago sa had’e da cewa lfy ?”meya faru…

Cikin kuka Hafiz ya sanar da ita komai had’e da cewa meye mafita ammi?”

Cike da tausayinsu tace lallai mutum mugun icce bacin rabasa da mahaifiyar sa da tayi,shine shikuma zata kasheshi….insha ALLAH Bata isa tayi hakan ba ALLAH bazai Bata ikoba….ta fad’a had’e da kallon Hafiz tace shawara4 ce zuwa ukku mafita ayau…

Ak’agare yace miye shawarar?”

Share
BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????

???? AUREN WATA SHIDDA????

????????????????????????????????????????

Story & written by
mmn fareesa

Dedicate to all my fans????????????

Not edited

P 30

Ak’agare yace miye shawarar?”

Ajiyar zuciya ammi tayi had’e da mik’e wa tsaye tana safa da marwa… cike da tausayawa tace na farko dole Abdallah yyi mutuwar wucin gadi sbd shi yak’i Dan yaudarane,inbaka iya Kama b’arawoba saishi yakama ka”
Ma’ana zanyiwa Abdallah allurar da zatayi 24 hours ajikinsa tana aiki “tun dg yau zuwa gobe kamar yanxun , sannan ta sakesa kafi….Amma ammi ta yaya kenan bacin kinsan sotake taga bbushi aduniya..jirani Mana Hafiz”cewar ammin.
Ai yanzun zanmasa allurar zaiyi kusan 30 or 35 minit kafin tafara aiki ajikinsa”
Na biyu…shine byn yanxun kamaidasa gd “zamuje Gurin liman me tsaran makabartar dake k’arshen g r a,nida kai muyi Masa bayani in ankai Abdallah anbinnesa zaka koma ku hak’osa kaidashi”sai dare yyi kaje ka daukosa ka maidosa nan gdn”na ukku shine in anyi sadakar 7 Zan canza Kama na nuna nice yayar mahaifiyar riyan naje na cewa hjy hafsat Zan tafi da ita gd tayi ta kaba,nasan zataso hakan”dana tafo da ita nan sai kawai ,mujabgoransu nidakai zuwa k’auyen karaye gdn baffanka MLM HABIBU(masanin kur’ani mai girma,Yana karya sihiri yayan mahaifin Hafiz ne) nasan insha ALLAH Abdallah komai Daren dad’ewa zai warke sbd da alama sammu aka Masa “kaga dg nan inya warke sai ya fito ya yak’i hjy hafsat,Amma tunkararta yanxun gsky bashine mafitaba sbd shikanshi mahaifinsa tagama dashi….na hudu shine duk jawabin nan kusanar da matarsa (riyan) sbd gobe in ALLAH ya kaimu zatafito tana kururuwa byn sallar asuba ta nufi part d’in hjy hafsat tasanar da ita Abdallah baya numfashi ko motsi…munsan dama burunta kenan ,Kuma baza a bincika ba sbd tagama da Abbansa,inkuma riyan ta ji ana cewa za’a bincika aga ya mutu ko kuwa to tayi hanzarin kiranka !kaikuma ka kirani…..

Ajiyar zuciya Hafiz yyi had’e da kallon Abdallah cike da tausayawa abd ganin za’a sa yyi mutuwar wucin gadi…

Ahankali yace AK kaji duk jawabin ammi ko?”

“D’aga Kai yyi “alamar eh.

Hafiz yace ka amince da shawarar ta?”

Abdallah ya d’aga Kai hawaye masu zafi na zubar Masa akumatu…ba tausayin kansa yasa Kashi kukaba,ah ah tausayin mahaifiyar sa da aka rabashi da ita tsawon wasu shekaru… lallai ya tafka kuskure “Yana zaune duk baisan hakan ba..wata zuciyar tace K’ADDARA ce tayi sanadin hakan..

Muryar Hafiz ce ta katse Masa tunani gun cewa to ammi kusanar damu wacece HASSU TSIYA TSABA?”

Ammi ta ce Zan sanar da ku,Amma lokaci ya kure yanxun Hafiz ,muyi abinda ke gaban mu..

Hafiz yace to shikenan….

Kamar yadda ammi tace haka akayi tayiwa Abdallah allurar(bazan fad’i sunantaba sbd kada anema acutar da wani)

Sannan Hafiz da body guards nasa suka maidasa gd gab da magrib , Hafiz be bar gdn ba Saida yyiwa riyan bayanin komai gameda shawarar da ammi ta basu,yakuma sanar da ita tayi taka tsan tsan Dan kubutar da rayuwar Abdallah ,sbd yau da isha’i mom zatazo ta kawowa Abdallah frash milk,kada ta yarda yasha..

Bayan Hafiz ya koma gd sunyi magrib da isha’i,yaja ammi amotarsa ,sukaje gun liman me tsaran makabartar,suka Masa bayanin komai sbd sun San insunkoma basu sanar masaba ,da matsala za’a zargesu ne…da farko liman ya nuna be yardaba ,Amma dasuka Masa bayani sosai suka nuna Masa photo na Abdallah sai ya amince ,yyi musu fatan samun nassara.

Bangaren su riyan kuwa.

Suna cikin tashin hankali da faduwar gaba har akayi magrib zuwa isha’i.

Zaune riyan take kan kujera, yyinda Abdallah ke kan kekensa zaune jigum Yana jiran zuwan mom.. had’e da tunanin Wai shine gobe zaa binne da ransa….oh shin mi wasu suka dauki duniyane Wai?”

Sallamar mom ta kashe Masa. Tunani… Wani mugun faduwa gaban su yyi shida riyan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button