AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da wannan tunanin ya isa part nasa”
Murmushi yyi sakamakon hango Hafiz dake zaune kan 2 seater .
Shima Hafiz tashi yyi Yana dariya had’e da hugging abokin nasa dayake masifar kauna yyi, sannan suka yi musabiha suka zauna had’e da Fara firan yaushe gomo.
Abdallah yakalli agogon dakin yace friend time din sallar la’asar yakusafa!
Y’ar dariya Hafiz yyi hade da cewa hmmm big man kenan Ashe har yanxun halayenka masu kyau nanan?” zuwanka turai bai canzakaba ko?”
Harararsa Abdallah yyi yace Kai Dan iskane wlh to Dan mutum yafita waje sai yacan za halaye .
Amma ai kasan akwai masu canzawa,bama wannan ba kasan bikinmu my feedo ,saura 3 weeks Kuma sbd Kai nakara Masa tsawo Dan biki bbu aminin ango ai bazaiyi armashiba, kaga kaima dg nan ai sakasamu wata fine baby ko jone ko?”cewar Hafiz Yana dariyar shakiyanci…
Tsaki abdallah yaja had’e da cewa hmmm kaifa matsalata dakai kenan wlh bakada mgn sai ta mata ai gara su ammi suyi maka aure wlh sbd jarabarka kada wata Rana ka Fara kama ya’yan mutane wlh ,sbd nason inkana mafarki da sabbatun….look mlm dallahai gara Ni dakai,tunda Kai boye taka jarabar kake amma saika rik’a basarwa,garama ka falka dg bacci cikin y’an matan dake tururuwar cewa suna sonka ka fitar da guda musha biki kawai..
Harararsa yyi cikin kosawa yace hmm aini har yanxun Banga macen data isa nace inasontaba bangantaba Dan duk basuyiminba ,ita xeenat tursasawar mom ce kawai yasani kulata da kokarin cusata araina Amma taki ta cusun.
Shiru Hafiz yyyi danko shi kanshi wani time din Yana tunanin anya mom ce mahaifiyar Abdallah kuwa?"
Sallamar zeenat ce ta katse musu firarsu…tuni gogan naku yyi kicin kicin da fuska sbd ganin yadda tabayyana surar jikinta a fili Kuma Wai itace matar dazai aura..
“Sanye take da riga da wando sun matseta kirjinta have waje “ga gashin doki da tayi attached dashi ,tasaka wani siririn mayafi dashi gara bbu,sai fitinan nan kamshi ketashi ajikinta.
Hafiz ne yyi kokarin danne dariyarsa sbd ganin yanda Abdallah yahade rai,ya amsa sallamar ta, had’e da cewa ranki yadad’e munyi fushi gsky sai yanxun zakizo ganinmu .
Murmushi tayi hade da cewa hmmm wlh ba laifina bane ,Saida na tambayi baby yaushene time din dazai sauka dg jirgi naje airport tararsa ,amma yaki fad’a.
ta fad’ar hakan had’e da nufar tana kokarin hugging nasa…wata zabura yyi hade da kaucewa tafad’a kan kujerar ,fuska bbu walwala tace meye haka baby?”
Tabe bakiyyi beyi mgn yadubi hafis yabanko Masa harara sbd ganin Yana tarin k’arya akan dariya nason kuccemasa.
Cikin basarwa had’e da danne zuciyarsa yace my zeenat ya kk ya su ummi ??”
Lumshe ido tayi sbd jin sansanyar muryarsa mesata nishadi,tuni ta nemi bacin ranta ta rasa”ahankali ta ce lfy lau alhmdllh gsky baby kayi kyau Zama ingila ya karbe ka dukda wani time din Muna video call ,amma sainaga kafi kyau azahiri.
Murmushn gefen Baki yyi hade da mik’ewa tsaye sbd tuni Hafiz yabasu guri gudun kada yyi katib’ara..
Ya dubeta ,cikin k’osawa da surutunta yace my zeenat zamu wuce masjid dg nan …amma aizaku dawo Zan jiraka pls shekara4 fa bamu haduba,tayi saurin katse Masa mgn,adakile yace dg masjid akwai inda zani..amma baby b….pls ya isah banason surutu kada kisamun ciwon Kai malama .hmmmm kodai gun wata zakaje ,inkuwa hakn yafaru wlh zatayi nadama yarinyar sbd indai akankane to wlh har kasheta Zan iya yi sbd….stop it Abdallah yakatseta atsawace, had’e da ficewa dg parlourn fuska daure.
Tsaki yaja azuciyarsa yace shiyasa banson xaman Nigeria gashi tun ban kwana ba Raina na baci,wlh taci darajar mom shiyasa nike binta ahankali sbd gudun b’acin ran mahaifiyata da wlh sai tagane kuranta ,sbd rashin hankali Wai zata iya kisa mittss yasake Jan doguwar tsuka….Hafiz dake kallon sa yace lfy dai ko AK(haka abokansa ke kiransa) naga kana tsaki ko kaida madam ne?”
wata uwar harara ya maka Masa suka fice zuwa masjid, yyinda Hafiz yyi shiru sbd yasan halin abokinsa.;;;;
Da dare byn yagama isha’i sannan yanufi part din abbansa.
Byn sun gama gaisawa atare sukayi diner da Abba sannan suka Fara fira .
Can Abdallah yace Abba Wai Dan ALLAH miyasa baka zuwa bauci Kuma bakason naje??” bacin kasan danginkane acan pls ka amsamun .
Shiru Abba yyi hade da Jan numfashi , sannan yashe kayi hkri nima bansan daliliba ,amma very soon zamuje tare amma kada kasake kayiwa mominka wannan zancan kaji?”
Cikin mamaki abdallah yace miyasa Abba?”
Kallon sa Abba yyi yace kayi hakuri banason tambayar kaji ?”shiru Abdallah yyi Yana tunanin Wai Mike faruwa ne tsakanin Abba da danginsa daya mantadasu baya taimakonsu da d’inbin dukiyarsa”.
Kallon Abba yyi cikin marairai cewa yace pls my Abba Zan maka wata tambaya “
Kallon sa Abba yyi hade da tsaresa da ido yace inajinka”
Fuska bbu walwala yace Abba miyasa kake bin umarnin momy saikace Kaine mijin itace matar?”gsky Abba abun namun ciwo inda Momi ba mahaifiyata bace dole karabu da ita,sbd bazanso ganin ana juyaka ba Abba why?”yafad’a cikin ‘bacin rai ,idanunsa sunyi jajir, yyinda Abba yakasa mgn dabashi amsar tambayar sa.
Cikin huci yace shiyasa banson aure sbd abinda mom ke maka Abba gsky ,dan bazan iya k’yale mace ta juyaniba,Kuma Ni xanmata mgn Abba sai….da sauri Abba yace kul!
Kada kasoma kaji abdallan Abba kamana addua komai zai daidaita zata denakaji insha ALLAH yafad’a cikin damuwa.
Kallon Abba yyi hade da cewa shikenan Abba baza n mata mgn ba…. murmushi Abba yyi yace ko kaifa my son .
Mamaki abdallah keyi azuciyarsa ganin Abba yasaki ransa jin Wai bazaiyiwa mom mgn ba lallai akwai abinda ke faruwa wanda besaniba ….
Besake ma Abba wata tambayar ba baci wannan haka sukayita firarsu har mom takira Abba a waya tukum sukayi sallama.
Part d’in sa yawuce, direct toilet yashige ,yafi 30 minit sannan yafito yyi Shirin kwanciya yafeshe jikinsa da turarukan sa masu masifar kamshi.
Tamkar zeenat najira ta yi kiransa,tsaki yaja ganin itace,saima yarufe wayar baki daya ,dama be dadeda saka sim card d’in sa ba na Nigeria.,,,,,
Bangaren su riyanatu kuwa”da dare byn sunyi komai harda Shirin kwanciya zuwaira ta shigo”
Bayan ta sallami customers,da sallama ,ta zauna suka sake gaisawa sannan ta musu murnar kubutarsu dg garinsu..
Sannan tace to da farko dai mariya Yar uwatace, sannan nima mijina y mutu inada y’a zatayisaar wannan,ta nuna riyanatu dake zaune kan ta duke.
Tana makaranta kwana ajinta5 befi saura kwana 8tadawo hutuba nan dakintane kuke.
To yanxun wace Sanaa Zaki iya?”
Umma taja ajiyar tace ko aikatau nasamu lfy lau.
Zuwaira tace to shikenan ma sai kimun sbd memun wanke wanke tayi aure sati2 dasuka wuce,awata Ina Bata dubu ukku ,Kuma nikecida ta,Zaki iya?”
“Umma tace eh insha ALLAH”
Zuwaira tace to ita riyanatu tayi makaranta?”
Umma tace eh wlh dg aji 3 tabari,anata mun surutu Wai nabarta tana karatu bbu aure saita lalace ta girma ta gand’ame.
Murmushi zuwaira tayi tace hmmm in bacin abin mutumin kauye duka riyanatu nawa take,ai batawuce 17 ko 18 ko?”
Umma tace eh”
Zuwaira tace to shikenan insha ALLAH in sun koma huta sai a maida ita da islamiya ko?
Umma tace eh ,acan ta allo takezuwa tayi ihu34 .
Zuwaira tace Masha ALLAH.
Nan sukayi sallama ta basu guri su sake.
Washe gari…
Share pls
BY MMN FAREESA
????????????????????????????????????????
???? AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????