AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Cikin ambaton ALLAH riyan ta amsa”tana kallon frash milk din dake hannun mom cikeda cup…..
Zama tayi fuska asake ,ta amsa gaisuwar riyan,kafin tace yamai jikin?
Riyan tace gashinan da sauk’i…
To madallah”ga frash milk sabon yayi,abashi Dan tafi waccan dakuke bashi,ta fad’a had’e da cewa to gata abashi mugani kota Masa dad’i…
Karb’a Riyan tayi hannu na kirma..
Mom ta matsa ta shafi kan Abdallah had’e da cewa sannu my son kaji”ALLAH ya tashi kafad’ar ka “dakai nake kwana nake tashi azuciyata sbd tausayin ka Abdallah kana cikin wannan hali,bbu jiii bbu mgn Amma aikomai yakusa zuwa karshe tunda za’a fita dakai waje… fad’a had’e da kukan munafurci Wanda bbu hawaye.
Azuciyar riyan tace shaid’aniya kenan,afili kuwa sai taita rarrashinta gun cewa kiyi hakuri mom ki yarda da k’addara insha ALLAH zai Sami sauk’i.
ALLAH yasa riyan “
Ameen mom”maza ki basa mugani kozai shnye ne…
Daukar cup d’in riyan tayi tana latsa wayar Abdallah dake hannunta had’e da kokarin Zama kusada keken Abdallah Dan tabasa…
Bata kaiga zamaba aka d’auke nefa ta gdn Baki daya…
Mittsss mom taja tsaki hade da cewa Kai Yan nefa bbu tabbas Yanzun ai ya’u direba zai tada Jan…
Kafin riyan tayi mgn haske ya gauraye parlourn…
Murmushn samun nassara mom tayi had’e da cewa yauwa anmaido”maza kibasa yasha aje akaisa ya kwanta…
Kallon mom kawai Abdallah keyi,jiyake kamar yashaketa sbd tsanarta,sai yau ya yadda da ake cewa wasu dg cikin Mata shaid’anu ne,Kuma dangin shaid’an…Ashe duk abin nan da mom ke Masa ba Dan ALLAH bane…cup d’in da riyan ta Kai bakinsa yadawo dashi tunaninsa….
K’uri da ido mom tayi tana dubarsu har Abdallah yashanye tas , riyan ta dubi mom had’e da cewa Kinga kuwa ya shanye duka bara na Kai cup din kicin natafo Masa da fura ya k’ara….
Ajiyar zuciya mom tayi aboye, yyinda fuskar ta fal da farin ciki tace to shikenan jeki dawo nima na wuce,namaji Alh shiru baidawoba bare yazo yaduba my son…riyan ta fice dg parlourn da cup a hannunta….
Tana fita mom ta kece da dariya had’e da cewa banzaye ,wawaye daku kaida ita… lallai Abdallah dg yau kagama numfashi… matsiyaci na tsaneka bana kaunarka kokadan ,ko rungumeni kayi ,jinake tamkar na shakeka,naso ace ka auri zeenat nasakata ta kashemun kai….
Duk abinda take cewa Abdallah najinta Amma be dagoba balle ya nuna alamar yaji,yyidai shiru…akuma dedenan Abba yyi sallama yashigo cikin parlourn.
Amsawa mom tayi , had’e da maida fuska kalar tausayi,tace Alh yakamata fa amaida Abdallah hospital kafin zuwan ranan da za’a fiddasa waje….
Zama Abba yyi hade da cewa,eh wlh nima naso hakan Amma k’ila amaidasa gobe….kafin tayi mgn riyan ta shigo.
Nan suka gaisa da Abba,kafin yakoma Gurin Abdallah Yana shafa kan sa, Yana Masa fatan samun lfy…dg bisani sukayi sallama ,atare da mom suka fice.
Byn sun fita ne…. Saiga ammi ta fito dg bayan kujerar da riyan ke zaune tana ajiyar zuciya. ..riyan tayi ajiyar zuciya tace hankalina fa yatashi danayita ma yaya Hafiz flashing,amma anki adauke nefa…sai yanzun Dana kirasa akicin yacemun ai akan idonsa mom ta shigo parlourn nan..
Ahankali ammi tace nikaina wlh ,hankalina be kwantaba Saida aka d’auke nefa na canza Miki frash milk d’in na karb’i me maganin.
.gata maza kije kiyi floshing nata ,nibara natafi gd zanbi ta inda Hafiz ya shigo Dani,yanacan Yana jirana.ALLAH yashige Mana gaba ,ki kula sosai kiyi yadda komai zai tafi daidai…
Insha ALLAH ammi ,riyan ta fada had’e da nufar bed room d’in ta.
Ammi ta kalli Abdallah dake sauronsu Yana kallonta da ido yanason yin mgn sai bakinsa ke motsi.
Murmushi tayi had’e da babu godiya tsakaninnu kaji Abdallah dakai da Hafiz duk d’aya me aguna,ta fada sbd talura abinda yakeson fad’a Ken.
Saida riyan ta dawo , sannan ammi ta fita….
Washe gari…….
Share
BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????
???? AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????
Story & written by
mmn fareesa
Wannan shafin nakine mmn sudesss????
Not edited❌
p 31
Washe gari….da misalin karfe 6:30am riyan ta tashi “ahankali ta duba Abdallah tagansa tamkar mataccen da gske sbd ko kad’an be motsi balle numfashi”ta rasa meyasa take damuwa dashi da mugun jin tausayin da??”hijab tasaka ta fice da gudu dg part d’in Abdallah”
Tana tafe tana ihu da kururuwa harta iso parlourn mom”mom!mom!!mom!!! Riyan ta k’wala Mata Kira afirgice had’e da gigicewa tamkar da gske…lolx
Mom dake bed room nata tana jiran tsammani”tttanajin ihun riyan tasaki ajiyar zuciya had’e da yin wata dariya afili tace sainiiiiii!HASSU TSIYA TSABA!duk Wanda yaja Dani,zaifadi k’asa warwas…. adedenan riyan ta shigo afirgice tana kuka da hawaye lafiya lau,tamkar da gske…tuni mom itama tayi nata acting d’in”tayi saurin rik’e riyan had’e da cewa ke lfy,Miya faru??kisanar dani” Dan ALLAH kada kicemun wani abu yafaru da d’ana…ta fad’a hankali tashe…mom Abdallah baya numfashi ,inazaton ya mutuuuuuuu! tafad’a cikin kuka…. INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU’UN!sukaji muryar Abba ta daki dodon kunnansu. dake kokarin shigowa yafad’a cikin wani irin yanayi….ihu mom tasaka had’e da rik’e riyan ta na kuka “Abba yace muje Dan ALLAH in gansa….bejira amsarsuba yyi gaba cikin hanzari har Yana tuntub’e..da gudu suka Mara Masa baya zuwa part d’in Abdallah.,,,,
Agigice Abba ke dubasa,Yana Kiran sunansa hawaye na zuba afuskar sa...salati yasaka sbd yatabbatar bbu Abdallah d'a guda daya mallaka aduniya....su mom da riyan dake tsaye suna kuka had'e da kallon Abba" mom tace da gske alh ya mutu?"cikin wani yanayi Abba yace ehhhhh....basu ankaraba sukaga yazube k'asa su mamme.....
Bayan awa1da rabi….ammi ce fuskarta fal da damuwa had’e da tausayi…gefenta Hafiz ne rik’e da gawar Abdallah Yana kuka sbd bayan Abba ya farka yakira alh bukar agigice “byn yazone, atime d’in Kuma riyan ta Kira Hafiz sbd ta lura za’a binciki gawar sai sukazo ,tare da ammi ta dubasa ta tabbatar musu ya rasu…Wanda ko dubawar agaban mom akayita”tayi kashe ka tsare da komai…gefe guda Kuma riyan ce da fiddausi matar Hafiz tana rarrashin riyan akan ta yi shiru ta Dena kuka sbd har idanunta sun kumbura, Abba kuwa da k’yar yake mgn “daurewa kawai yakeyi,Amma zuciyar a cunkushe take…wani gefen na zuciyar sa nason yakira alh nura yayansa yasanar Masa mutuwar Abdallah… Amma wani Abu yadanne Masa zuciya yahana yayi hakan…
bayan an gama kimtsa Abdallah akasakashi mankara????aka Masa Sallah,kafin afito dashi zuwa makwancinsa na gsky”
Bbu laifi Masha ALLAH Abdallah yyi jama’a Dan D’an mutum baya kirguwa Gurin jana’izarsa”yyinda Hafiz ke lura da komai yadda ya kamata..
Bayan an rufesa kowa ya watse”Hafiz yyi kokarin komawa ,Amma be Bari kowa yaluraba ,ko Abba dayaga Yana kallonsa dazai tashi dg Gurin zaman makokin ,sai ya matsa gab da shi yace abba zanje air port natafo dawasu abokanmu dasukaxo yanxun…cikin damuwa Abba yace to Hafiz…jiki asanyaye Hafiz d’in ya wuce sbd mugun tausayin abban dayaji.,,,,
Kai tsaye acab’a ya hau”yakaisa makabartar nesa da makabartar ya ajesa”sbd tsaro “byn yasallamesa,yashiga ciki,bbu bata lokaci shida liman cikin Yan mintina suka hako Abdallah da haryanzun baya numfashi… sannan suka maida komai suka rufe tamkar ba’a budesa ba”sannan Hafiz yatafi yabar shi gun liman acikin wani d’aki dake cikin makabartar,sbd sai zuwa isha’i zaidawo tare da ammi a daukesa sbd liman yace sai yaga Abdallah ya farfado tukum zai badashi ,besan ko da gske ya mutuba ,sukayi k’arya Dan su hak’osa….
Haka aka cigaba da karban gaisuwa bbu dangin Abba ko guda ,saidai abokan arziki da mutanan anguwa da tauwagar mom,ammi da feedo da Hafiz duk nan suka yini ana karb’an gaisuwa.