AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yyinda mama zuwaira da Fatima sukaji labarin rasuwar Abdallah,hankali tashe sukazo gaisuwa”dukda riyan bataso sunjiba sbd gudun kada su narda umma gashi ba gske bane,burunta sai byn sun bar garin tukum ta kirata ta sanar da ita komai.

Bata nuna musu komai ba,har suka tafi gd”

Bayan sallar magrib gdn,yad’an rage hayaniya da cikowa har zuwa byn isha’i.

An gama Sallah,kasancewar abakin get akayi rumfuna anan wani yajasu sallar, Hafiz yyi ma su Abba sallama had’e da Kiran feedo da ammi ta waya dasuke cikin gd suka fito suka tafi.

Gidansa ya wuce sbd afara aje feedo Dan ba’asan meke faruwa ba”wayar Hafiz tayi ringing dubawa yyi yaga taslim ce kanwarsa dake kano tana karatu, kasancewar kafin ayiwa ammi transfer ta Fara karatun shiyasa suka barta tana zaune a hostel”
Dubar ammi dake baya yyi had’e da cewa ammi autarkice!
Murmushi tayi had’e da cewa oh taslim sarkin kulafuci k’ila ta kirani taji akashe shine ta kiraka”Amma barta inmunkoma na kirata..ok yafad’a had’e da yin parking abakin get na gdnsa..

Fitowa feedo tayi ,fuska bbu walwala sbd ganin bazai shi ga gd ba yanzun.
Ammi data lura da ita saitayi murmushi tasan Mai ciki da saurin fushi sbd cikin yad’an tasa,
Ahankali tace jeki ciki kinji y’ata!daya ajeni zai dawo…cike da kunya feedo tashige ciki tana murmushi…

Basufi 10 minit ba suka iso makabartar”parking Hafiz yyi suka shige “
Sun samu Abdallah yafara motsi Amma bedawo normal ba.

Hakan yasa liman d’in ya yadda, Hafiz ya dakkosa,mom ta bud’e Masa gdn baya yasakashi ,kafin su shige , Hafiz ya ja motar suna hamdala ga ubangiji.

Ahanya ya Kira riyan ta wayar Abdallah yasanar da ita komai na tafiya yadda yakamata.

Bayn sun iso gdn ammi,d’akin da Hafiz ke zaune kafin yyi aure nan yakai Abdallah .
Byn ammi tasake saka kayan aiki ta bincika taga normal”

Befi 15 minit ba yabude idanunsa Yana kallonsu,da sauri Hafiz yace yayadai ,komai normal??”d’aga Kai yyi alamar eh.

Hakan yasa Hafiz ya taimaka Masa yyi brush da sallolin dake akansa,tabashi tea mai kauri yasha ,kafin ammi tamasa allurra bacci ,sbd dare yyi balle ayi Masa wanka,Kuma Hafiz yace saidai riyan ta Masa Amma shi Yana jin nauyin hakan.

Sai ammi tace to yakira riyan din , yasanar da ita gobe byn sallar asuba ta sato jiki ta fito ,su had’u bakin titi sai yakawota tayimasa wankan ,sai tasaka nik’ab ta koma…

Da wannan shawarar sukayi sallama da ammi sbd ganin yadda feedo keta faman jera Masa Kira…

Ita ammi sai asannan ta Kira autarta taslim……


Washe gari ,kamar yadda suka tsara haka akayi komai”byn riyan tagama shirya Abdallah agaggauce ta basa tea fuskarta adaure sbd ta lura sai wani kallonta yake Yana kashe Mata ido”yyinda Hafiz dake jiran tagama su wuce,yake satar kallon su,sbd tuni ya fahimci mutumin nasa ya zurma dg ciki….lolx…saiso yake su had’a ido Amma Taki yarda sbd yau wata irin kunyar Abdallah takeji had’e da tsoronsa sbd yau bbu komai ajikinsa tamasa wanka???? ,ganin tak’i yarda su had’a ido gashi ta daure fuska sai yyi zaton kota Fara gajiya dashine”sai ya kalli Hafiz yatambayesa da ido Wai mi takema fushi?”
Oho”Hafiz ya fad’a had’e da d’age gira”itadai riyan batayi mgn ba,idonta akan red lips nasa tana bashi tea….Wai riyan ko kingajine da kula da abokina me”Naga kin wani daure fuska?”
Cewar Hafiz sbd yalura abinda ke ran Abdallah kenan.
Murmushi tayi had’e da cewa ah ah Yaya Hafiz,kawai dai Ina kewar ummana ne, ai bazan gaji da kulada shiba sbd irin d’unbin ladar da nike kwad’ayin nasamu.
Sannan bazan gaji da kulada shiba insha ALLAH har ya warke mu rabu…..sbd bazan iya barinsa ahakaba Dan D’an Adam darajace dash….. kwarewar da Abdallah yyi da tea d’in datake basa ,yasakata k’in k’arasa maganar ta….

Share…

BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????

???? AUREN WATA SHIDDA????

????????????????????????????????????????

Story & written by
mmn fareesa

Not edited❌

p32

Murmushi kawai Hafiz keyi”azuciyarsa yace yauwa yarinya gara ki Fara ramawa “wani abunma sai ya warke”
Abdallah kuwa maganganun riyan suka sakashi k’ware wa, azuciyarsa yace tabbas riyan Bata SONA! Tunda tana maganar rubuwa… yafad’a had’e da k’ok’arin hararan Hafiz daketa murmushi…tashi Hafiz yyi had’e da cewa to marigayi AK saina sake dakkota gobe tasake maka wankan harzuwa ayi adduar bakwanka… yafad’a Yana dariya… yyinda riyan ke goge Masa tea din daya zubar Masa ajiki”
Duk yadda Abdallah ya so su had’a ido da ita” Amma tak’i yarda”harya hardai ya hakura suka fice itada Hafiz…


Bayan kwana7 “Hafiz ya buye number yarufe account d’in Abdallah kud’i basa shiga basa fita sbd ganin mom ta cire dubu dari biyar, sannan ya had’a duk takardun kadarorinsa da campany d’in sa ya b’oye ma Abdallah sai byn komai yalafa tukum….

Riyan zaune kan carpet da hijab ajikinta ita ga Mai takaba” kusada ita kan kujera mom da hjy ikilima ne zaune..suna wani yatsina sbd mom tafara gajiya da riyan,a yau takeson sanar da Abba yakamata riyan ta koma gdnsu tunda anyi7…sallamar wata Mata ta katsewa mom tunanin ta “sanye take da safa da hijab duka bak’ak’e da farin glass afuskarta”kallo d’aya zaka Mata kasan Yar shi’a ce”da murna riyan ta tashi tana cewa lahh goggo!sannu d xuwa..ta fad’a sbd tagane ammi ce”
Zama tayi kan kujera , yyinda mom da hjy ikilima keta wani Shan k’amshin”byn sun gaisa “goggon ta bukaci abata riyan sbd ta maida ita gd tayi takaba! Washe Baki mom tayi sbd dama haka takeso abata guri ta Wala yadda ta gadama…tuni ta amince ,tacewa riyan ta je ta kwaso kayanta apart d’in Abdallah tabata keys sbd ta anshe keys d’in da wayoyinsa guda 2 danma riyan ta yi dubarar boye 1 da ita suke mgn da Hafiz”
Gurin debo kayan ne dg nan ta had’a da wasu na Abdallah tasaka akasan nata kayan , sannan ta fito sukayi sallama da mom byn tabasu dubu 10 Wai suyi na mota…kafin su amsa Abba yashigo yaji Wai riyan zata tafi…beso hakanba , sannan yahana abata dubu 10 yabata dubu 100 “sannan yace byn tagama takaba tadawo za’a raba gado abata hakkin ta….mom na kokarin mgn hjy ikilima ta k’yafta Mata ido tayi shiru…

Har get Abba yarako su riyan Yana Mata godiya da saka Mata albarka, har suka fice dg gdn “ya k’udurta azuciyarsa inhar riyan zata amince to zai saka Hafiz ya aureta sbd samun irin yarinyar sai antona”yasan Hafiz zeji dad’in Zama da ita, sannan yasan tayi hakuri da Abdallah kafin yasamu lalurarsa”har hawaye Saida Abba yaji…

Byn fitar Abba mom tayi tsaki had’e da cewa wlh bazata dawoba sbd zansa amantar da ita mu,balle hr araba gadon da ita,shikuma wata6 nabasa kafin yabi byn D’ansa…hhhhhhhhhhhh????
???????? suka shek’e da dariyar mugunta suna jin duniyar ta zamo masu tamkar sabuwa.

Bayan sun tsagaita dariyar”hjy ikilima tace Toni in ankammala komai miye nawa kason adukiyar Abdallah?”

Kafin mom tayi mgn”anyi sallama”d’ago wa tayi had’e da kallon wacce ta shigo!

Goggo ce”fuska asake ta ce hjy nayi mantuwa Dan ALLAH wayata na b’ari”ta fad’a had’e da nunawa wayar da ke
Cikin kujera inbaka luraba baza ka gantaba”tayi saurin d’auka had’e da cewa sai anjimanku.

Suka tab’e baki had’e da rakata da harara…

Ammi na fita tasamu riyan inda tabarta” sannan suka hau adedeta.

Abakin get na gdn ammi ya ajiyesu,suka sallamesa had’e da shigewa cikin gdn.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button