AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

A bak’in kofar waiting parlour suka Kira Hafiz yazo ya bud’e musu, sbd tunda aka kawo Abdallah agdan basu barinta bud’e sbd gudun idon sani yashigo yagansa …
Zama sukayi , yyinda Abdallah yakafe riyna da ido ,tayi kyau Masha ALLAH cikin riga da zani na jar super da hijab ja har k’asa..jiyake inama zai iya mgn…muryar ammi ce ta katsesa gun cewa to bara nafara saka muku recording d’in kuji….
Kaf suka saurari suk maganganun mom da hjy ikilima har karshe…kafin ammi ta dubi riyan da Abdallah tace gobe insha ALLAH zaku tafi sbd munyi waya da mlm jiya ,sai kin kula da addua shima zai dukufa da addua muma haka kunadai jin mugun nufinta ko?”
Abdallah ya kafe Hafiz da ido Yana tambayarsa in wata shidda yyi be warkeba kenan mom zata kashe abbansa?”
Girgiza Kai Hafiz yyi had’e da cewa insha ALLAH kafin lokacin ka warke AK ALLAH ya shige Mana gaba.
Suka amsa da Amin, sannan ammi tace ai kada kadamu Abdallah dama nasn zakayi wannan tunanin,Kuma muma zamu rik’a lurar maka da mahaifinka kaji ko?
Yad’aga Kai alamar eh yajin”
Ahankali ammi tace Zan sanar da ku wacece HASSU TSIYA TSABA sbd nafison kuji kafin kutafi….
Hafsat sani shine cikakken sunanta,suna zaune a unguwar Jan bulo itada iyayenta”iyayenta talakawane Amma akwai wadatar zuci,dukda mmnta nadason abin duniya”
Hafsat yakasance masifaffa hakan yasa ake Mata lak’ani da HASSU TSIYA TSABA!yarinyace ita Mai matukar kwad’ayi, had’ama ,son abin duniya ,burunta ta auri Mai kud’i sb d tazamo wata acikin k’awayenta,hafsat bak’a ce ba k’irinba, sbd tanada D’an haske…Kuma bazamu kirta mummunaba bbu laifi tanada kyau tuni tayi amfani da shawarar k’awayenta akan tarika bleecing”tuni tayi bau da ita,batayi karatu Mai zurfiba iyakarta J S CE ta watsar….nakasance makotansu sbd gdna na kallon nasu alokacin da na auri mahaifinka Musa,kowa da naja’at Musa ake kirana,byn zuwana anguwar hafsat ta ruk’a zuwa musammun dataga bbu laifi munada wadata “agd na take cin abin Rana Dana dare da Naga mijina zai dawo zance ta tafi”Bata zuwa islamiya inhanturata sai tataho gdn,Kona ce ta tafi batazuwa har nagaji na k’yaleta…
Wani lokacin mahaifinta yakamata ya Kinga Amma Bata zuwa makarantar”ana cikin haka ta had’u da wani saurayi Mai suna Suraj ,Wanda bbu laifi yanada abun hannunsa Amma ita ta Raina Abu daya yasakata kulasa shine kyawun sa,Amma tunda taga bbu mota bazata kulasa.
Tazo tasanar Dani amatsayina na uwar d’akinta , shawara nace inyanada halin kirki ta yarda harsuyi aure Mana.
Murmushi tayi had’e da cewa aurefa kikace?ai wlh bazan auri Suraj ahkaba albashinsa dubu 85 awata,sai yazama wani Abu zaidai ruk’a tatsarsa kawai inyazama wani Abu na auresa,danbdubu 85 ai baiwuce asati nagama dasuba “su amaleji kawai, inkuwa,jiya iya yaune to nacanza shek’a.
Girgiza Kai nayi had’e da cewa hmmm ALLAH ya shiryaki…
Haka kuwa ta kasance , hassu kullum saita Rok’i Suraj wannan “gobe wancan jibi wancan,shikuma dayake ALLAH ya jarabetasa da sonta begajiya dayimata hidima komai nasa akanta yake k’arewa,inyabata tayagarma mamanta wani Abu dg saitaki yimata fad’a inkinga ammata fad’a to babantane.
Shikuwa Suraj dama mahaifiyar sa ba ta raye sai ubansa ,bbu laifi Yana taimaka Masa,Amma Koda yahadu da tsiya tsaba ai saiya Dena.
Gefe guda Kuma Suraj nacikin maza masu yawan buk’atar mace ,hakan yasa yasanar da hassu cewafa gsky yanason turo magabatansa sbd yanason kasancewa da ita.
Fau fau fau tace ba hakaba,wlh bazatayi aure ayanxunba ta tsofe abanza ,hakan yasa sukayi fad’a da ita, sbd ta sanar Masa ta Raina samunsa ,wato albashinsa daya ke dauka sbd Yana teaching…
Kwana3 sukayi basuga junaba ,sai a lokacin tasan tabbas tana sonsa,hakan yasa ta nemi shawara gun kawarta ikilima sbd tasan intazo guna zanbata shawarar kirki.
Aidama haka ikilimar keso sbd ita tana bin maza ita Kuma batayi.
Hakan yasa tabata shawarar yo miye aciki kawai kucigaba da huddarku dashi indai zai yarda ,har zuwa lokacin da zakuyi aure tunda jarababbe be…
Jikinta asanyaye tace Mata to Amma Ina zamu ruk’a haduwa ne?
Gidan hajjo”(dillaliyace Kuma Yar duniya,anashiga gdn da Mata tabada d’aki abiyata)
Tundaga wannan lokacin Suraj ya maida hassu tamkar matarsa kullum suna atare gdn hajjo suna aikata Masha’a ALLAH katsaremu.
Nikuwa bansan komai ba gameda da hakan Saida abbanka yasanar da ni abinda hassu ta koma sannan yace nasanar da ita kada Takoma shigo Masa gd.
Ana cikin hakan mahaifiyar ta tarasu sakamakon ciwon kensa,byn tayi 40 ta koma ruwa.
Wani lokacin insukayi fad’a da Suraj yyimata mugun duka,Amma da dare tare zasukwana.
Lokacin da mahaifinta yafahimci inda tasaka gaba saiya koreta dg gdnsa dama bayn mutuwar mmnta yyi aure.
Hakan yasa ta koma gdn hajjo da Zama suka watsewarsu da Suraj ,dukda haka tana kuka samari Amma bata hud’d’asu sai da Suraj kawai take hudd’a.
Bayan na haifeka ,baza ka wuce shekaru 2 da rabiba.
Asannan ne hassu ta had’u da Alh kabir girma…..
Wash nagaji wlh muhade next page danjin ta Yaya Hassu ta had’u da Alh Kabir girma….
Share
BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????
????AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????
Story & written by
mmn fareesa
Wannan shafin nakune SURRY BABY&RAFI’ATU…kuyi yadda kukeso dashi Ina mugun jidaku????????
Not edited❌
p 33
….Ayau yakama Friday akuma ranar ake dinner party na bikin Dan sarkin kano”hakan yasa aketa zumudin zuwa gun dinner d’in.”
Hassu ba’a gaiyacetaba ,haka ta dauki wanka na kece raini ta tafi Gurin dinner d’in dukda Suraj yaso hanata zuwa Amma ta kafe sai taje…
Byn komai ya hallara MC yakira babban abokin ango sbd yabada tarihinsa….wato ALH KABIR GIRMA”hassu ta d’ago kanta sbd son taga waye shin Dan taji Marika nata kuzuzutashi….cak numfashinta ya tsaya sbd tozali datayi da kyakykyawar surarsa fari doge yyi kyau bbu karya ,cikin shadda light blue yar ciki da babbar riga” ga wani hand some asaman kafad’ar sa,yyinda hannunsa guda ke cikin na wata kyakykyawar mace koba tamtama matarsace,itama tana sanye da shadda doguwar riga kalar tasa”kallo d’aya zaka musu kasan suna matukar kaunar junansu… yyinda matar ta fito da rafa ta Yan dubu dubu tafara rabawa marok’an…
Har yagama jawabinsa yaja matarsa da D'ansa(Abdallah da mamansa) idanun hassu na akansu"sbd lokaci d'aya taji yyimata ta ko Ina , musammun sbd ta ga yanada zufar aljihu wato(kud'i)
Har aka tashi dg Gurin dinner d'in,idonta akansu , takuma tabbatar yanawa iyalinsa son dabaya was kansa shi...
Acikin kwanakin tayi binkice akansa taji Shiba Dan garin nan bane shida maatrsa aiki be yamaidosa anan,Kuma yaronsu 1 Abdallah Dan shekara3 da rabi,tuni ta je gun boka yabata wani kwalli da turare ta fesa ta shafa kwallin,daya had’a ido da ita ,yakuma shaki turaren angama zai sota ya aureta.
Sunsha rigima da Suraj kafin ya amince ,saidatace zata ruk’a yagomasa rabonsa dakuma cigaba da hud’da dashi tukum ya amince.
Haka kuwa akayi tashirya komai taje office nasa ,suna had’a ido da ita yaji tamkar ya mutu sbd ita.
Acikin wata 2 akayi komai aka gama ,inda tanuna Suraj amatsayin yayanta,hajjo mahaifiyar ta,saitace ubanta ya mutu, sannan ta ci alwashin tarwatsa matarsa intashiga gdn ,sbd likita ya tabbatar mata mahaifar ta ta lalace Bata ita haihuwa sbd tulin magungunan Hana d’aukar ciki datake Sha..
Hakan yasa ta ci alwashin rabasa da matarsa da gdn.
Lokacin da nasami labari” auren be wuce saura sati1 ba,naje na Mata nasiha har inda take nabata shawara taje ta Rok’i mahaifinta yafiya ,tace to Ashe batajiba”