AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan auren ,Ashe matar nada yaron ciki dabaifi 3month ba ,sai dokin cikin uban keyi…Koda hassu ta lura da hakan saitafa Kai sunnsa gun boka tafara mallakesa alokacin mamanka tashiga wani hali gashi alokacin akayiwa alh kabir girma transfer yakoma kaduna da aiki,sukabar garin kano”
Bayan komawarsu can ,hassu tarabasa da danginsa da matarsa saidai aka nemeta aka rasa sbd kurciya ta Mata”Amma tabar Abdallah annan, alokacin shekarsa 4″nan hassu taja sa ajiki sosai yasake da ita har ya manta da mamansa ,kamar yadda ubansa ya manta da ita…

Hakan yasa dangin mamanka “basu San inda abbanka yakomaba,sbd sunxo say bbu addadi neman mamnka sai ace musu suntashi sbd wasu ke agdn zaune byn tashinsu..
Yyinda dangin mahaifinka suke zuwa Amma bbu sakin fuska gurun abbanka da hassu sai wulakanci da tozarci,sunason tambayarsa Ina mamanka Amma bbu fuska.
Kanada shekara 18 aka kaika Cairo karatu “acan kayi degree naka ,dg nan ka koma ingila kayi degree na2 acan , sannan duk azatonka hassuce mahaifiyar ka.

NiKuma dalilin dayasa nasan katafi karatu acan,sbd alokacin shima Hafiz can yatafi,munkawosa airport nida mahaifinsa,mukaganka kaima zaka shiga jirgi da abbanka,anan abban Hafiz kecemun Kinga Dan mijin hassu can,ko Ina zashi?”
Nace k’ila shima cairon zashi”dg nan byn tafiyarku ,Inna Kira Hafiz ya ke sanar Dani cewa ai skul d’aya kuke Amma kowa da department d’insa Amma a hostel guda kuke dashi”
Hakan yasa kuka Zama abokai sosai ,baku rabuba Saida ,kukayi degree,shiyadawo gd,Kai kawuce ingila” alokacin dakadawo kasami mijina yarasu,hakan yasa nakoma naja’at haruna”byn dawowarka ne akamun transfer nadawo garin nan da aiki…..
Wannan shine asalin hassu dakuma tarihin Abdallah,Abu dayane banfada mukuba shine mutuwar uban hassu dakuma , ikilima ta dawo gdn hassu da Zama “har suka samu wani Mai kud’i ta auresa da asiri….

Ajiyar zuciya Hafiz yyi had’e da cewa lallai mutum abin tsorone”to Amma ammi ta Ina zamu soma gano wacece mahaifiyar Abdallah da danginta??”

Ai insha ALLAH Hafiz zaa gane “mudai fatanmu shine samun saukin Abdallah,sbd ai kun sanarmu a yadda kukaji tace inhar Abdallah ya warke to ciwon zaidawo ajikinta,Kuma alokacin zata ma kanta tonon asirin abinda tayi tunda Bata ahaiyacinta,Kuma tace inharta fad’i da bakinta ita tayiwa mahaifiyar Abdallah kurciya to asirin zai karye”kaga zata waiwayi gd,dukda nasan insha ALLAH in tanada Rai to kano zata Fara zuwa hakan yasa in Abdallah ya warke zamuje kanon har gdn da abbanka yafara Zama musanar dasu intazo ga number sukiramu ,kada insha ALLAH komai zaizo da sauk’i,fatanmu ALLAH yasa tana a raye..

Gaba d’aya sukace ameen…

Abdallah kuwa sai hawaye yake na tausayin kansu”ALLAH yasa cikin da mamansa ta Bari be zubeba, yafad’a azuciyarsa…

Rarrashinsa ammi da Hafiz sukayi tayi,kafin ayo Masa alwarlal magrib suka gabatar da Sallah……

Washe gari tunda wuri riyan ta gama shirya Abdallah Wanda ta lura yau Yana cikin damuwa sosai…

Kan kekensa ta turosa har zuwa parlour suka gaisa da ammi da Hafiz (wand ayyiwa feedo karyar zashi Lagos)sbd shizaiyi driving d’in su….

Bayan tabasa tea da fresh milk ,itama ta karya a gaggauce ,kafin ammi taja ta d’aki ,yamata nasiha cikin minti 15 akan ta kula da kanta da Abdallah bbu ruwanta da kowa Kuma duk abinda Bata ganeba ta kirata da wayar Abdallah…

Allurar bacci ammi tayiwa Abdallah aka sakashi gdn baya aka Dora Masa Kaya marasa nauyi(sbd gudun kada masu tsaron hanya Yan garin su duba su gansa hannun agogo ya dawo baya.

Acikin boot sukasaka kekensa da kayan sawarsu sai irinsu kayan tea da katan na fresh milk sbd su ne zai iya sha ,sai gdn sauro sbd k’auye ne garin…dawasu abinda zasu bukata dakuma kud’i duk akabawa riyan inji Hafiz dukda tak’i karb’a saidai yanuna ransa yab’aci tukum ta karb’a..

Cikin ikon ALLAH komai ke tafiya lafiya suna waya da ammi a hanya”

Basu iso garinba sai byn sallar la’asar”sunyi tafiyar awa 7″

Abdallah dake zaune gdn baya ,kasancewar bedad’e da farkawa ba sbd Hafiz ya budesa da sukayi nisa sosai yasan bazasuga idon saniba”

Bayan sun yi parking”Hafiz da riyan suka Fara fitowa , Hafiz ya dubesu yace Ina zuwa pls,kafin yashige wani Dan madaidaicin gd,me zaure dogo ,yasha Suminti da dakali babba akofar gdn”bbu laifi garin akwai iska Mai Dadi Kuma bawani mugun k’auye bane akwai Yan boko ma’ana Yan k’auyen nazuwa bunni karatu.

Ajiyar zuciya Abdallah yyi Yana k’arewa Gurin kallo azuciyarsa yace ikon ALLAH Ni Abdallah yau Kuma anan zanyi rayuwa! lallai naga rayuwa…isowar Hafiz da wani matashin magidanci da Kuma mlm yakatse Masa tunanin da.

Nan Hafiz ya fito da keken aka aza Abdallah riyan dake tsaye tafara jansa da nufin su shiga ciki.

Salisu babban Dan mlm HABIBU ne “kallon riyan yyi Yana Taya Hafiz shiga da Kaya yace wannan fa?”yafad’a lokacin da riyan ke gaidasa ganin yanata aikin kallonta.

Fuska bbu walwala Hafiz yyi saurin cewa matar marar lafiyarce sbd yason salisu da son Mata ,gashi Kuma yalura Abdallah ya had’e rai ,fuskarsa murtuk,sbd ganin wawan salisu na kalle Masa riyan”wani malolon Abu Mai zafi da d’aci yatsaya Masa akirji….

Itadai riyan batace….

Share

BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????

????AUREN WATA SHIDDA????

????????????????????????????????????????

Story & written by
mmn fareesa

Wannan shafin nakune”Queen minart &teema&mmn abdussamad????????

Not edited❌

p34

“”Riyan batayi mgn ba tacigaba da tura Abdallah har suka shige tsakar gdn”sallama tayi fuska asake”wata dattijuwar mace tayi saurin amsawa tana Mata Mara,byn sun gaisa Hafiz ya shigo tare da su mlm,aka shimfid’a tabarma aka sake gaisawa sannan mlm yanunawa Hafiz wani d’aki dake cikin rumfa yace ga d’akin bak’in”da to ya amsa yyinda riyan ta musu godiya kafin su shige d’akin da kayansu…

Dakine falle guda ashafe yake da sumunti ga ledar k’asa sabuwa sai katifa k’atuwa itama sabuwa daidai kwanciyar mutum 2″ sai gefe fanka Yar girkece anjonata tana aiki kasancewar sunkawo nefa.
Trolley d’in su guda2 riyan ta aje,ta zauna gefen katifar tana ajiyar zuciya.

Hafiz ne yakai Abdallah yyi alwalla,suka Yi azahar da la’asar”kafin Inna mairo(matar mlm ) ta kamusu tuwon masara miyar kubewa busassa da ruwan tulu Mai sanyi,shikuma Abdallah aka kamasa fura damamma dataji kindurmo da madarar shanu”
Saida sukayi Kat “sukayi hamdala yyinda haryanzun fuskar Abdallah adaure take , Hafiz nason yin dariya Amma yadaure sbd ya lura har yanxun kishine dank’are azuciyar Abdallah.
Ruwan dumi Hafiz ya saka Inna mairo ta had’a aka wanke bayin , sannan yatura Abdallah ya kaisa toilet ,kafin yakira riyan tazo tayi Masa wanka…

Kafin su gama Hafiz ya sakawa d’akin labulaye da shimfid’a bed sheet kan katifar yashare d’akin sbd yason AK akwai son komai yagansa very need”
Byn tagama shiryashi me sukayi magrib da isha’i….

 Da dare kasancewar anan Hafiz zai kwana washe gari zai koma da safe"ad'akin mlm dake soro akamasa shimfid'a Yana wayarsa da feedo Yana murmushi... Hafizu kaje gun yaron nan naga bakinsa na motsi da alama ko yanason ganinkane"cewar mlm dake tsaye akan Hafiz,sbd yaje yayiwa Abdallah addua yashafe Masa jiki yabasa rubutu...shine yalura da hakan.

Tashi Hafiz yyi had’e da tsinke Kiran feedo”yanufi dakinsu Abdallah…. Abdallah ya samu kwance gefen katifar ga Gurin kwanciyar mutum1 anbari “yyinda riyan ke zaune kan carpet d’in Sallah fuskarta bbu walwala”duka da kallo yabisu,sbd yafahimci,riyan bazata iya kwana ashimfida 1 da Abdallah ba”ahankali yace sannunku!Ashe bakuyi bacciba?”dama nazo yimuku Saida safene…
Eh wlh “dama nace kizan Sami tabarma saina shimfid’a na kwanta?”yo meyasa bazaki kwanta akan katifarba?”
Ai Zan yakirasa,gara abarsa yasake ko”Abdallah ya kalli Hafiz da ido ya roke’sa akan y rarrashi riyan tazo sukwanta, hararan sa Hafiz yyi had’e da make kafad’a alamar ah aha bbu ruwansa…zansamune ko kuwa? Cewar riyan tana hamma”bara mugani ko’a samu , yafad’a hade d fita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button