AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da misalin karfe 5:35pm riyan na zaune atsakar gd bayan tagama yiwa Inna mairo tankad’an garin tuwo tana game da wayar Abdallah”
Can wayar tafara ringing” da sauri riyan ta duba taga ummace!
Murmushi tasaki had’e da dagawa ta nufi dakinsu”nan suka soma gaisawa…cikin wani yanayi na damuwa umma tace riyan kina Ina?Ina fatan badai duniya kikashigaba ko? Sbd jiya muka dawo dg k’auye yaunaje gdn mama zuwaira mugaisa sai take mun gaisuwa nace Mata waya rasu?”tace mijinki!nayi mamaki had’e da sanar Mata bansaniba,tafaru ta Kare riyan ta fada azuciyarta…
Salati riyan ta yi hade da cewa ki kwantar da hankalinki umma bbu inda natafi asalima Ina tare da mijina..da sauri umma tace miyake faruwane kinsani aduhu ?”yanxunfa dg gdnsu mijinki Nike ,nayiwa mahaifiyar sa gaisuwa na tambayeta kina Ina tace ai yayar mahaifiyar ta tazo ta tafi da ita,Amma na lura batason nice mamankiba”hankalina yatashi Riyanatu bandaice Mata komaiba nabar gdn da niyar nakiraki awaya naji kina Ina ne…ajiyar zuciya riyan ta yi sbd jin umma Bata lalata musu aikiba.
Kallon gefenda Abdallah ke bacci tayi taga baccinsa yake.
Ahankali tace wlh umma bbu lfy Amma zanmiki bayani ki kwantar da hankalinki Amma kada kigayawa mama zuwaira da kowama Wai mijina na araye sbd ko abbansa yadauka ya mutu !zankiraki anjima namiki bayani…batajira me umma zatace ba ta kashe wayar…
Meyasa bazakiyi Mata bayanin yanxunba? Muryar Abdallah ta daki dodon kunnanta”cikin zaro ido had’e da Shan jinin jikinta ta d’ago kanta suka had’a ido da sauri ta janye nata idon sbd wani yarrrrrrrrrrrr!dataji ajikinta”kinyi shiru!kisanar da ita gsky kodan hankalinta ya kwanta…
Ahankali tace to… sannan ta Kira umma “kaf tamata bayanin komai.salati kawai umma keyi tana jinjina wannan lamari tamkar almara”ta tsorata da D’an Adam, sannan ta yarda tabbas akwai k’addarar data saka suka baro garinsu”gashi sunfara ganinta sai fatan ALLAH yasa su ida ganin karshenta lfy…tayiwa riyan nasiha sosai dukda riyan Bata fad’a Mata auren contract sukayi da Abdallah ba, Kuma shima yaji dad’in kin fad’ar datayi.

********

Mom ce tsaye fuska bbu walwala”yyinda hjy ikilima ke zaune jigum tamkar masu zaman makoki” cikin bacin rai mom tace nayi mamakin meyasa hakan tafaru?Amma ba ri ubansa yadawo dukda shi yasan banina haifesaba Amma ai bazaimun musu ko hanani iko da abunsaba”
Hjy ikilima ta karbe zancen da cewa Ni wlh abinda yatsoratani shine rufe account d’in da Kuma b’oye number d’in daakayi amfani da ita”kodai wani yasan me muke nufi…
Cikin faduwar gaba mom tace Kai haba!bana tunanin hakan gsky”Amma Bari Alh yadawo naji koshi yarufe account d’in Abdallan”
Haushin guda bbu kud’i da yawa guna ,gashi Suraj ya matsamun akan 3 million yakeso”kinsan innace alh yabani zai tuhumeni akan mezanyi dasu ,Kuma bansan amsar dazan bashiba”
Haba Mana karkibada Mata saikace ba TSIYA TSABA ba!kusamu karyan dakika Masa Mana ki karba may bee dg baya musan yadda zamu yi abude account d’in Abdallan,sbd Kinga inbaki bashiba akwai matsala, sannan in kikayiwa alh maganar account d’in Abdallan shima zaimiki wani zato ko fassara,Koda kina ganin ki Masa asiri azuciyarsa zai Yi wani zato daban Koda ke bazaimiki mgn ba….
Ajiyar zuciya mom tayi had’e da cewa wannan gsky ne aminiya”ta fad’a suna dariyar mugunta….

######

Bayan wata 2 ,kwanci tashi asarar Mai Rai” yanxun dai su riyan da Abdallah watansu 2 kenan akauyen karaye”bbu laifi jikin Abdallah saidai muce Masha ALLAH !sbd yanzun kusan abinda yarage ajikinsa kad’an ne Dan yanzun hannunsa da kafarsa suna aiki da motsi har kansa ma zai iya turawa Yana akan keken..yanxun tashi yyi tafiyane kawai matsalar sa,shima Kuma mlm yad’age Gurin basa taimako, yyinda shida riyan sakaci da adduar neman tsari da azkar…

Har iya yanxun riyan Bata sakarwa Abdallah fuskar yyi Mata wata mgn dashafi soyayya inma yyi sai tabasar”inkuma Hafiz ya zo dubiya yaroki yatayasa camphane “sai yayi k’ememe yace bbu ruwansa…hakan yasa Abdallah ya Dena rokarsa”sannan itama yadena nuna soyayyar sa yabar wa yasamu k’afa tukum dukda wani lokacin say tari yakan kwatanta intazo basa Abu yahad’a da hannunta yarik’e”saita daure fuska ta kwace hannunta”ranar da yarik’e hannun ta yafisgota tafad’a ajikinsa yaga bacin ranta “batace komaiba sai kuka kawai “hakan yanuna Masa cewa tabbas riyan Bata SONSA takuma tsanesa Wanda abad’ini ba haka bane..
Gefe guda Kuma mlm yahana salisu ahiga gdn sbd lura da yyi inhar Abdallah ya ganshi musammun in riyan nagun to besake mgn ko faraa,in salisun Kuma yamasa mgn da k’yar yake amsawa…hakan yasa mlm yace insuntafi yadingashigowa sbd yafahimci Abdallah nakishin iyalinsane, sannan Kuma bega laifinsaba…

Yau yakama juma’a”bayn sundawo dg masjid, Abdallah yacewa Inna mairo adama Masa fura,bacin ga riyan wacce ta nunama ko ajikinta Dan talura yau wani shan k’amshi yakeji ga wani kyau namusammun da yyi sbd anmasa aski da gyaran fuska…har cikin ranta taji bbu dad’i Amma saita share..

Yyinda gogan keta aikin satar kallonta”sbd tunda yake da riyan sai yau yamata kallon tsab “wata zazzafar kaunar ta na fisgarsa”jiyake kamar yajanyota jikinsa Amma ba damar hakan”ita kuwa Sarai tasan Yana kollonta sbd ta na lura ta gefen ido.

Inna mairo ta mik’o wa riyan cuein fura had’e da gidauniya da nono kindirmo aciki tace gashi kidama Masa.

Dagowa tayi taga ita yake kallo”harara tasakarmasa,sai yyi murmushi had’e da d’age Mata gira guda”

Lumshe ido tayi ,kafin ta cigaba da dama furar har ta idar akan idon Abdallah.

Shikanshi Yana mamakin wannan kauna dayakewa riyan “

Ko sadda take Masa aiki ,in yasata kuka bayajin dad’i ga tausayinta yanaji,dukda yasan atime d’in baso bane”sannan yanajin dad’in yadda take kiransa da Yaya Abdallah…

Tura kansa yyi har cikin d’akin sbd ganin ta tashi ta shiga d’akin.

Ahankali yace madam abani “tunda baza’a cemun gashiba…

Tashi tayi had’e da turo baki tace aibaka tambayaba”

Hmmm Anya ke ba auta bace my riyan?”
Mik’o Masa tayi had’e da cewa me ruwanka da hakan”

Murmushi yyi yace nidaiko riyan ya?

Eh din meza iyayimun?”insha ALLAH daka warke anan gdn zaka sallameni ,bazan bikaba ,balle kamun mugunta.

Ko ka manta da azabtar Dani dakayi adaren da aka kaini gdnka?

Shiru yyi jikinsa yyi sanyi sbd bemason tuna wannan abubuwan….

Waiwaye…

Share

Zakuji shin maman Abdallah Ina tadosa bayn fitarta dg gdn alhj Kabir girma?”
Tana raye kobata raye?

Muhade a next page…

BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????

????AUREN WATA SHIDDA????

????????????????????????????????????????

Story & written by
mmn fareesa

Not edited❌

P 37

Waiwaye

Tunda tabar gd Gurin karfe 5:30 am na asuba taketa Jan trolley dinta guda2 da hand bag nata “tana tafiya kawai batasan Ina zata dosaba?” gaba d’aya taji garin yamata zafi tamkar ana sukan jikinta da allura”ga kunci da bacin rai tana ji ,Wanda batasan Kona meye bane”ge fe guda Kuma Tama manta ita wacece”
Tafiya kawai take Yi “tun gari da duhu har Rana ta fito.
Tana bakin wani titi taga motoci na wucewa”can taji wani mutum nacewa ADAMAWA ko YOLA…cak tatsaya had’e da juyowa tanufi Gurin motar…
Karfe 6:25 suka d’auki hanyar YOLA….tunda tashiga motar Bata um bare um um tayi gum da bakinta tana Yan kalle kalle…can wata yarinya budurwa dabata wuce shekara ashirin zuwa da d’aya”sai kallonta take , yyinda itama yarinyar tana cikin damuwa.
Sunyi tafiya Mai nisa akatsaya Dan aci abinci ayi Sallah”
Bayn sun gama sallar gefen wani guri da ake siyar da abinci”sai sai ummin Abdallah ta tashi taje ta siyo plate d’aya har zata Fara ci”sai takula da yarinyar ce kadai ke Bata siyi abincinba!dakuma alama tanason abincin “da hannu ta yafitota”bbu musu ta taso tazo gurinta.
Ahankali tace ke miyasa bazaki ci abincinba?”shiru tayi hawaye na zuba afuskar ta”cikin damuwa tace banida kud’i!asalima ko kud’in motar bandashi Kuma bansan inda zaniba…. tafad’a had’e da rushewa da kuka.
Rarrashinta ummi tayi had’e da siyamata abincin “kafin sokoma mota suka dauki hanya..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button