AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hannunta yasaki had’e da Shan ruwansa,ita Kuma ta juya zuciyar ta fal da tausayinsa,tasan tabbas be kamata tahada Masa zafi 2 ba tabarsa da abinda ke damunsa…saidai fa Bata tunanin tagama koya Masa hankali , sannan Kuma sai yafad’a ma iyayenta da kanshi cewa AUREN WATA SHIDDA sukayi yakuma bawa ummanta hakuri…tukum takejin zata iya karb’an soyayyarsa Dan yasan tana daraja …Amma yanzun da sauransa …
Riyan bazaki hakuraba Dan ALLAH?
Me kakeso nace maka Yaya Abdallah?mubar maganar dan ALLAH ,addua yakamata muyi akan ALLAH yabaiyana Mana mamanka kawai dakuma samun lafiyarka….keba mamanki bace kenan?”ah ah nidai banceba…hmmm zoki kamani natashi… mak’e kafad’a tayi had’e da cewa Ium um d’azun bashareni kayiba”kak’i sakani aikin komai… murmushi yyi Yana kallonta azuciyarsa yace gsky yarinyar nan ta cika wauta da kuruciya…afili sai yace ai laifi kikamun shiyasa nashareki nayi fushi dake ke Kuma Baki iya rarrashi ba,kokuwa Dan bakya jine Dani shiyasa…
Bata basa amsaba ta matso kusadashi ta kamasa ...wuf yafisgota tafad'a kansa...ya matseta akirjinsa Yana ajiyar zuciya"hannuwansa yasaka yarik'e Gam ganin tanson kwace kanta...sai mutsu mutsu take had'e da cewa Dan ALLAH kayi hakuri kacikani .....banza yyi Mata saima yafara kokarin sinsinar Mata wuya...wayyo ALLAH tuni tsikar jikinta ta tashi ,jikinta yasoma rawa saikuma tafara hawaye had'e da cewa wlh Zan maka ihu koka cikani...ajiyar zuciya yyi had'e Dora fuskarsa kan tata yace so what? inkinmun ihun ne..
Hmmm to naji sakeni”bazanfa cikakiba,atare zamu kwanama ,sbd nagaji da kwana Ni daya bacin inada iyali”yanzun Dan ALLAH ko tausayina bakyayi riyan?”
Ina tausayinka Mana”nifa ba wancan tausayin na rashin lafiya Nike nufiba….um ..um Dan ALLAH cikani zanshiga ba’yi… tafad’a tana zillo “irin abukace take da lalura”cikata yyi da sauri…
Tashi tayi sg jikinsa tayi Masa gwalo had’e da cewa dama ba wani bayin dazan shiga Dan ka cikanine…
Nidai ko riyan?”eh din me zakamun me?”hmmm haba yarinya saikace ba yanzun kike mun magiya na cikakiba,Ai insha ALLAH Zan tashi ko”nidake ne…cikin rashin gane manufarsa tace ohodai Ni na kwanta in mlm yashigo yataimaka maka ka kwanta.
Tayi saurin kwanciya tana addua.
K’uri da sexy eyes nasa ya Mata ,shifa yanzun komai tayi burgesa take “lumshe ido yyi Yana kissima abubawa dayawa game da riyan inya warke…
Washe gari suna zaune atsakar gd bayan sallar Zuhur sukaji sallamar ammi da Hafiz..
Cike da farin ciki riyan da Abdallah suka tarbesu…
Byn sun gaisa sunci abinci Abdallah ya ja Hafiz gefe harda kwallonsa yace pls abokina miye shawara wlh na lura yarinyar nan da gske take tanason murabu?”
Dariya Hafiz ya kece da ita”take Abdallah ya had’e rai.
Mlm inbazaka bani shawaraba toshiken….hmmm lallai AK ai wlh gara tagaraka son ranta in ALLAH ya taimakeka k’ila tasoka sbd kamarka da k’yar asamu wacce zatace Baka mataba”
Murmushi Abdallah yyi had’e da cewa ai badolene ba ka birge kowaba….
Hakane ,amma ai nason abokina taurarone”
Yau Ina pics d’in dakake yawan yima nida my riyan?”
Ashek’e Hafiz ya kallesa had’e da cewa bacin kagayamun mgn ai nagogesu ma…haba Mana pls kabani nagani….Wai kus kus dinme kuke hakane?”cewar ammi data fito sanyin alwallal la’asar…
Tab’e baki Riyan tayi had’e da kauda kanta “
Hafiz ya Yi murmushi yace ai kinsan tsakanin aboki da aboki sai ALLAH ko”
Buta ammi ta d’auka had’e da cewa kwaji dashi ,tashige bayi abinta…
Abdallah yasakarwa riyan wani killer smile daya kusa Tona asirin zuciyar ta”sbd smile din yatafi da ita ainun..
Bayan sun yi Sallah ,nanma Saida suka Dade suna fira ,kafin suyi sallama har kofar gd su Abdallah da riyan suka rakosu,bayan ammi ta kwantarwa da Abdallah hankali kan cewa tasanar akano gdn dasuka zauna in mamansa tazo akirata da number indata basu, sannan Abba ma suna bibiyarsa bbu matsala insha ALLAH…
Bayan sati2
Share
BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????
????AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????
Story & written by
mmn fareesa
Not edited❌
p40
Bayan sati2
“”Kinga yadda ALLAH yamaidoni arayuwar mijina ko?ga Kuma yarana kingani “duk bak’in cikin ki saiya kasheki”inaso kisani duk zakaran da ALLAH ya nufa da cara…ko ana muzuru ana shaho sai yyi!ummi ta fad’a tana kokarin shak’e wuyan mom …. dedenan ta farka a rud’e tayi sharkaf da gumi….wani uban ihu tasaki…Wanda yasa Alh Suraj (Suraj) yyi saurin tashi dg bacci. kasancewar Abba baya gdn ,shine yazo kamar yadda suka Saba..
Mitttsss yaja tsaki hade da cewa lfy Wai inajin dadin baccina Zaki wani tasheni da ihu?”jiki bbu lakka tasanar da shi mafarki da tayi had’e da cewa yanxun me hakan kenufi?”kaddai ace da gske HAJARA zata dawo ta fad’a hankali tashe”tabe baki yyi had’e da cewa may be ta dawon “dakuwa tawa ta sameni! Dole na koma gun boka sbd fa harda wannan mataccen ta nunamun a mafarkin” Hmmm lallai hassu waike ko tsoron ALLAH ma bakyayi”kinzo ki rusa gd kinata makirci da cin Amana gsky karsh….dallah dakata !aikin banza aikin wofi”aidole kace haka tunda ana yagomaka rabonka kana fantamawa ko?”duk wani cin amanar dawa na aikatashi badakaiba” butulu !zaka rik’a gayan mgn “to wlh ka kiyayeni…anki akiyayekin k’aramar y’ar iska k’aramar y’ar bariki,nizakiya akuyanci”indani aka ci Amana aibani na aza ki kan turbarba ganinki nayi akai nima gashi adalilinki har yanzun banyi aureba balle nayi Dan kaina”tir dake wlh “nayi nadamar saninki arayuwata’kinjani ga aikata halaka…Suraj nikake gayawa mgn haka? lallai Dan Adam bulune!
Eh angayamiki,ribar mi nasamu atarena dake inba faduwa ba”nabiye Miki Muna cikin Bata”inbaki sannuba ,yadda kikazo agyara to Zaki koma a alakoro…kutumar ubancan! cewar mom had’e da k’ok’arin shak’e wuyan Alh Suraj d’in”tana huci cikin tsananin b’acin rai….kaucewa yyi had’e da cewa haukan naki Zaki nunamun ko?”to Bari kiji dg yau bazaki sake ganin Suraj ba”sbd nagama dake zanje na yita istigifari ga ubangiji !ke kuwa nasan bazakiyi nadama ba sbd kinsaka shirka aranki “saidai Ina Miki albishir d’in cewa kina d’auke da cuta mai karya garkuwar jiki(H I V )dake da kawarki ikilima sbd inbaki saniba yau kisani “ikilima Ina nemanta sbd ita takamun kanta Kuma agunta nasami wànnan ciwon sakamakon kwana2 dasuka wuce Muna gdnta tare “tana toilet”aka kirata awaya na d’aga ,kafin nayi mgn “naji ance kawata kiyi hakuri kicigaba da Shan mgni Zaki rayu lfy bbu komai,sbd ita H I V indai kana shan magani to baza’a gane kana d’auke da itaba…iya nan naji nakashe wayar ,ko afuska ban nuna Mata nansaniba,saidai nasha alwashin Zan goga Miki kamar yadda aka gogamun sbd kece silar shigata bariki,Kinga kuwa dole mudauki cutar atare… sannan dg karshe kisani ikilima Bata kaunarki ko kad’an tana Miki iza me kantu ruwa ,Tasha fad’a mun cewa akullum tanajin zafin hinta dakikayi…
Daskarew a mom tayi tamkar gawa jitake tamkar amafarki”shin meke Shirin faruwane Dani?”ta fad’a afili batare da tasan ta fad’a d’inba…watan Dana saninkine yatsaya…wani uban ihu ta kurma tan cewa Zan nunamaka d’aya dg cikin kaidina”murmushi Suraj yyi had’e da cewa to shikenan inzaki iya,Koda hakan ta faru banajin komai sbd na boye number naturama Alh Kabir girma da cewa kinada HIV , sannan na sanar da abokina cewa inhar yaji kinmun wani sharrin to yatura Masa video d’in da namana nidake muna aikata Masha a Kinga zai yarda da gske ke annobace! Dukda nasan kinmasa asiri….
Kuka kawai tasaki had’e da fadawa kan bed”sbd rashin sanin me yakamata tayine,shin da gske zai iya tura. Vedio d’in,shin Wai hjy ikilima dama kinta take tuntuni???”””
K’arar rufe kofar ya maido tunanin ta”da sauri ta tashi tsaye had’e da ficewa…
Ihu take iya karfinta tana cewa kwarto jamaa kwarto jamaa!!!kutare kutare!!
Tuni ma’aikatan gdn suka Fara fitowa da masu gd…cikin ikon ALLAH suka Kama Alh Suraj dake niyar ficewa Gurin karfe 5:30 na asuba…
Saidai sunyi turus sbd ganin ai wannan yayantane sbd duk sadda zaizo har get take rakosa,takuma musu gargadin duk time d’in dayazo su barashi yashiga…
Hakan yasa suka tsaya had’e da cewa kobashine bane,ana hakan yyi wuf yafice dg gdn” ita Kuma alokacin ta iso Gurin..
Sbd tashin hankali tuni ta fad’i Gurin su mamma…