AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Abdallah da mlm na zaune atsakar gd suna fira…sukaji sallama…da gudu riyan ta fito Dan darban ummanta sbd tasan da zuwanta sunyi waya ajiya ta sanar da ita sunan k’auyen datazo ta tambayi gdn mlm HABIBU za’a kaita..
Wani mummunan faduwa gaban umma yyi alokacin da suka had’a ido da Abdallah dake murmushi Yana Mata sannu da zuwa!Bata tab’a ganinsaba sai yau ,dama sau d’ayane yaje yagaida ita shima Kuma Bata kallesaba”
Fuskarsa ta Mata Kama da KB(sunansa na kuruciya) mijin HAJARA yayarta data Bata…
Dakewa tayi had’e da boye mamakinta”ta gaida mlm da Inna mairo kafin Abdallah da riyan suka bita d’aki suka gaida ita…
Kok’arin fita Abdallah ya keyi “sauri riyan ta ce lahh Kinga umma Yaya Abdallah fita zaiyi Wai kunyarki yakeji… murmushi umma tayi gabanta na faduwa sbd ta tuna sunan Dan Yaya HAJARA Abdallah”
Hararar riyan umma tayi hade da cewa to yyi dakene ?
Juyowa Abdallah yyi da keken Yana murmushi yace rabu da ita umma bacin yanzun kindena Yi da ita saini… yafad’a Yana kashewa riyan ido…
Turo baki tayi had’e da cewa umma Wai da gske?”
Eh Mana “
Dariya yyi ta Mata,itakuwa tana hararan sa”
Sosai umma ta jajanta Masa had’e cewa Dan ALLAH ko kanada photo na mahaifinka nagani sbd inason sanin gano wani Abu?”
Da mamaki abdallah yace ah ah wlh sbd manyan wayoyina matar Abba ta k’wacesu… k’aramar ce kawai hannun riyan”Amma Zan iya zanamaki tunda hannuna na aiki…
Umma tace ah ah abarshi kawai…ah ah umm tunda zai iya bbu komai fa cewar riyan..
Haka kuwa akayi cikin kankanin lokaci mlm yasaka aka samo pencil da colours Abdallah cikin kwarewa yasoma zana alhj Kabir girma….
*********
Zazzaune suke har da ummi suna cin abincin Rana”cikin son tsokana Alhasan Yadubi hussy yace kije ki gyaramun d’akina kihadamun ruwan wanka… murmushi tayi had’e da kallonsa ashek’e yace to Yaya angama!
Itadai ummi najinsu batace komaiba!
Ummi Wai kece kikayi girkin nan kuwa?”
Itace Mana!cewar hussy dason jin mezaice!
Haba no wonder shiyasa yyi mugun dad’i…..hhhhhhhhh???????? dallah mlm bi ahankali kada ka k’ware Gurin yin Santi” to ninayisa ba wata ummi…
Yamutsa fuska yyi had’e da cewa hmmm to ai nima Wasa nake Dan naji Mai zakice ai!
Hmmm kajidashi ai ,sarkin gulma”kadai Fadi gsky kaji.
Naji ta Mohd bada kanki asare… had’e rai tayi had’e da cewa wlh ya isheka”
Haba my sweet hussy!Kinga kawai ayi Yar gida da friend d’ina farouq kawai”ummi kingani ko?
Tsaki ummi tayi had’e da cewa kunfi kusa ai…
Aje spoon d’in hannunsa yyi had’e da cewa muje mugyara d’akin kinji antyna yafad’a cikn marairai cewa…
Murmushi hussy tayi sbd tasan badan ALLAH yaceba”tashi tayi tabisa tana cewa hmmm su oh oh d agdn masu kud’i ka fito dakayi mulki da son jiki son ranka wlh, komai sai namaka, to inda babbuni ummi kasan bazayi makaba ko?
Yatsina fuska yyi hade da cewa Kinga inbazaki gyaramunba kirabu Dani ,kintasani agaba kinamun surutai…
Eh naje nayi ,kayi maganin abun manah”ance kayi aure amma kaki Yi,in kanada Mata saika juyata yadda kakeso…
Finciko hannunta yyi had’e da cewa me kike fade?”
Haba my sweet broth!Yaya Alhasan !muje nagyara maka d’akin.
Murmushi yyi mai sauti….
Abba ne zaune a office nasa.
Wayarsa tayi k’ara alamar shigowar sako!
Dubawa yyi saiyaga ansaka kamar haka…..
Kun rage comments ba kamar daba, kodan kunga kullum kuna samun 2 pages to dg yanzun 1 zaku samu”
Banason tanx ko steakers comments kawai….
Share
BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????
???? AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????
Story & written by
mmn fareesa
Dedicate to all my fans????????????
Not edited
P 41
Ak’agare yace miye shawarar?”
Ajiyar zuciya ammi tayi had’e da mik’e wa tsaye tana safa da marwa… cike da tausayawa tace na farko dole Abdallah yyi mutuwar wucin gadi sbd shi yak’i Dan yaudarane,inbaka iya Kama b’arawoba saishi yakama ka”
Ma’ana zanyiwa Abdallah allurar da zatayi 24 hours ajikinsa tana aiki “tun dg yau zuwa gobe kamar yanxun , sannan ta sakesa kafi….Amma ammi ta yaya kenan bacin kinsan sotake taga bbushi aduniya..jirani Mana Hafiz”cewar ammin.
Ai yanzun zanmasa allurar zaiyi kusan 30 or 35 minit kafin tafara aiki ajikinsa”
Na biyu…shine byn yanxun kamaidasa gd “zamuje Gurin liman me tsaran makabartar dake k’arshen g r a,nida kai muyi Masa bayani in ankai Abdallah anbinnesa zaka koma ku hak’osa kaidashi”sai dare yyi kaje ka daukosa ka maidosa nan gdn”na ukku shine in anyi sadakar 7 Zan canza Kama na nuna nice yayar mahaifiyar riyan naje na cewa hjy hafsat Zan tafi da ita gd tayi ta kaba,nasan zataso hakan”dana tafo da ita nan sai kawai ,mujabgoransu nidakai zuwa k’auyen karaye gdn baffanka MLM HABIBU(masanin kur’ani mai girma,Yana karya sihiri yayan mahaifin Hafiz ne) nasan insha ALLAH Abdallah komai Daren dad’ewa zai warke sbd da alama sammu aka Masa “kaga dg nan inya warke sai ya fito ya yak’i hjy hafsat,Amma tunkararta yanxun gsky bashine mafitaba sbd shikanshi mahaifinsa tagama dashi….na hudu shine duk jawabin nan kusanar da matarsa (riyan) sbd gobe in ALLAH ya kaimu zatafito tana kururuwa byn sallar asuba ta nufi part d’in hjy hafsat tasanar da ita Abdallah baya numfashi ko motsi…munsan dama burunta kenan ,Kuma baza a bincika ba sbd tagama da Abbansa,inkuma riyan ta ji ana cewa za’a bincika aga ya mutu ko kuwa to tayi hanzarin kiranka !kaikuma ka kirani…..
Ajiyar zuciya Hafiz yyi had’e da kallon Abdallah cike da tausayawa abd ganin za’a sa yyi mutuwar wucin gadi…
Ahankali yace AK kaji duk jawabin ammi ko?”
“D’aga Kai yyi “alamar eh.
Hafiz yace ka amince da shawarar ta?”
Abdallah ya d’aga Kai hawaye masu zafi na zubar Masa akumatu…ba tausayin kansa yasa Kashi kukaba,ah ah tausayin mahaifiyar sa da aka rabashi da ita tsawon wasu shekaru… lallai ya tafka kuskure “Yana zaune duk baisan hakan ba..wata zuciyar tace K’ADDARA ce tayi sanadin hakan..
Muryar Hafiz ce ta katse Masa tunani gun cewa to ammi kusanar damu wacece HASSU TSIYA TSABA?”
Ammi ta ce Zan sanar da ku,Amma lokaci ya kure yanxun Hafiz ,muyi abinda ke gaban mu..
Hafiz yace to shikenan….
Kamar yadda ammi tace haka akayi tayiwa Abdallah allurar(bazan fad’i sunantaba sbd kada anema acutar da wani)
Sannan Hafiz da body guards nasa suka maidasa gd gab da magrib , Hafiz be bar gdn ba Saida yyiwa riyan bayanin komai gameda shawarar da ammi ta basu,yakuma sanar da ita tayi taka tsan tsan Dan kubutar da rayuwar Abdallah ,sbd yau da isha’i mom zatazo ta kawowa Abdallah frash milk,kada ta yarda yasha..
Bayan Hafiz ya koma gd sunyi magrib da isha’i,yaja ammi amotarsa ,sukaje gun liman me tsaran makabartar,suka Masa bayanin komai sbd sun San insunkoma basu sanar masaba ,da matsala za’a zargesu ne…da farko liman ya nuna be yardaba ,Amma dasuka Masa bayani sosai suka nuna Masa photo na Abdallah sai ya amince ,yyi musu fatan samun nassara.
Bangaren su riyan kuwa.
Suna cikin tashin hankali da faduwar gaba har akayi magrib zuwa isha’i.
Zaune riyan take kan kujera, yyinda Abdallah ke kan kekensa zaune jigum Yana jiran zuwan mom.. had’e da tunanin Wai shine gobe zaa binne da ransa….oh shin mi wasu suka dauki duniyane Wai?”
Sallamar mom ta kashe Masa. Tunani… Wani mugun faduwa gaban su yyi shida riyan.
“Cikin ambaton ALLAH riyan ta amsa”tana kallon frash milk din dake hannun mom cikeda cup…..