AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Story & written
By mmn fareesa

Wannan shafin nakune halak malak
Bilkisu Auwal
Fatimatou
Queen
Kuyi yadda kukeso dashi comments naku yafi nakowa yimun ????????❤

K’oRAFI…wasu dg cikin ku suna mun korafin Wai banfadi waye Abdallah ba da Kuma wacece riyanatu ba,musammun mmn shukra novel kunfi K’oRAFI. To kusani gsky banison gajan hakuri kubi komai ahankali zakuji ,dukafa pages3 akayi Amma anfaramun K’oRAFI,duk wadda taji bazata iyaba so pls tadena bina…

P4

”'”””washe gari misalin karfe 8:30 am Abdallah yafito cikin bacin rai da damuwa a fuskarsa”straight parlourn mom yanufa yasameta ita da masu aiki a dining area suna shirya breakfast .
Koda ta lura da yanayinsa,tuni ta sallami masu aikin .byn sunfita yazo yazauna kusa da ita had’e da aza kansa agefen kafad’arta,cikin shagwaba yace good morning my mom! Murmushi tayi had’e da shafa kansa tace morning my son,yahbak’unta?” Turo baki yyi tamkar yaro yace gsky mom bazan iya Zama cikin dattiba,kwata kwata masu Miki aiki basu iyaba nifa nafison ko Ina nagansa need…. girgiza Kai tayi had’e da cewa pls my son kayi hakuri Zan sake Kiran harira ta sake bincikamun wacce zata ruk’a kularmun dakai,amma yanxun muje nahada maka ruwan wanka ,kafin ka fito nagyara inda kakeso kaji abdallan momy ta fad’a cikin rarrashi…
Murmushi yyi yace yauwa kokefa mom ,to Amma gaskiya me tsabta zaa samu ko Kuma marar surutu . sannan gsky momy intazo kiyi warning nata akaina danbanson shishgi…. fuska bbu walwala tace Wai yaushe zaka Dena wannan miskilancin nakane?”damafa jiya da zeenat tazo gunka haka tadawomun da kuka Wai ka shareta kunyi tafiyarku kaida wannan yaron mittsss taja tsaki hade da cewa ni wlh narasa wacce jaraba ce wannan kudai ba gari daya kukeba aiki yakawosa anan iyayensa na kano,dg kunyi skul tare yazo yawani manne maka ,kilama shike turaka ka wulakanta zeenat…
Kallon mom yyi”ahankali yace kiyi hkri mom Hafiz bashida wani aibu ko wani mugun hali sai kyawawan halaye, sannan zeenat banmata komaiba, lokacin sallah yyi dalilin dayasa muka fice kenan,dg karshe mom zeenat batada tarbiyya da kamun Kai na ya’yan kwarai…
Ya isa haka kayi hakuri zata canza kasan dai uwarta kawatace ko?”to banison jin komai muje kayi wankan.
Bbu musu yabita har part nasa.
Mom batabar part d’in ba. saida komai yyi yadda Abdallah keso tukum ta fito da niyar aiko Masa breakfast dinsa.,,,,,

  Bangarensu riyanatu kuwa ,cikin yadda ALLAH suka tashi da safe suka kimtsa hade da Karin kumallo , sannan umma ta Fara aikinta yyinda riyanatu ketayata.
Azaman dasukayi da zuwaira dg jiya zuwa yau sun gane mace ce ita mai kirki dason jamaa,sbd duk wani Abu dazasuyi kauyanci akai ,zatayi saurin gyara musu shi cikin aminci  bbu tsangwama.

Abbane ketsaye gaban dressing mirro Yana fesa turaruka,yanata sauri da alama fitama zaiyi… Abdallah yyi sallama yashigo Yana murmushi had’e da kallon Abban nasa Yana gaisheshi,hade da cewa Abba office zakajene kk sauri?”
Juyowa yyi Yana dariya yace ah ah my son!wlh tafiyace ta kamamu harta tsawon 2 weeks Kuma tare da president zamuyita zuwa indiya dg nan mudawo Abuja muyi wani meeting tukum nadawo ,nima da safen nan byn nadawo dg masjid sakon tafiyar ya isomun jirgin karfe,9:am zamu hau…
Fuska bbu walwala yace Abba gsky nidai banison katafi dudu yaub kwana na nawa a Nigeria?”murmushi Abba yyi hade da cewa sorry kaji my son nima naso mu zauna sbd inason to bude sabon kamfaninka kafara aiki ,karika fita office Amma insha ALLAH innadawo munyi mgnar..
Yafad’a had’e da daukar wata jaka, yyinda Abdallah yakarba da nufin Masa rakkiya.
A parking lot ne yakedubarsa ganin bbu momi amasu rakkiyar ,yace Wai Ina mom bazata maka rakkiyaba??”
Murmushi Abba yyi hade da cewa ah ah munyi bankwana ai da ita”Abdallah bece komaiba yyishiru har guards d’in Abba suka bude Masa gdn baya yashiga ,nan yarika dagawa Abba hannu had’e da Masa adduar sauka lfy..

    #####

Haka rayuwarsu umma da riyanatu ta kas canance agdn zuwaira mai abinci bbu kyara balle tsangwama har tsawon kwanaki 8
Ayaune Kuma suke jiranxuwan Fatima y’ar zuwaira dg skul kasancewar yau ake hutu ….

Zazzaune suke atsakar gd bacin sun gama aikin safe ,zuwaira nata yanka salad na abinci .wata dattijuwar mace tayi sallama , zuwaira ta amsa fuska sake tana cewa ah ah lallai harira b’atan Kai kikayi agidan nan?”
Murmushi harira ta yi tace hmmm ah ah wlh naxo mu gaisa ne andad’e baahad’uba …

Nan suka gaisa da zuwaira, sannan umma tace Ina kwana?”

Harira ta amsa , had’e da cewa Masha ALLAH zuwaira Baki kikayine agdn?”

Zuwaira tace eh Yar uwatace wannan yartace,banan suke ba ,Amma sundawo da zama agarin nan.,,

Harira ta ce Masha ALLAH”

Byn taci abinci sukayi sallama ta fice..

Harira batafi minti12 da fitaba saiga Fatima da masu daukar Mata kaya sunyi sallama.

Da gudu tajeta rungume mamanta ,tana ihun murna, dariya zuwaira tayi tace to auta sakeni karki kadani ga Baki nan munyi Kuma goggonki ki gaishe d ita…

Juyowa tayi lahh Ina kwana ?” Waccan kyakykyawarfa mama?”ta fad’a tana nuna riyanatu dake kallon ta.

Murmushi zuwaira tayi tace y’ar uwarkice Kuma kawarki….ihun murna tayi had’e da zurawa aguje t rungume riyanatu sbd Fatima akwai son jamaa.

Ita riyanatu cikin murna ta tarbeta,kafin kace me,harsun shaku da juna,komai tare suke har aka kwana aka wuni ,tuni Fatima ta Fara kokarin wayar da riyanatu da koya Mata kwalliya duk da bbu abin kwalliyar Dan kayanta basufi kala7 ba ,suma kuma duk sunji jiki,hakan yasa Fatima tabata nata kala4 Kuma sabbi , sannan da kayan kwalliyar ta suke amfani…
Hmmmm acikin kwanakin duk Wanda yasan riyanatu a kauye to yaganta yanxun bazai ganetaba,sbd yadda ta canxa.
Dama gata da muguwar tsabta ,saidai matsalarta guda batason saka gyale saidai hijab.

Lokacin da Fatima ta koma islamiyya duk tadamu sbd ita agd ake barinta Kuma zaman gundurarta yake,Koda umma ta lura rarrashinta tayi had’e da cewa in wata yyi zata sakata Amma bacin wannan aikatau dole su nemi wani abun suyi.sbd sai wata yyi abasu kuma kafin zaka zasu iya bukatar wani Abu gakuma skul da akeson mayarda riyanatu,danma zuwaira na kokari akansu to Amma yau d gobe sai Allah.


Mom ce zaune kan kujera ta aza k’afa daya kan daya ,ga lemun kwali gabanta kan center table tana kurba ,tana yatsina, yyinda tayi wani murmushi had’e da kallon matar dake zaune gefen kafafunta kan carpet tace to harira kinji dai dalilin. Kiranki Dan ALLAH kisamo mai tsabta, wacce zata kularmun da yaro Amma ba mai surutuba Kuma banison babba ,nabaki nan da kwana 2 Dan ALLAH kikamun ita muyi mgn nasanar da ita aikinta ,Amma banison mai yawan mgn da surutu gsky sbd my son bayason yawan mgn , sannan Kuma kikawo marar wayo sbd kinsan banison sa ido gsky…inhar kikayi yadda nikeso kinada kaso mai tsoka kema.

Ajiyar zuciya harira ta yi hade da cewa to ranki yadad’e insha ALLAH zaasamu Dede yadda kikeso.zan bincika dg yau zuwa gobe insha ALLAH.

Kafin mom tayi mgn Abdallah yashigo parlourn da sallama, sanye yake da suit farare ,yyi masifar kyau ,yyinda sallayar dake tsakkiyar goshinsa takara fitowa da Masa kyau ga sajensa yasha gyara sai kamshi take tashi ajikinsa tunkan ya ida isowa kamshinsa ya bayyana. kamar kulum fuska atamke yazauna Yana gaida mom had’e da cewa harira Ina yini?”

Baki washe ta amsa tana Masa kirari,yatsina fuska yyi yamike tsaye da nufin barin parlourn, adedenan zeenat tayi sallama sukayi 4 eyes da Abdallah tabe baki yyi hade da kauda Kai yyi haryar dazata sadasa da part nasa….

Mom ta yi saurin dakatardashi gurincewa haba my son !bak’uwa fa kayi zaka tafi kuma”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button