AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Zama tayi fuska asake ,ta amsa gaisuwar riyan,kafin tace yamai jikin?
Riyan tace gashinan da sauk’i…
To madallah”ga frash milk sabon yayi,abashi Dan tafi waccan dakuke bashi,ta fad’a had’e da cewa to gata abashi mugani kota Masa dad’i…
Karb’a Riyan tayi hannu na kirma..
Mom ta matsa ta shafi kan Abdallah had’e da cewa sannu my son kaji”ALLAH ya tashi kafad’ar ka “dakai nake kwana nake tashi azuciyata sbd tausayin ka Abdallah kana cikin wannan hali,bbu jiii bbu mgn Amma aikomai yakusa zuwa karshe tunda za’a fita dakai waje… fad’a had’e da kukan munafurci Wanda bbu hawaye.
Azuciyar riyan tace shaid’aniya kenan,afili kuwa sai taita rarrashinta gun cewa kiyi hakuri mom ki yarda da k’addara insha ALLAH zai Sami sauk’i.
ALLAH yasa riyan “
Ameen mom”maza ki basa mugani kozai shnye ne…
Daukar cup d’in riyan tayi tana latsa wayar Abdallah dake hannunta had’e da kokarin Zama kusada keken Abdallah Dan tabasa…
Bata kaiga zamaba aka d’auke nefa ta gdn Baki daya…
Mittsss mom taja tsaki hade da cewa Kai Yan nefa bbu tabbas Yanzun ai ya’u direba zai tada Jan…
Kafin riyan tayi mgn haske ya gauraye parlourn…
Murmushn samun nassara mom tayi had’e da cewa yauwa anmaido”maza kibasa yasha aje akaisa ya kwanta…
Kallon mom kawai Abdallah keyi,jiyake kamar yashaketa sbd tsanarta,sai yau ya yadda da ake cewa wasu dg cikin Mata shaid’anu ne,Kuma dangin shaid’an…Ashe duk abin nan da mom ke Masa ba Dan ALLAH bane…cup d’in da riyan ta Kai bakinsa yadawo dashi tunaninsa….
K’uri da ido mom tayi tana dubarsu har Abdallah yashanye tas , riyan ta dubi mom had’e da cewa Kinga kuwa ya shanye duka bara na Kai cup din kicin natafo Masa da fura ya k’ara….
Ajiyar zuciya mom tayi aboye, yyinda fuskar ta fal da farin ciki tace to shikenan jeki dawo nima na wuce,namaji Alh shiru baidawoba bare yazo yaduba my son…riyan ta fice dg parlourn da cup a hannunta….
Tana fita mom ta kece da dariya had’e da cewa banzaye ,wawaye daku kaida ita… lallai Abdallah dg yau kagama numfashi… matsiyaci na tsaneka bana kaunarka kokadan ,ko rungumeni kayi ,jinake tamkar na shakeka,naso ace ka auri zeenat nasakata ta kashemun kai….
Duk abinda take cewa Abdallah najinta Amma be dagoba balle ya nuna alamar yaji,yyidai shiru…akuma dedenan Abba yyi sallama yashigo cikin parlourn.
Amsawa mom tayi , had’e da maida fuska kalar tausayi,tace Alh yakamata fa amaida Abdallah hospital kafin zuwan ranan da za’a fiddasa waje….
Zama Abba yyi hade da cewa,eh wlh nima naso hakan Amma k’ila amaidasa gobe….kafin tayi mgn riyan ta shigo.
Nan suka gaisa da Abba,kafin yakoma Gurin Abdallah Yana shafa kan sa, Yana Masa fatan samun lfy…dg bisani sukayi sallama ,atare da mom suka fice.
Byn sun fita ne…. Saiga ammi ta fito dg bayan kujerar da riyan ke zaune tana ajiyar zuciya. ..riyan tayi ajiyar zuciya tace hankalina fa yatashi danayita ma yaya Hafiz flashing,amma anki adauke nefa…sai yanzun Dana kirasa akicin yacemun ai akan idonsa mom ta shigo parlourn nan..
Ahankali ammi tace nikaina wlh ,hankalina be kwantaba Saida aka d’auke nefa na canza Miki frash milk d’in na karb’i me maganin.
.gata maza kije kiyi floshing nata ,nibara natafi gd zanbi ta inda Hafiz ya shigo Dani,yanacan Yana jirana.ALLAH yashige Mana gaba ,ki kula sosai kiyi yadda komai zai tafi daidai…
Insha ALLAH ammi ,riyan ta fada had’e da nufar bed room d’in ta.
Ammi ta kalli Abdallah dake sauronsu Yana kallonta da ido yanason yin mgn sai bakinsa ke motsi.
Murmushi tayi had’e da babu godiya tsakaninnu kaji Abdallah dakai da Hafiz duk d’aya me aguna,ta fada sbd talura abinda yakeson fad’a Ken.
Saida riyan ta dawo , sannan ammi ta fita….
Washe gari…….
Share
BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????
????AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????
Story & written by
mmn fareesa
Kuyi hakuri my fans dajina shiru Ina da uzurirrikane???????? sannan Ina godiya ga wadanda suka kirani da Kuma masu turo sakuna” nagode sosai d kulawarku… sannan duk week end gsky bazaku samuba????
Not edited❌
p 41
……Matarka!hjy hafsat tana d’auke da cuta mai karya garkuwar jiki H I V….nine Kuma na lik’amata ita”
In kana kokwanto zanturo maka video d’in da nike kusantarta! Kana sone?”sannan nasan tamaka asiri tana juyaka bacin ta rabaka da iyalanka…kada kasake ka kusanceta Koda ta bukaci hakan “sannan inta maka kwarjini ka ambaci sunan ALLAH insha ALLAH zakaji tsoron yarage “
Niii..na tuba yanzun ,inhar kana bukatar jin sirrin Matarka ka turo sako ta wannan number 09087671240….. Ka Kuma goge sakon sbd zata iya dubawa….iya nan Alh kabir girma yakaranta” zuface keta keto Masa dukda acikin AC yake d fanka” yyinda zuciyarsa ke tambayar sa cewa ta rabaka da iyalanka? To suwaye kenan…wani faduwar gaba yaji had’e da mugun sarawa kansa yyi “da k’arfi yyita ambaton sunayen ALLAH…ji yyi zaman office d’in ya ishesa,hakan yasa yatafi gd “zuciyar sa nason tuna Masa yau kimanin wata 3 kenan rabonda yakusanci mom tun kafin marigayi Abdallah yarasu..lolx..yakuma aiyana aransa Dole yaga video d’in, sannan bazai yarda wani Abu yashiga tsakanin suba “Kuma Wai da aurenta take aikata Masha’a ,inda gske ne to tun yaushe ta Fara aikata hakan?”
Koda ya iso gd "har part nata yaje Amma bbu ita bbu alamarta"yakira wayarta akashe"to Ina ta tafi?yatambayi kansa dukda Bata tambayar sa zuwa anguwa...wasu hawaye ne masu zafi suka zubo Masa sbd tuna Abdallah da yyi"ahankali yace ALLAH ya jikanka da rahama...gaba d'aya sai yaji yatsani rayuwarma gaba d'aya...
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU’UN!shine abinda umma ke maimaitawa had’e da nuna photon Abba da hannu tana hawaye had’e da cewa shine!shine!!shine!!!wlh shine mijin yayata HAJARA data Bata shekara 25 kenan…cikin zaro ido had’e da mamaki riyan da Abdallah keyiwa umma kallon tambaya…da sauri ta d’aga Kai had’e da nuna Abdallah tace Ni jininka ce Riyan k’anwarkace! shin ya akayi hakan yafaru ?”tafad’a cikin kuka da shashsheka”dama hassu itace kishiyarta?”ni dama bansantaba alokacin da akace mahaifinka zai k’ara aure sbd alokacin ko aure baa munba”Kuma bayan AUREN abbanka da wata2 mukaje kano gun mahaifiyar ka kace sun tashi…
Cikin mamaki had’e da al’ajabi Abdallah yace umma ke k’anwar mahaifiyatace?”
Tace k’warai da gske “sbd ga sheida nan,na photon mahaifinka da Kuma yadda Naga kuna yanayi da Yaya HAJARA”sbd Kai jinintane,gashi sunanka Abdallah ,hakan ne sunan d’an data Haifa…umma na yarda !Ashe dama ko Yaya zanga jinin mahaifiya ta kafin nabar duniya ?
Yafad'a Yana hawaye"kafin yad'aga hannunsa sama Yana wa ALLAH godiya"
Mlm yyi gyaran murya had'e da cewa Masha ALLAH Alhmdllh lallai kunga rayuwa"ubangiji yabaiyanata aduk inda take yasa tana raye....da ameen suka amsa kafin mlm yafita Dan basu guri...
Riyan kuwa tamkar gunki tayi sbd ganin abun tamkar almara!Wai Abdallah jinintane?”
Yayanta ne! Shiyasa haba take yawan jin tausayinsa dakuma kin mom tunda tagane ba itace mahaifiyar sa ba”sannan inya Mata wulakancin batajin zafinsa ,ga yawan damuwa dashi datayi ,Ashe D’an uwantane… lallai ikon ALLAH beda k’arshe… d’ago kanta tayi ta kallesa saitaga yyi saurin janye idanunsa dg nata…
Shikuwa Abdallah kunyace fal da Dana sani aransa! lallai yaga rayuwa”tabbas Hafiz ya Sha fad’a Masa yadena wulakanta mutum bakasan meyimaka ranaba ,gashi Riyan ta Masa Rana dg k’arshe Kuma Ashe ita d’in jinin sa ce”yayantane”lallai Hafiz bazai tab’a mantawa dashiba”sai yanzun yagano dalilin dayasa mom Bata kaunar Hafiz”
Wato Dan taga Yana fad’a Masa gsky “tabbas bazai manta da AUREN WATA SHIDDA ba !gashi sanadinsa yasan abubuwa da yawa”wad’an da ko a mafarki bai sansuba”inama ace ana maido baya”yadawo da rayuwarsa ta baya “ya gyara kuskuransa…
Sai yanzun ya tuna da tunatarwar malaminsa na addini(a ingila) dayake cewa kuguji k’in Abu”Amma kunemi zabi agun ALLAH”ma’ana in wani Abu yashige maka to Rok’i ubangiji yazaba abinda yafi alkhairi…sbd da yawa abinda kuke k’i,sai yazama alkhairi agareku”abinda kukeso yazama sharri agareku!to gashi yak’i AUREN WATA SHIDDA Ashe shine sanadin warwarewar matsalar sa,fatanshi ALLAH ya bashi lfy yagyara abinda yabata agurin Riyan d’in shi …wani murmushi yasaki daya tuna irin farin cikin da Hafiz da ammi zasuyi….Amma Wai duk ta Yaya hakan tafarune ?ya akayi kukazo nan Kuma ita hassun tasan Kuna nan??”