AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

D’ago kanta RIYAN tayi ta shiga warwarewa umma komai”sbd abaya akwai abinda ta boye Mata,saidai ko yanzun Bata Fadi aurensu na WATA SHIDDA bane…
Saida umma tasake yin wasu koke koken, sbd tausayin su Abdallah”takuma yarda Abu na farko shine subar komai sai Abdallah ya ida samun lfy tukum..
Ahankali umma tace Zan sanar da ku wacece HAJARA da yadda akayi ta auri Abbanka da halin da muka shiga alokacin da muka gane ta Bata!konace ,abbanka yasiyarda ita ya gudu kamar yadda muke cewa a k’auye…
#######
Zaune take gaban bokanta”fuska bbu walwala “kallo d’aya zaka Mata kasan tana cikin damuwa”
Cikin muguwar muryarsa irinta dodanni yace “Al”amarinki yazo Kashi 2 na farko nassara…tuni tasaki ajiyar zuciya…na biyu akasinta,sbd zanbaki mgn kiyi matsi dashi in har mijinki yakusanceki to kingama mallakarsa har abada bayin maganar kowa sai Taki… Kuma kinsan zai d’auki cutar dake jikinki”sannan akasin haka shine yaki kusantarki, sannan duk ranar da yyi tozali da jinin matarsa to zai tunata ! ma’ana yaga yayan matarsa ko k’aninta ko kanwarta….cikin katse hanzari mom tace insha ALLAH ma bazai gansu ba….keeeeeeeee!rufe Mana Baki anan,kibar Kiran sunan ALLAH sbd inda dashi aranki bazaki zo nanba! yafad’a cikin wata mahaukaciyar tsawa had’e da k’yalkyalewa da dariyar mugunta irinta bosawa….
Shiru tayi ,sai zare ido take,kafin boka yabata izinin tafiya.
Koda ta shiga mota,kasancewar ita takawo kanta,Koda tafito dg dajin ,gdn hjy ikilima ta nufa ,sbd ta Mata wankin barko,ta tona Mata asiri…
Gaban get d’in gdn ta yi parking Bata shigaba”
Babu ko sallama ta banka Kai acikin parlourn gdn…
Hjy ikilima na zaune gefen mijinta Alh tanimu, yyinda zeenat ke zaune kan carpet tana chat…
Wani faduwar gaba hjy ikilima taji ganin mom tamkar anjehota”cikin rawar jiki tace hjy hafsat kece da Rana haka dg Ina kike?”dg gdn uwarki!mom ta fad’a cikin b’acin rai da masifa”kafin ta cigaba da cewa munafuka, makira matsiyaciya, maciyiya amana “to ALLAH ya Toni asirinki,Ashe kina da cutar me karya garkuwar jiki?”keeeeeee!dabbar inace ko kin Fara shaye shaye be??Zaki shigo kina Mana haushi acikin gd tamkar karya…cewar hjy ikilima azafafe…
Tashi tsaye Alh tanimu yyi da ma shi har ga ALLAH yagaji da Zama da hjy ikilima dukda Yana tsoronta ,Amma takaisa karshe Bata basa hakkinsa na aure kimanin wata 4 kenan ,zaman dasuke ayanzun so yake yamata zancen Amma Yana shakkarta…jin wannan maganar ta mom ta fidda Masa tsoronta…
Fuska daure yace keeeeeee hjy hafsat kisanar dani gsky!
Wani faduwar gaba hjy ikilima taji had’e da dubarsa tace Ina ruwanka ne,fita dallah kabamu wuri…Bata rufe bakintaba taji saukar wani gigitaccan Mari akuncinta…
Hahahahahahahahahahahahahahahahahahahaha???????????? mom tasaki had’e da cewa tabbas asiri ya karye “to Zan sanar da Kai tabbas tana d’auke da cuta mai karya garkuwar jiki wato H I V, sannan inaso kasani waccen y’ar ta nuna zeenat ba y’arka bace shegiya ce,tayo cikinta awaje ta manna maka…zaro ido yyi had’e da fibncikar hjy ikilima cikin tsawa yace da gske take?ita kuwa tsabar mamaki yarufe Mata Baki takasa mgn sbd batayi zaton haka dg mom d’in ba” ga kuma ihun da zeenat keyi sbd jin ita shegiya ce…
Murmushi mom tayi had’e da kallon hjy ikilima wacce Alh tanimu yyiwa muguwar Shaka tace k’arshen maciynin Amana kenan,kafin ta dubi Alh tanimu tace saika binciki kanka kaji kanada cutar,saika d’auki mataki ,tunda Kai doctor ne…
Bata bi ta kansuba ta fito,dg parlourn tashige mota da niyar yau Kota tsiya Kota arziki sai Abba yakusanceta…
Shikuwa Alh tanimu ,dg hjy ikilima har zeenat d’in jansu yyi yarufe adaki, sannan yatafi asibiti..
Bedawoba Saida yatabbatar anmasa gwaji…cikin ikon ALLAH bashida cutar..
Kaitsaye d’akin dasuke yashige ,yarufe,yyiwa hjy ikilima d zeenat d’in mugun duka na fitar hankali ,ko tashi basu iyawa ,da kansa yajasu kamar kayan wanki yafito da su waje,yace suyi gaggawar banmasa gd ,Kuma cutarsa dasukayi ALLAH ya isa yagode ALLAH da zeenat ba y’arsa bace,ko tsinke basu d’auka ba agdn ,dg su sai kayan jikinsu,sukja jiki sukabar anguwar gab da magrib,bbu halin shiga makota sbd hjy ikilima Bata hud’da dasu sai d’aga Kai take musu….
Gyaran murya umma tayi had’e da cewa…..
Share
BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????
????AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????
Story & written by
mmn fareesa
Not edited❌
p 42
Mlm jamilu shine mahaifinmu,asalinsu shida mahaifiyar mu halimaYan agadas ne dg can ne,sukazo k’auyen wazo k’ayawa”suka yada zango.
Alokacin anhaifi Yaya HAJARA,byn haihuwarta aka naifi IRO saini Fatima ana min lak’ani da BINTU..muntashi cikin tarbiyya da kaunar junanmu had’e da hadin Kai”mun Sami ilimin addini sosai agun mahaifinmu….kasan cewarsa malami masanin addini”
Bayn YAYA HAJARA takai shekara 12″kwasam mlm yyi bak’i dg birni,wato kakanka da mahaifinka anan Alh Kabir girma da akewa lak’ani da KB (sunansa na kuruciya)yaga HAJARA yaga ta Masa,anan maifinmu yabashi ita aka d’aura musu aure yabaro kauyenmu da ita ,suka tafi garinsu wato KANO…anan mahaifiyar KB dataga HAJARA tace Sam tayi k’ranta da aure ,abarta gurinta ko shekara 3 tayi alokacin 15 years gareta saisu tare…
Wannan dalilin yasaka aka sanya HAJARA primary 4 bayan tayi JSCE suka tare agdnsu ita da mijinta acikin so da kaunar juna..
Alokacin da naji tayi boko sai naji inama Ni, sannan nida IRO Muna kamata ziyara Ni har sati1 Ina Mata har ALLAH yasa tahaifeka"
Bayan haihuwarka ne mahaifin mu yaraasu” munshiga tashin hankali matuk’a,nan ababnka da mahaifinsa Alh Abdul fata suka dawo taimaka Mana sosai”yyinda Kanata girma da wayo har kayi shekara 4 alokacin Kuma mahaifinka yabijiro da maganar k’ara aure,Wanda HAJARA ta tashi hankalinta,Saida mahaifiyar mu ta Mata nasiha sosai , yyinda kakanka Alh Abdul fata yak’i amincewa da auren sbd aganinsa ,bega abinda HAJARA taragi KB dashiba”yyinda abbanka yakafe kan sai yyi auren…badan yasoba yabarsa,bakufi sati 3 da aurenba Alh Abdul fata yarasu…akuma lokacin HAJARA nada shigar karamin ciki ajikinta”
Kwatsam bayna rasuwar kakanka ,munje kano gdn Yaya HAJARA Babu kowa Mai gd yace Mana suntashi ai…mukaje gdn marigayi kakanka sai akace Mana ai kakarka Bata k’asar anfita da ita waje sbd Bata lfy tun bayan rasuwar mijintakuma dg can intadawo Nigeria to zasu wuce Mai duguri Gurin danginta, sbd su Yan can ne aiki yakasu kano,anan muka tambayi Ina su HAJARA da mijinta akace anmasa transfer Gurin aiki amma basusan ko wane gari sukeba…
Cikin tashin hankali da damuwa muka koma gd,muka sanar da mahaifiyar mu,itama ta damu kwarai “tun Muna saka ran jin wani Abu game da su harmuka fidda rai….
Shekarar Yaya HAJARA 5 da Bata akamun AURE,bayan na haifi Riyan mahaifiyar mu bango yafad’a Mata tarasu…
Haka yasa muka Zama marayu nida Yaya Iro,cikin ikon ALLAH shima yyi aure ak’auyen” lokacin da naji gwamma na mutu da rayuwar shine mutuwar mahaifinki da ciwon ciki yakasheshi a “yanxun haka Yaya iro Yana da yara3 bilkisu,Bashir da aminatu… sannan ta sanar da Abdallah dalilin zuwansu kaduna dakuma abinda yasami yarima HAMZA…
Hawaye kawai Abdallah keyi “sbd tausayinsu ,Ashe dama wannan dalilin ne yasakasu barin garinsu “sai gashi yajeho riyan arayuwarsa… lallai wani Abu sai ubangiji”tabbas har ya mutu bazai iya yafewa mom ba sbd ta cutar da rayuwarsu matuk’a”saidai Alhmdllh tunda asannu ALLAH keta warware musu abun…