AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Taslim kuwa cike djin haushin Alhasan tana ganin yatakurawa rayuwar”itafa Sam bataso dawowar su gdn ba”kada yyi zaton sbd tana gdnsu yanemi takata ko yimata Gori”ai basu sukadawoba ca akayi sudawo”
Da wannan tunanin ta isah part d’in Alhasan d’in…
Bayan tagyara ko Ina”tanama kok’arin fita”wayarta tayi ringing”d’agawa tayi ganin hakim course mate nata”har ka isone?”tafad’a, kasancewar d’azun ta kwatan ta Masa gdn”ok ganin zuwa”
Kai tsaye bakin get ta nufa ,kasancewar jikinta doguwar riga ce gwont dark purple da veil tayi rolling…
Yana tsaye gaban motarsa Yana murmushi “itama fuska asake ta k’araso suka gaisa,Yana cewa gobe zai wuce kano(garinsu) kasancewar yaxo daurin aurene a kaduna shine yabiyo su gaisa,dukda shi sonta yake,Amma ita saita nuna batama ganeba…
To Amma muje ciki ko ruwa kasha Dan ALLAH….kafin yyi mgn taga Alhasan gabansu Yana huci ,fuskarsa murtuk bbu alamar wasa acikinta,yace ke shiga ciki”
Tabbas yamata kwarjini”hakan yasa tace Dan ALLAH Yaya kayi hakuri course mate d’ina ne , tafiya ma zaiyi,yabiyo mu gaisa..wani sanyi yaji aransa,gashi dama dason girma,kansa yafasu…sai yabawa Hakim hannu suka gaisa cike da basarwa yace aidakin kaisa ciki ko ruwa yasha..Hakim yace ah ah nagode barama na wuce”yafad’a sbd tsab yagano wannan guy d’in son taslim yake…
Bayan yashiga mota ,taslim ta d’aga Masa ,hannu tana kokarin komawa ciki”Alhasan yace dg yanzun kada nakoma ganin ki da wani nmj”akan wane dalili?”
Basai kinjiba”sannan kije kidamaman kunun gyada…ni wlh nagaji!ok bara nasanar da ammi cewa bazakiyi ba”nifa bacewa nayi bazanyibaHmmmm”oya muje inkin gama kisameni adakina”
Batayi mgn ba ta wuce,cikin gd”yabi bayanta…Yana tunanin hussy Yana dariya,Ashe tanason Faruq ,iyayintane yahanata ta nuna…
######
Cike da farin ciki bayan sunyi sallar asuba ,suke sanar da mlm anga ummi”sosai yatayasu farin ciki”kafin yacewa Abdallah nasan kanason komawa gd ko?” Cikin girmamawa Abdallah yace eh mlm”mlm yace Masha ALLAH to kayi hakuri zuwa nan da kwana 3 ka Ida shanye maganinka”nakara baku adduo in tsari tukum sai kutafi…
Abdallah yace to shikenan ALLAH ya kaimu…
Gaba d’aya zaune suke a babban parlourn gdn”harda hjy Kaka da ga kugunta gana Alhasan Yana zuba Mata shagwaba sbd tunda sukazo take mugun jidashi”yyinda hussy ke kusada Abba”
Acikin 2 days da dawowarsu sunyi bala’in canzawa dg ummin har yaran..
Abba yadubesu yace…
To Masha ALLAH “Alhmdllh mungode ma ALLAH Mai rahama Mai jin Kai”su Abdallah sai bayn kwana 3 zasu dawo, yafad’a mun d’azun damukayi waya insha ALLAH.kowa yace ALLAH ya maidosu lfy…kafin yaci gaba to husaina zata cigaba da aikinta na nursing ,yyinda Alhasan shima zai Fara aiki abanki dg gobe insha ALLAH”
Sannan Abdallah inyadawo ,byn yahuta shima zai koma campany d’in sa yacigaba da aiki ,Amma kafin haka sai anyi taro na nuna farin cikin warkewarsa ,sbd har yanzun awaje bbu Wanda yasan be mutuba,garama jiya nasanar da ma’aikatan gdn nan da Alh bukar”cewar be mutuba…
Umma tace eh gsky sbd inya koma aiki mutane ,hankalinsu zai rabu ayita wasi wasi…..
Bayan kwana3
Share
BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????
???? AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????
Story & written by mmn fareesa
Happy Sallah all my fans! ALLAH ya maimaita Mana yakarbi ibadunmu????????????
Godiya….Ina Mika godiya ta sosai agareku masoya wannan novel…ada nace bazan cigaba ba Amma sbd magiya dana samu ana hadani da ALLAH yasa Zan ciga ba har karshe d neman sa da jamaa keyi…Amma insha ALLAH dg garesa bazan koma rubuta novel ba….sai dai in true life story ne… nagode????
Wannan shafin sadaukarwane gareki aminiyar k’warai mmn sultan.marubuciyar ( Y’AR SADAKA)
ALLAHU yakai haske kabarin baba yajikansa da rahama…???????? Ameen…
P49
Bayan kwana 3…
Riyan ce da Abdallah zaune gdn baya”yyinda hafis da driver ke gdn gaba zasu tafi kaduna sunbar kauye…
Jigum riyan tayi duk jikinta yyi sanyi sbd nasihar da mlm yyimusu dakuma shawarwarin daya basu..gameda su dage da addu o in tsari sbd ita addua takobin mumini ce!
Juyowa tayi ta saci kallon sa…caraf suka had’a ido da sauri ta janye idanunta dg kansa…shikuwa gogan murmushi yyi Yana kokarin aza hannunsa kan nata ita Kuma Taki Bari..
Yyinda motar ta dauki shiru bbu Mai mgn, hafiz ne yakatse shirun gun cewa Abdallah ango ango!! Banza yyi dashi be kulasaba shikuwa Hafiz murmushi yyi yace gsky friend kauyen nan yakarbeka saidai kayi duhu Amma nasan damun koma gd zaka washe..kallon riyan Abdallah yyi murya qasa qasa yace Wai da gske nayi duhu?”
Harararsa tayi had’e da cewa ai dama kaiba fari bane nafika haske….wani mugun murmushi yyi yace hmmm nidinko?”zamu had’u ai Zaki gayamun da hujja nidake wayafi wani fari… hafiz ne yace Wai abokina kus kus din me kuke haka ko duk murnan ce ?zakuje gd..bansaniba D’an sa ido kawai Abdallah yabasa amsa Yana harararsa ta madubi…
Kallon sa yamayar gun riyan dake saurarensu yace oh wai naga ke ko zumudi bakyayi zamuje muga family mu ko?”ahankali tace hmmm ai farin cikin danake bazai musultuba kodan sbd AUREN WATA SHIDDAN da akamun awarwaresa sbd kasan har munshiga 8 month da aure!…wani Abu Mai kama da faduwar gaba Abdallah yaji Amma sai yadake be nunba..saidai tunani yake aransa dama har yanzun riyan Bata sonsa kudirinta na nan na sai sun rabu?bazata iya sonshib akodan sbd ya na d’an’uwanta na jini…amma ko sama da k’asa zasu had’u bazai iya rabuwa da itaba…gaba d’aya sai yaji zuwa kd d’in yafita aransa sai ya ji kamar su dauwama a k’auyen”sbd yasan yanxun bagu d’aya zasu zauna da riyanba…balle yakalleta Koda zata Masa tsiwa yaji dad’i,sunkwanta gu d’aya suci abinci atare.. Kuma inhar tasanar Bata sonsa zaace araba aurensu…karar bud’e murfin motar da riyan ta yi yadawo dashi tunaninsa.,,,,,,Ahankali yabude murfin motar yafito…lumashe ido yyi Yana karewa gdn kallo tamkar yau yafara shigowarsa ,ganin komai yake tamkar amafarki” Yana maijin wani irin farin ciki Wai yau shine agdnsu zaiyi ido 4 da mahaifiyarsa da k’annensa…gaba d’aya ma’aikatan gdn suka nufo su suna gaida Abdallah damasa murnar warkewarsahade da dawowar mahaifiyar sa..
Itadai riyan tana gefe gu d’aya ranta fari k’ar da farin ciki,tana kallon yadda Abdallah be iya boye farin cikinsa Yana gaisawa d jamaa”tamkar ba Abdallan data sani adaba Mai girman Kai…
Hafiz ne yajanyesa Yana cewa kabar nurul khalbinka nata jiranka kushige muje…yafada cike da tsokana… yyinda riyan batace komaiba tabi bayansu suka bar parking space din.,,,,
Babban parlourn gdn suka nufa”
Tun kafin su karaso su hussy,alhassan,taslim,abba,ammi ummi,umma suka fito….atake Abdallah yaji hawayen farin ciki na zuba dg idonsa azuciyarsa kuwa Yana tir da halin mom data iya raba d’a da uwa…hussy da alhassan har rige rigen zuwa suke su rungume Abdallah sbd sunyi vedio call sunsa…bbu musu yyi hugging nasu back shima…yyinda riyan ta ruga aguje ta rungume ummi dake kukan farin ciki…shikansa abban hawayen ne kwance a idonsa yadai ki Bari su fito…ita kuwa ummi cikin kuka ta rungume riyan sbd Bata iya rungume Abdallah tana kawaicinsu na Fulani tunda d’an fari ne Shi..
Bayan ta rungume ummi sannan ta rungume ummanta tana kuka,” kafin su hussy su sake Abdallah yaje yayi hugging na abba..