AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Muryar hjy Kaka tasaka Abdallah yanufeta ya rungume”, yyinda riyan hussy ta ringumeta.
Feedo natsaye da tulelen cikinta ,taslim na gefenta d ammi…cikin subutar baki hafiz yace oh my feedo sannuki kinji bake kadai cikin nan yata kuraba wlh har Dani shiyasa na k’agara ki haihu Kona rik’….,tsawar da ammi ta Masa yahanashi k’rasawa…Yana dagowa yaga duk sunshige babban parlourn gdn….””Sosa Kai yyi had’e da kallon feedo dake kusa dashi yace mmn baby muje ko”harararsa tayi cikin yamutsa fuska tace gsky baka kyautamun kana bani kunya wlh.
Yanzun ji yadda kawani Yi subutar baki…dariya yyi had’e da Kama hannunta yace I’m sorry kinji…yafada suka shige ciki.,,,,
Gaba d'aya yaran nakan carpet zaune manyan nakan kujera suna ta murnan ganin juna... Abdallah kuwa Yana zaune kusada k'afar ummi hannunsa da kansa kan cinyarta yanajin wani irin nishadi Wai yau shine yakejin dumin mahaifiyar sa...
Bayan wasu mintina kowa ya nutsu…Abba yasa akayi addua”kafin yyi gyaran murya yace Masha ALLAH ALHMDLLH mungodewa Allah daya nuna Mana wannan rana.. sannan ayanzun Zan sanar da ku yadda akayi auren Abdallah da riyanatu yakasance…..kaf Abba yasanar dasu mom ce ta had’a AUREN WATA SHIDDA sbd wani buri nata gashi yyi sanadin warwarewar matsalar su”
Umman riyan kuwa Tasha mamaki afili tace dama riyan da Abdallah bakwasan juna kukayi aure?”
Da sauri Abdallah yace eh amma yanzun munason juna….ummmi tayi saurin dubar riyan tace Wai haka y’ata ?”karki cuci kanki ki fad’a Mana inbakiso araba auren tunda na yarjejeniya ne kuk…Dan ALLAH hafiz kasanar dasu wlh munshirya pls Abdallah yatari numfashin ummi tamkar zaiyi kuka… hafiz yace bbu ruwana ni…riyan kuwa tashi tayi fuska bbu walwala tabar parlourn…ummanta na kiranta batako tsayaba.
Ummi kuwa bada gaske take nufiba ” tanaso ne riyan ta jawa Abdallah aji tanema wa kanta daraja…
Shikuwa Abdallah duk yarude…yyinda hussy da alhassan keta dariya abinsu “Abdallah kuwa murtuke fuska yyi yadawo sak Abdallan sa nada “
Yadubi su hussy fuska atamke yace dallah malamai kuyi ma mutane shiru ko kuwa wlh yanxun nabaku mamaki,sai wata dariya kuke saikace sabbin kamun hauka”banida sabo Koda …haba abokina ai basu suka kashe zomanba…wata uwar harara Abdallah yabankowa hafiz “hakan yasa hafiz murmushi yyi shiru”
Ammi ce tayi murmushi tace abi su ahankali “kukuma Yan saka ido saiku kiyaye”tabe Baki hussy tayi sbd atake Abdallah yyimusu kwarjini tuni suka nutsu “
Tashi Abdallah yyi yace Abba abamu key din part namu naje na watso ruwa.
Abba yace to muje ko”ummi tayi saurin cewa shidai yaje Amma banda riyan tana nan bangarenmu…umma tace ah ah Yaya HAJARA kibarta tabisa sukoma Dan ALLAH….bbu ruwanki nida yatane! murmushi umma tayi sbd tuni tagane abinda ummi ke nufi…shikuawa Abdallah Sarai yaji Kuma beso hakanba yabidai Abba suka fice..
Hafiz ma shida feedo fita sukayi”
Taslim ce ta tshi zata wuce, tazo gab dasu alhassan ahankali tace hmmm naji dad’i sosai da Yaya Abdallah yadawo kosu oh oh sun bar mutane su huta “sbd in izzace mutum yaga Wanda yafisa Kuma mutum yamun wani Abu na hadasa da yah Abdallah ehe…
Murmushi alhassan yyi sbd yasan dashi take saurin tashi yyi shima zai fita “aikuwa sai taslim tafasa fitar gudun su had’e .
Riyan kuwa Koda ta tshi d’akin su hussy ta nufa dukda batasan ko d’akin su waye ba…
Takusa 30 minit sannan hussy tashigo da sallama ta zauna gefwn bed kusada riyan ,tana murmushi tace kanwata Kuma antyna! Ashe kina nan ,kinbar mijinki yanata Shan kamshi..gsky Yaya Abdallah akwai izza Kinga fa yau yafara ganinmu Amma Kinga yadda yake Mana masifa! murmushi riyan tayi tace hmmm laifi kuka Masa shiyasa”
Hussy ta gyara Zama tace ” hmmm ai gayacan zai tafi part naku ummi tace Kuma Baki binsa…zaro ido riyan tayi had’e da cewa da gske Dan ALLAH?” Hussy tace kinsan anty riyan na fahimci Yaya namiki wani irin so ki Kama ajinki Dan ALLAH ki garasa tukum ki amince Dan nasan kina Sansa tungashi kin razana jin nace ummi tace bazaki bisa part naku ba”…
Kinga dole ki koma skul gsky sbd kisake sani meye rayuwa Kinga dai mijinki yadda yahade da yawa dole Mata suruka Kai Masa farmaki…
Riyan tace insha ALLAH Dan wlh inada zafin kishi…dariya hussy tayi tace to ko dole kizage damtse ki rik’e abinki Gam…yanzun ki shiga wanka lokacin lunch yakusa…
Zazzaune suke kan kujerun dake dining area….riyan Tasha kwaliya cikin doguwar riga ta lace orange Masha ALLAH tayi kyau dukda tayi duhu sbd zamansu a kauye”ga wani k’amshi na musammun dake fita ajikinta….su hussy da taslim na gefenta da feedo..sai su umma dake gefe ” hussy ce tafara seving nasu …batagamaba Abdallah yashigo sanye da jallabiya Fara sai zuba k’amshi yake,yyi kyau Masha ALLAH, fuskar nan atamke sbd bayason raini”shikansa hafiz dake bayansa sharesa yyi sbd yaji haushin abinda yyi Masa d’azun ..shikuwa Hafiz bedamuba sbd yasaba da halin Abdallah…
Gurunsu yanufo tundaga nesa yaga yada riyan tayi kyau ,sai yaji besan hafis yakalleta….Yana karasowa hussy tace sannu da fitowa Yaya me zaa zuba maka…fuska bbu yabo bbu fallasa yace yauwa…kafin yadubi riyan dake satar kallonsa,fuska a had’e, cikin bada umarni yace ke tashi kiyi seving d’ina,yafada in a serious tone!
Hussy kuwa tabe Baki tayi ta zauna..
Cikin tsawa yace kobakya jine?”
Jikinta na Bari ta tashi”
Tama rasa me zata zuba Masa sbd ga abinci nan calours da yawa..shikuwa tsaki yaja yanufi kan kujerun dake parlourn yazauna..
Azuciyarsa kuwa Yana jin haushin abinda riyan tayi d’azun hakan yasa yyi alwashi ko mutuwa zaiyi bazai iya rabuwa da itaba hakan Kuma bazaisa yadauki rainiba,koba Dan Yana aurenraba ya isa da ita tunda kanwarsace… sannan dole yagyarawa yaran nan Zama hussy da alhassan and yaga kansu na rawa…kamshin turarenta ya ankarar dashi isowarta”plate ne da bowle ta aje gabansa Takoma ta kamasa drinks da ruwa..
Duba abincin yyi yaga sakwarace d miyar agushi..
Kalonta yyi ganin zata tafi” ahankali yace ke dawo ki zauna!
Ashagwabe tace Dan ALLAH kabarni natafi gunsu”
Ok tunda sunfini matsayi agunki Zaki iya tafiya amam bada yawunaba inkinga Zaki iya bin umarnina fine! Inkuma tsinuwar mala’iku kika zaba shima well…
Batace komaiba ba tazauna kan kujera tana fuskantarsa..
Hafiz daya nufosu zai wuce shida feedo d plate na sinasir a hannunsa yace kanajin dad’inka mutumina irin wannan iko haka””Tsaki Abdallah yyi had’e da kallon feedo yace mmn baby Allah yasa ki haifa Mana baby girl “
Inyiwa my riyan ta kwara! Murmushi feedo tayi tace to Allah yasa… hafiz yace hmmm nidai nasan nayi laifi wannan Shan kamshin da ake mun bazan denaba…yafada suna ficewa…
Can carpet Abdallah yakoma yyi Bismillah yafara cin abincin sa”Yana satar kallonta..can yace ke kinci abincin?”
Innaci ko banciba me ruwanka?”
Kafin yyi mgn alhassan yashigo parlourn Yana huci bema lura dasu Abdallah ba,,,
Taslim!taslim! Taslim!!! Yaketa kwalawa Kira afusace…ita kuwa suna dinning area suna lunch tana hangensa…tayi Masa sbd ita tasan Bata Masa laifin komai ba..
Isowarsa gun yyi, cikin rufewar ido yace ke ban hanaki kula kowaba?”sannu uwarta sannu ubanta kaji”cewar ummi cike da mamakin ikon alhassan kan taslim”
Cikin dabir cewa yasosa k’eya sbd yamanta suna agurin” yace Amma ummi bakiga fa Wanda yake nemantaba bbu wata tarbiyya atare dashi… murmushi ammi tayi tace kayi hakuri insha ALLAH zata kiyaye…ita kuwa taslim sai tura Baki take batace komaiba…cikin jin kunya alhassan ya wuce.