AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Abdallah kuwa tsab yaji komai ,yakuma gano alhassan son taslim yake sbd yadda yaga Yana nuna kishi tsantsa…akanta.”””

Bayan yagama ne ,yadubeta yace in anjima da dare kima shirya part namu zamu koma ko kuwa nazo na daukeki da hannuna !kin San zan iya tashi tayi tace aisai k’asa niya..tayi saurin barin Gurin”…

  ********

Da misalin karfe 8:30 pm kowa yakimtsa “Abba yace wa Abdallah suje part d’in da mom take sbd dg yau tagama zamar Masa gd,gobe insha ALLAH zaisa afitar da ita dg gidan..
Wani bacin rai Abdallah yaji sbd jin an anbaci sunan mom”
Dandai be iya musu da mahaifins ada bazaya ba..
Ummice tasaka aka Kira riyan dake d’akin su hussy”tazo itada Abdallah auka jera sai Abba suka nufi part din da mom take…

Suna….

Banyi alkawarin post kullumba…????

Share….

BY MMN FAREESA
????????????????????????????????????????

????AUREN WATA SHIDDA????

????????????????????????????????????????

Story & written by
mmn fareesa

Godiya ta musammun ga masu dogon sharhi..????????????

P 50

…..suna Murd’a k’ofar suka shiga”Abba beko kalletaba yajuya baya sbd yatsani ganinta agdn….riyan kuwa jikinta yyi sanyi tasake yadda D’an adam ba bakin komai bane agun ubangijinsa”sbd yadda taga mom ayanzun da Kuma sadda take gautsar cin duniyar…
Lallai duniya abin tsoro ce ta fad’a azuciyarta….mom na kwance bacin wari da zarni bbu abinda takeyi dama d’akin Baki d’aya tayi Baki ta lalace ta fita hayyacinta!Kashi nan fitsari nan Bata iya komai sai anmata,abinci kadai ake Bata shima Dan kada yunwa ta kasheta” shima masu aiki be ,wadanda ada suke karkashinta take wulakantasu ” yanzun sukuma suke Rama abinda ta musu… tanaji dai tana mgn Kuma…hanci toshe Abdallah yadube ta zuciyarsa na Kuna sbd daya tuna itace snadin rashin lafi yarsa da raba ummi da Abba!
Wani mugun tsanarta yaji yakaru aransa…cikin kallon tsana yadubeta Yana murmushi me ciwo yace Kinga ikon ALLAH ko?kin had’a AUREN WATA SHIDDA tsakani na da riyan sbd wata manufa Taki,byn nan kin saka ankoreta bayan kamuwata da ciwon dakece sanadi saigashi mun maidake wawiya mun boye wayonmu munbarki muga iya gudun ruwanki….yanzun Ina mashirikin bokan naki?daya kasa Baki lfy!hmmm bara na sanarmiki aurena da riyan mutu ka raba “sbd ni AUREN WATA SHIDDA alkhairi yazamarmun sbd asanadinshi Nagano bakin zaren komai…

Uhmmmm!ehemmm!tari yasarke mom” Baki jirkice maganar Bata ma fita sosai take ba Abdallah hakuri hawaye na zuba akuncinta…riyan daketa kallonsu tace hmmm yanzun kin yadda da ake cewa d’an hakkin daka Raina shike tsone maka ido?”

Dan nasan kin daukeni k’aramar alhaki gashi Kinga akasin haka”ALLAH ya shiryi masu hali irin naki dg karshe sai muce to ayi hauka lfy sbd kinsan bokanki yatada Miki haka…Tsaki Abdallah yyi yadubi Abba yace pls Abba gobe insha ALLAH kasa afita da ita akaita bakin bola ko jibji sbd dasu tadace nan yakamata yazama muhallinta…

Bejira amsar Abba ba yafice daga d’akin sbd yadda zuciyarsa ketashi daya shaki warin d’akin ….

Itama riyan fitowa tayi”tana kokarin wucewa Abdallah yyi saurin finciko “Ashe labewa yyi a corridor din”ihu riyan ke kok’arin sakawa sai tashaki kamshinsa hakan yasa takane shine..

Mlm meye haka? Koka cikani ko nama ka ihu” so what? dankinmun ihun nasandai ni mijinkine na biya sadakina…wata harara Riyan ta bankoma sa dukda be ganiba” tana mmkinsa” Wai yau Abdallah ke fad’a Mata yabiya sadakinsa…ta yadda da ake cewa nmj bashida kunya..
Abba ya fito hakan yasa Abdallah saurin cika riyan ,tun kafin abban ya iso tabar Gurin…yyinda Abdallah yaji tamkar yabita ,Dan yasaka rai yau agado daya zasu kwana.,,,,,

Magana sukayi da Abba kafin suyi sallama Abdallah ya wuce part nasa zuciyarsa bbu dad’i…toilet yawuce yyi wanka sannan yyi Shirin kwanciya..
Amma bacci yaki zuwa riyan kawai yake tunani ,da Kuma tuna baubuwan da yyimata abaya har wani nauyi yarukaji naja Kai gsky tsakaninshi da mom saidai yace ALLAH ya isah and ita tamasa tarbiyyar wulakanta jamaa da kyamar talaka…ya lura dole yazage damtse indai yanason riyan ta dawo hannunsa gsky gashi gobe zaije office yaduba ma’aikatansa da komai da komai sbd Hafiz yasanar musu Abdallah be mutuba sannan zaije Gurin liman me tsaron makabarta yasanar Masa ya warke…da wannan tunanin bacci yyi awon gaba dashi.,,,,;;;***

Washe gari Gurin karfe 8:22 am Abdallah yafito cikin Shirin zuwa office yasha fararen suit sai k’amshi ketashi ajikinsa…kwana 1 da dawowarsu Amma har Yacanza “fuska bbu walwala yyi Sallah ma awaiting porlour”ummice da ammi sai umma dasu taslim , yyinda hafiz suna part nasu..cike da girmawa yaran suka gaidashi harda riyan data nuna ko inkula da ganinsa” hakan kuwa ya k’ular dashi”
Matsawa yyi yagaida iyayen nashi “umma ce ta tambayeshi fita zaiyi?” Yace eh zaije office tace to kajira ka karya Mana( break fast) ah ah umma nayi acan nama makara wlh ,yafada Yana nufar part na Abba..

Bayan yafito dg part din Abba yadaci kallon riyan yaganta cikin gayunta kanta yasha gyara tayi parking naza…wani kishi yaji yataso Masa yasan hafiz ko alhassan wani zai iya shigowa”Amma shine tabar Kai bud’e haka” be San sadda yace RIYAN zonan ba!
Intazo ta maka me?canake yanzun ta isa ka gane matsayinka agunta ko na tambayeta jiya ,tace bazata cigaba da Zama da kaiba sbd haka saika sallameta ko…haba Wai meye haka ,ke Kuma Zaki tashi kije kiji Kiran da yake Miki ko kuwa cewar umma atsawace… yyinda Abdallah yakulu da yadda ummi ke Masa fad’a agaban Yara..cikin kakkausar murya yace dallah malamai kubacewa mutane da gani mitttsss yaja dogon tsuka ya fice…

Riyan kuwa dama aranta taso zuwa Kiran”

Sum sum taja mayafinta ta fice”

Gurin flowers tagans atsaye yabada baya gabda parking space.

Ahankali tace Yaya gani!

Juyowa yyi sukayi 4 eyess…ta tsorata da yadda taga idanunsa sunyi jajir ga aLamar
b’acin Rai atare dashi k’ara ra”tambayar kanta take Miya Bata Masa rai?

As from to day nakoma ganinki bbu Dan kwali agdn nan wlh nidakene agdn nan sannan ki cigaba da nunawa duniya cewa bakya kaunata da nuna halin ko ingula dakike nunamun…bejira amsar ta yyi wucewarsa yashige mota driver yaja body guards nasa suka rufa musu baya…

Jiki asanyaye riyan ta juya gefe guda tanajin dad’i,sbd shawarar hussy datace ta zauna bbu dankwali indai true love yake Mata dole yaji kishi” gashi Kuma ta gane irin son dayake Mata,jitake kamar ta sakko su shirya…

Bayan sati 2 gaba d’aya Abba ya nemawa riyan skul harta Fara zuwa amm a ss3 aka dauketa yyinda hussy tafara aikinta na nursing ,gefe guda Kuma shima alhassan Abba ya aza shi a harkokinsa, sannan magabatan faruq sun zo nemawa faruq auren hussy inda Abba yasa auren 3 month, yakuma sanar da alhassan muddin har lokacin yazo to zai hadashi da wacce yagadama tunda yakifito da wacce yakeso…gefe guda Kuma feedo tashiga watan haihu “zumudin gun hafiz baa mgn..

Tsakani riyan da Abdallah kuwa wasan buya ake kwata kwata Bata San fitowa inyana Gurin ko intasan zaizo zata gudu ,tun abun be damunsa haryafara damunsa da halin ko inkulan datake nunawa akansa ga Kuma jama’ar gdn nagani basa tsawatar Mata….yanason tarar hafiz da zance Yana gudun yyita Masa iskanci ko yadawo da abinda yafaru ada…

Mom kuwa tun awashe garin da Abdallah yadawo Abba yasaka Mai gadi dawasu maaikata sukafice da mom dg gidan yace su ajeta duk inda suka gadama…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button