AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da misalin karfe 2:30pm mai adaidaita yasauke harira d riyanatu a kofar gidan alh kabir girma,byn sun sallamesa suka nufi k’atan get d’in gdn da riyanatu tashagala d kallo wani gefe na zuciyar najin faduwar gaba had’e da tsoro.

Get man ne yazo yabude karamar kofar shiga ,Koda yaga harira bbu musu yabasu hanya sbd yasanta ta Saba zuwa gdn.

Harira ta kalli riyanatu tace to yannan ki kama kanki kinjiko kada ki nuna kinada wayo kinji?” riyanatu tace to hade da mamakin miyasa harira tace haka.

Tafiya sukayi mai Dan nisa, yyinda riyanatu ke yaba kyawun gdn a zuciyarta,har suka iso kofar da zata sadaka da babban parlourn gdn.

Sallama sukayi kafin su shige ciki,bbu abinda ketashi a parlourn sai kamshin room frishners da turarukan wuta sai sanyin AC.

Masu aikine keta Kai da kawowa ,su suka amsa sallamar su, sannan byn sun gaisa harira ta bukaci suyi Mata mgn da hjy …

Sunkai kusan minti20 zaune har zaman ya ishi riyanatu ta Kuma tabbatar matar gdn batasan darajar bak’o ba.. maganar mom ce da kamshin turarenta yadawo da ita tunanin ta d’ago kanta da sauri sukuyi 4eyes da mom ,suduka atare gabansu yafadi, yyinda riyanatu ta sunkuyar dakanta k’asa.

Cikin yatsina had’e da izza mom tace wannan itace yarinyar?” Ta fad’a cikin gadara fuska bbu walwala, yyinda wani b’angaren zuciyarta ta tsorata da kyawun yarinyar.

Harira tace eh”

Riyanatu ta yi saurin dukawa tace hjy Ina wuni?”

Lfy ,ta amsa atakaice”had’e da cewa to da farko dai inason ki bud’e kunnanki kijini da kyau game da aikin da zakiyi .

Cikin girmama riyanatu ta ce to”

Mom tace da farko dai ranar monday Zaki Fara aikinki,kitabbata karfe7am tamiki agdn nan,sbd my son karfe8:am yake tashi to kafin yatshi kin gyara masa parlourn sakin wanke Masa toilet kin hada Masa ruwan wanka.

Inyashiga wanka ki gyara bed room d’in sa,kafin kije kitchen gun kuku ki karbo Masa break fast nasa kiyi serving nasa, sannan ki gyara Gurin da Kuma sake gyara bed room nasa sbd bayason k’azanta shi mai tsabtane sosai Dan in har bakida tsabta zaku Bata dashi gsky fuk in kika gama zuwa 9 am Zaki iya tafiya musammun inkina skul ,sai 2:pm kidawo sbd 2:30yake shigowa yyi wanka yaci abinci ,Zaki cigaba da kulawa dashi har4:00 pm sbd Yana fita Kinga inkina islamiya sai kije dg nan ki wuce gd sai wata safiyar.

dg karshe my son bayason surutu had’e da shishshigi,nima haka, sannan ban hada Dana da kowaba muddin ki ka b’ata Masa rai can hukuntaki nakuma koreki , sannan kada ki yi zaton d’ana mutumin banzane kice Zaki ja raayinsa da kyawunki to ba haka ABDALLAH yakeba.nasake gayamiki ki kularmun da yaro kada ki bata Masa rai….

Jikin riyanatu yyi sanyi,jiki bbu lakka tace to insha ALLAH Zan kiyaye.

Harira tace ai hjy batada matsala yarinyar nan….ban tambayekiba ,mom ta katse harira hade da zuge jaka ta fito da kudi ta mik’awa harira , sannan tace albashin ta a wata dubu 30 be,sai Monday din.

Harira ta karba , sannan tayi godiya , sannan tace ai hjy anyi hutun boko itakuma sai islamiyya take,mom tace bbu damuwa akwai islamiya farkon layin nan zanma ya’u direba mgn asiya Mata foam intazo saita ruk’a zuwa.

Godiya su riyanatu da harira sukayi kafin suyi sallama su fice,mom tabi bayansu da harara.

Koda suka fita , adaidaita suka hau ,har gd harira ta raka riyanatu ta ma su umma bayanin komai da irin aikin da riyanatu zatayi da albashinta da sakata islamiya duk sunji Dadi sosai , sannan harira ta dubi zuwaira tace ammainaganin kafin Monday din yaka Mata akoya Mata kamar…
Wanke bayi da yadda ake hada ruwan wanka da turare d’aki dasu moping da sauransu dukda nasan xata iya amma gara ak’ara nuna gudun kuskure ..

Zuwaira tace to shikenan Zan saka Fatima suje gdnsu yusra kawarta tunda suma masu haline sai ta kara ganin yadda ake amfani da komai .

Harira tace to sannan suka yi sallama.

A cikin kwanaki biyu riyanatu ta koyi duk abinda akeson ta koya, yyinda riyanatu ke ta faman Yaya zata kasance da ita gobe Monday agdn aikinta.

Monday….

Innaga ruwan comments kujini da safe….
Happy juma at kareem❤

Share pls

BY MMN FAREESA
????????????????????????????????????????

???? AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????

Story & written by
mmn fareesa

Dedicate to all my fans ana mugun tare????????

p6

      Monday

""""Tun  gurin karfe 6:30 riyanatu ta shirya cikin doguwar riga bak'a y'ar kanti tasaka hijab Fara "bbu wata kwalliyar datayi dg powder sai kwalli ta shafa ,sukayi sallama da umma dasu Fatima dake Mata fatan alkhairi itada mama zuwaira"

Adedeta tahau ,ya ajeta a unguwar nassarawa G R A.byn ta sallamesa tashiga ciki kasancewar get man yasan da zuwanta.
Waiting parlourn gidan ta nufa gabanta na mugun faduwa,tasami mom da Yan aiki”har k’asa ta tsugunna ta gaishe d mom ,ta amfa fuska a tamke yyinda tasaka ladidi(d’aya dg cikin masu aiki) ta nunawa riyanatu part d’in Abdallah..,,,

   Suna zuwa kofar shiga part d'in ladidi ta juya ta tafi"

Wani mugun tsorone fal aranta ,amma saitayi jarumta had’e da yin addua azuciyarta,kafin ta murd’a kofar tayi sallama”bbu kowa a parlourn”
Tasbihi riyanatu tayi da ganin wannan kayataccen parlourn a zuciyarta ,ko Ina k’al amma Wai nan sai an gyara sai kamshi ketashi na room frishners aciki..
Kofar dake cikin parlourn ta kalla hakan yanuna Mata nan be bed room d’in.
Tsintsiyar data shigo da ita had’e da mofa da wani towel ,tasaka ta Fara gyaran parlourn had’e da karkad’e kujerin d kayan kallo , sannan tayi moping.
Ta duba taga komai yyi daidai.
Sannan ta nufi kofar bed room gabanta na dukan Tara Tara,tayi Knocking yafi sau 3 shiru hakan yasa ta murd’a kofar tashiga ciki ahankali had’e da yin sallama,amma shiru”bed d’in tasaci kallo ta hango mutum kwance atsakkiyar yarufe jikinsa d alama bacci yake.
Kofar dake da keda carpet takalla ganin harda silifas akan carpet din haka yatabbatar Mata da nan ne toilet..

Addua tayi ta shige ciki ” sai zare ido take sbd atsorace take,Saida ta k’arewa toilet din kallo tukum sannan ta Fara aikinta , azuciyarta tana mamakin Wai bayine wannan aka zubawa kayan alatu haka tamkar baza a mutuba , lallai mutumin nan d’angatane sannan akwai muguwar tsabta gsky….
da wannan tunanin ta gyare toilet din k’al har tayis d’in jikin bango Saida ta wanke , sannan ta wanke hannunta ta fito…..tana fitowa taga mutum tsaye gaban mirro dg shi sai towel iya guiwa da alama wanka zai shiga ,yabada baya hakan yasa bataga fuskarsaba..
Ta tsorata ainun takuma razana sbd batatab’a ganin nmj hakaba “da sauri ta d’auke kanta had’e da cewa ranka yadad’e Ina kwana?” har sau2 jin yyi Mata banza sai ta nufi Gurin bed Dan ta gyara.
Shikuwa Abdallah uffan beceba Kuma be kalleta ba yawuce toilet ya rufe,k’arar rufe kofar ya ankarar da ita baya cikin room d’in”
Ajiyar zuciya tayi azuciyarta tace oh ikon ALLAH lallai mutumin nan baisan darajan d’an adam ba …

Cikin minti 25 tayiwa bed room d’in fas,ta duba kan mirro ta dauki air freshener ta feshe ko Ina harda parlourn tuni guri yakaure da k’amshi..
Bed room d’in ta koma ta ajiye air freshener din sannan ta duba wardrobe din haggu cikin saa taga bed sheet da sauri ta dauka ta canza ,sbd Fatima ta Bata shawarar ta rik’a canzawa tunda ance shi mai tsabtane.
Wayoyinsa data aza kan mirror taje da nufin ta dauka ta mayar Masa kan bed inda tagani… adedenan taji motsin zai fito da sauri ta janye hannunta ta nufi kofar fita dg bed room d’in…

Waye zai fitomiki da kayan da Zan saka?”

Yafad’a cikin husky voice,tamkarbashi yyi maganarba”

Cak yatsaya hade d juyowa sukayi 4eyes dashi”Masha ALLAH tace azuciyarta sbd ganin baiwar halitta agun sa,tayi mamakin jin yyi hausa ,dabaiyi mgn ba saitace balarabene bayajin hausa….tsakin dayajane yasata janye idanunta dg barin kallosa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button