AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ahankali tace to amma injin nauyin Kiran sunansa Kai tsaye….. ringing d’in wayarsa ta katse Masu mgn,da sauri ta shi da nufin Kai Masa.
Hafis kuwa yace Kinga kijirasa zaizo tunda mom tace mu basu waje,nima na wuce inyazo ki fad’a masa.
Bata kallesaba tace to shikenan nagode, murmushi yyi yace pls kici abincin nan kinji sbd ya koshi karshe ma badashi zaayi….da sauri ta ce ai hjy tace kada na ci ,naje can na karb’o acikin na masu aikin gdn.
Shiru Hafiz yyi,Yana tunanin hali irin na mom,sbd gudun kada ta disgata yace kada takai wayar”Kai Anya matar nan akwai gsky alamarinta?”
Kallon riyanatu yyi yace ki ciki kinji inkin gama ki Kai kayan gun masu wanke wanke ,baza tasan kinciba sbd in ya rage abinci masu gadi yake ba.
bejira amsarta ba yafice dg parlourn.
Ita kuwa riyanatu bbu bata lokaci taci ta koshi ta gyara parlourn tas , sannan ta fito da kayan da sukayi break ta nufi part din ma’aikatan gdn,ta tambayi gun masu wanke wanke aka nuna Mata takai masu.
Komawa tayi part d’in Abdallah,da nufin dauko Masa wayarsa ta Kai Masa,tasamesa zaune hakimce kan 2 seeter yana latsa waya, sallama tayi …ya amsa akan labb’ansa “
Ahankali tace dama zantafi gd!
banza yyi da ita dg karshe ma sai ya rufe ido “tab’e Baki tayi had’e da dage kafad’a alamar ko ajikinta “saidai batasan duk Yana kallon ta ba”hijab nata ta gyara ta nufi kofa da nufin fita….keeeeeee!cak ta tsaya cikin k’uluwa ganin raininwayonsa yyi yawa besan tana d’aga masababa”tagaji haka nan,shiru tayi ita batayi mgn ba ,Bata Kuma juyoba” yyinda shima yyi shiru.takuma yi alkawari muddin bazaiyi mgn ba to itama bazatayi ba saidai sudauwama a haka .
Shikuwa gogan yacika yyi fam da rainin hankalin wannan ta tsitsiyar yarinyar nan,wani gefe Kuma Yana tunanin magan ganun mom na d’azun byn tafiyar su Hafiz,yarasa me Hafiz yakashewa mom, sannan miyasa batadamu da Abbansa yadawo gd ba koma maganar sa bataso yyi shin Wai Mike faruwa ne haka ?””
Sake duban riyanatu yyi dake tsaye tun d’azun databashi baya ,tsaki yyi azuciyarsa yace me wannan tsakuwar yarinyar nan ke nufi?” wato ita bazatayi mgn ba kenan ,aiko in har sainayi mgn zata yi to saidai ta kwana anan,kuma ta tafi to bakin aikinta…..
Riyanatu kuwa…
Share pls
BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????
???? AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????
Story & written by
Mmn fareesa
Not edited
p8
“””Riyanatu kuwa gajiya tayi da tsayuwa “sotake ta ta fi gd “tana gudun kada ta tafi yakoreta.azuciyarta tace bara na kyalesa kawai “cikin jin haushi ta juyo tana murgud’a baki tace Dan ALLAH kasanar dani me zanyi ?”
banza yyi Mata ,Kuma Yana lura da murgud’a bakin datayi”sai da yagama Shan k’amshinsa tukum “ya ware golden eyes nasa akan fuskarta “ya had’e girar sama d k’asa”saurin janye idanunta tayi sbd jin yyi Mata mugun kwarjini….mitttsss yaja tsaki hade da cewa ke vileger girl wakika bari yagyara Miki bed room d’in?”
and last kika koma kallo na ko yimun mgn atsatstsaye amatsayinki na hadimata to Zan koyamiki manner of toking”maana ladibban mgn dan nalura da alama kinada k’wak’walwar kifi…. mitss yakoma Jan tsaki akaro na biyu sannan yadauki wayoyinsa yafice had’e da buga kofar da k’arfi….
Hawaye masu zafine suka wanke Mata kunci sbd jin haushin abinda yyi mata….oh dama haka masu aiki ke ganin irin wannan tozarcin?”lalai dole ma tabar gdn duk rintsi ,amma bazata gayawa umma komaiba kodan sbd kada taji haushi ko hankalinta yatashi… ajiyar zuciya tayi sannan ta wuce ciki tasake gyarawa tukum ta fito ta nufi part d’in mom …
Ladidi ta gani a waiting parlou tace Ina hjy Dan ALLAH?"
Tace tana parlourn ta,Kinga kofar can ta nuna mata da hannu”kofar ta nufa ta murd’a….cak ta tsaya sbd jin wasu maganganu da kus kus….innalillahi wa inna ilaihir Raju un kawai Riyanatu ke maimaitawa azuciyarta had’e da saurin toshe bakinta”sbd gudun kada aji motsinta “ahankali ta ja kofar had’e da yowa baya jiki na b’ari tabar part d’in..
Tunani take azuciyarta shin Wai meke faruwa ne?” Ita Tama fasa zuwa gd bara kawai tabari sai 6 d’in kawai tunda sai taje islamiyya”guri tasamu a gurin flawas na gdn tayi ta gumi tana kuka shin Wai wannan wace irin masiface ne?” Itadai rabon wahala yakata gdn nan da yanzun suna garinsu Kai ita dai tsakaninta da yarima ALLAH ya isa sbd shine sanadin zuwanta garin nan”
Ajiyar zuciya tayi had’e da d’aga Kai sbd wani tunani dayazo Mata dukda atsorace take.
Tafi awa1 anan har kusan 12: sannan ta bar Gurin ta tafi gab da part d'in Abdallah ta tsaya" batafi minti12 ba ta hangosa da body guards nasa suna biye dashi har suka iso gab da ita da sauri ta tashi tsaye had'e da satar kallon Abdallah tag a fuskarsa atamke"suit d'in dake rataye kan kafad'arsa tasa hannunta ahankali ta janye had'e da binsa ciki"ganin ya sallami guards nasa.
Suna shiga parlou yace zanyi wanka”atakaice sannan yashige bed room d’in beko kalleta”girgiza Kai tayi tabi bayansa”
Toilet ta wuce ta had’a Masa ruwan wanka tana mamakin Wai baya gajiya da yin wanka dudu ba gurin8 yyiba amma gashi yanxun be fi 12:30 ba Amma zai sake”
Fitowa tayi tace ranka yad…am in ab… mitttsss yaja doguwar tsuka had’e da tashi Yana kokarin cire kayansa “yyinda riyanatu tuni ta fice.
Tana komawa parlourn “xeenat nayin sallama suka had’a ido da riyanatu…wani faduwar gaba xeenat taji,murya asark’e ta kalli riyanatu up& down tace WHO ARE U?”
Tab’e Baki riyanatu tayi had’e da Zama kan kujera…da sauri zeenat tace keeeeee y’ar matsiyata ,talaka uwar me yakaiki dakin mijina ne ?”iye bazakiyi mgn ba Dan ubanki?”
Ak’ule riyanatu tace ya isa kinzo inda bazan iya jurewa sbd banhad’a iyayena d kowaba ,kada ki koma zaginsu, sannan dakike cewa mijinki ai Ni banga alamar ke matar aure bace ajikinki sbd duk macen datasan darajan kanta bazata yi shigar d kikayi ba…..ke wawiya y’ar iska mikikaje kukayine da kika fito da bed room d’in sa?”zeenat ta fad’a tana huci had’e da d’aga hannu da nufin Marin riyanatu.
Da sauri riyanatu ta rik’e hannun had’e da cewa baki isaba! sbd banmiki komaiba…afusace zeenat na fisge hannunta ta nufi bed room d’in tana cewa inke baki fad’a ba shi dole yafad’a mun…
Turus zeenat tayi sbd ganin Abdallah gaban mirro tsaye sg shi sai towel…shi kuwa jin anshigo ya zata riyanatu kasancewar yabada baya,cikin bada order yace ki fitomin da kayan….whattttttt?” Abdallah me kake fad’a haka ?”kaddai ace yarinyar nan…. afusace yajuyo sbd jin muryar zeenat”cikin tsanar halayenta yace lfy malama ?wabaki izinin shigomun bed room?”
A k’ule zeenat tace bansaniba Abdallah dama Kai maciyin Amana ne bansaniba to wlh kasheta Zan yi…..ta fad’a tana kuka hade d ficewa…
Tuni ran Abdallah yyi mugun b’aci dan in ya fahimci zeenat tana nufin sun aikata Masha a da wannan y’ar k’auyen kome?”
afusace yajawo jallabiya yasaka yafice dg bed room d’in.,,,
Yana zuwa yasami zeenat na dukan riyanatu ta haye saman ta…wasu maruka masu rai d kafiya yabawa zeenat har sau2 ,cikin b’acin rai yace i hate u zeenat nikike ma sharrin zina da mai aikina har kina dukanta sbd ni… girgiza Kai yyi had’e da fincikota yyi wurgi da ita kanta yabigi kujera”ya kalleta da jajayen idanunsa dasukayi ja sbd bacin rai ,yace dg yau kada ki koma zuwa guna na tsaneki bana son ganinki….ya fad’a had’e da sake nufarta….juyowa yyi sbd jin anrike Masa hannu”ido 4 sukayi da Hafiz Yana girgiza Masa Kai alamar yabari”
Zeenat kuwa kuka take tana cewa saita kashe riyanatu, yyinda riyanatu duk ta kara tsorata da lamarin gdn sai kuka take”
Abdallah ya matsa kusa da riyanatu ya yyimata alamar ta tashi zaune bbu musu ta tashi…. zeenat na ganin haka ta tashi da gudu ta fice.