BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 1 to 10

_________________________

Duk da cewa ranta ajagule yake hakan bai hanata yima kawunna nan nata sauka ta musamman ba kuma Saida tayi k’orafin auren da akayi batare da ansanar da ita ba Suma sun amsa laifinsu sai dai sunbata uzurin cewa basa sone su d’aga mata hankali wai idan abin yazo lokaci guda zai wuce ba kamar afad’a mata tunda wuriba abin yayi ta damunta.

Maman islam

بسم الله الرحمن الر حيم

*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

   FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*________________________

????BA JININA BACE????

      

2021

          NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI 

MAMAN ISLAM

Page 9

Haka dai ta daure tayi musu karb’a ta musamman har zuwa lokacin da suka wuce, cikin k’awayenta babu wanda yasan da maganar auren sai haj. Zakiyya dan haka da itakad’ai suka zauna har zuwa bayan sallahr magriba sanda ‘yan kawo amarya suka fara shigowa.

Haj. Zakiyya ce ta rik’a tausarta da k’yar tasamu ta hak’ura dan da cewa tayi wallahi saitayi musu hauka sai sun ganecewa mijin mahaukaciya ‘yarsu ta aura haj. Zakiyya tace “haba k’awata waishin duk abinda na fad’a miki tun muna gidana baki d’aukaba? na sani da ciwo amma idan kika daure zakiyi dariya harda shewa kinga yanzu idan kikayi wani abu to duk abinda yasamu ‘yarsu to kaitsaye zasuce kece dan zaki aikata amma idan kika bi yadda na fad’a miki zakiga yadda zasuga kima da darajanki”

Da k’yar haj. Zakiyya tasamu ta lallab’a haj. Sailuba a wannan gab’ar har ta hak’ura ta karb’i bakin amarya yadda ya kamata har suka tafi suna yabon kirkinta ganin yadda ta karb’i amarya cikin farin ciki da walwala, tare da ita aka raka amarya har d’akinta suka tafi suna godiya

Bayan ta tafiyar sune haj. Zakiyya ta dubeta tasaki shu’umin murmushi tace ba’a faraba k’awata sharar fage ake kafin wasan ya fara”

“Allah ko k’awata?”

“Ai ke d’ince bakya ganewa baki da aiki sai fushi Kuma babu inda wannan zai kaiki sai na dama”

“Abinne ya masifar d’amin hankali k’awata amma yanzun ya zanyi?”

“Shi nake son ai ki nutsu ki fahimta domin abune da zakiji dad’insa kuma zai amfaneki batare da kowa ya fahimtaba, Kinga yanzu angon yana hanya abinda nakeso dake goben ya kasance kin gama musu duk wani aiki har abin kari kafin ki fito, kidai fito da wuri kinsan wajan yana da nisa sosai” 

“Angama amine zanyi yadda kikeso insha Allah”

_________________________

Ranar dai ango ya gwangwaje agwancinsa shi da amaryar sa Amina yayin da Sailuba ya yadda taga rana haka taga dare batako runtsaba tsabar masifaffen kishin dayake cin ranta.

Koda gari ya waye tun bayan da ta idar da sallar asuba bata komaba ta zauna ta had’a musu had’ad’d’an break wanda rabon data girka irinsa har ta manta tsab ta gyare gidan tsab aranta take cewa duk wani abu da zanyi agidannan na bankwana ne domin nima lokacin hutawana yazo.

Sanda Baffa suka fito daga d’akinsa shida Amina tuni Sailuba sunyi nisa a hanyarsu ta zuwa wajen shahararren malamain da yai k’aurin suna aciki da wajen garin wanda ake kira da kowa naka.

Sosai yaji dad’in yadda ta gyare ko ina tayi musu girki duk da cewa yaji babu dad’in fitar ta arana irin tayau daya kamata ace ta tsaya ta Kula da komai na gidan kodan bak’in dayasan cewa bazasu rasayi ba aranar irin ta yau d’in.

Bayan gama cin abincinsu babu dad’ewa kuwa saiga yayar Amina wacce takasance ita kad’aice ‘yar uwarta mace dan duka yaran malam Babba mata biyune kawai sai maza guda goma Sha uku yayin da ad’akin su Amina ita kad’aice mace sai kuma d’aya d’akin nanma guda d’ayar ce shamsiyya.

Matan malam suna da matuk’ar had’in Kai yadda zai wahala a yaransu ma kaban bance na wannan da na wannan.

Yini su anty shamsiyya sukayi kamar yadda Amina take kiranta tare da bata shawarwari da buga mata misali akan gidansu da kuma nuna mata yadda umman ta take bin nanne mahaifiyar shamsiyya sau da k’afa duk da kasancewar Nanne wacce ainihin sunanta Zahra u irin matan nanne masu fad’an tsiya, hakan bai hanata jin dad’in zama da Mariya ba (Umma) domin ita mutunce mai mugun hak’uri dan zan iya cewa duk wani hali na Amina da shiru shirunta a wajenta ta gadosu, tun bayan da aka kawota gidan malam Babba ta kama yaran nanne ta runguma tamkar nata  dake tana da matuk’ar ilimi haka take dad’a fahimtar dasu duk wani abu daya gagaresu a makaranta hakan ba k’aramin dad’i yayiwa malam da Nanne ba gaba d’aya tasakarwa Mariya ragamar yaran hatta kayansu d’akinta suka koma sannan itace ta aurar da Shamsiyya yayin da tunda aka haifi Amina Allah ya jarabce ta da masifar k’aunar yarinyar wacce tun tana k’aramar ta take da wannan hak’urin abin har tsoro yake bawa Nanne takan cewa malam kodai yarinyar bata da lafiyane.murmushi yakeyi mata a duk lokacin datayi masa irin wannan tambayar yace “Zahra’u kenan ai kowane bawa da kikegani yana da kalarsa ita wannan kalar ta kenan hak’urinta har ya zarta na uwar ta”

Baki Nanne takan tab’e tace “sam ni wallahi hakan bamin dad’iba wani hak’urin idan yayi yawa a cutane” shima dariyar yake mata baya k’ara tankawa.

Sosai shamsiyya ta d’an bata kad’an daga tarihin gidansu da irin ribar da Umman take ci na irin tsantsar hak’urin da Allah ya hore mata

Basu bar gidanba sai bayan sallar la’asar kuma har lokacin haj. Sailuba bata dawoba.

_________________________

Tunda haj. Zakiyya tafara jan sailuba wajen malami bata tab’a kaita waje mai wahala da ban tsoron wajen ba dan haka ta matuk’ar wahala tun kafin ma su kai wajen domin tafiyar k’afa ce wacce koda tayi rayuwar k’auye bata tab’a, sai dai abinda ya matuk’ar k’ayatar da ita shine yadda suna zuwa malamain ya hau zayyano mata dukan abinda ya kawosu, sannan shi da kanshi yafara dace”kinyi babban kuskure da har kika k’i yarda ki haihu da mijinki Kuma d’an uwanki Baffa domin dakin haihu dashi shine samun nasarar rayuwarki ni bana fad’awa mutum abinda zai kasance karya dan haka nake tabbatar miki da cewa ita wannan mata zata haihu itace uwar ‘ya’yansa sai dai kuma ke kin riga kingama da rayuwarki domin keda haihuwa har abada kin gama lalata mahaifarki da k’wayoyin hana d’aukar ciki shekara goma shabiyar ba kwana goma sha biyar bane babu ke babu haihu amma zaki mulki mijinki da kishiyarki yadda ranki yake so.

Duk inda wani abu mai suna tashin hankali yake sailuba ta shige shi dan tun kafin malam ya k’arasa mata jawabi ta fashe da wani fitinannen kuka domin wani iko da k’udura na ubangiji a lokacin sai taji babu abinda take buk’ata sai haihuwar sai dai ta riga ta gama da rayuwarta tun farko a tunaninta Baffa da yake d’an boko me zaiyi da tarkacen yara su hanashi sakat.

Ranar dai bata tsaya amsar sak’on komai a wajen malaminba saboda tsantsar tashin hankalin data ke ciki wujiga wujiga ta dawo ba ita ta shigo gidan ba sai bayan sallar Isha dan lokacin Baffa yana massalaci Amina tana d’akinta tana sallah, dan haka duk basu san da dawowar taba.

Tayi kuka kuka dana sani da nadama mara amfani domin bakin alk’alami yariga ya bushe Saida tayi jinya saboda tsabar bak’in ciki tareda cin alwashi iri daban daban duk akan abinda ita tajawa kanta 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button