BA JINI NA BA CE Page 11 to 20

Wani d’an iskan kallo ta watsa mata tace “amma k’awata basiranki ya gude ne ko?kirasa yar da zakice na karb’a na raina da hannayena masu albarka”
“Hum k’awata kenan inbaki saniba ki sani rainon wannan yar shine zai baki duk wani abu da kike nema kuma ta hakane zaki cimma burinki akanta sannan zokiji” tajawo tayi mata rad’a, bushewa sukayi da dariya suka tafa sun jima suna kulle kullensu kafin su sallami juna.
Haka Maryam taci gabada samun kulawa daga ta ko wane fanni kamar yadda Nanne ta buk’ata haka dole Ammey ta cire kunya take kula da yarinyar ta domin ta kula abokiyar zamanta ba irin wannan matan bane da suke son jan d’an wani jikinsu.
Sai dai abinda yai masifar d’aga hankalin Amina shine sanda Maryam ta isa yaye kawai tace ita Maryam takeso abata tunda ita an tabbatar da bazata k’ara haihuwa ba, ita kuma Amina yanzune ma ta soma Kuma babu wanda yasan iyaka ci sai Allah dan Allah ya rok’ar mata ita ta temaka tayi mata wannan sadaukarwar.
Wani irin masifaffen tashin hankali ne yakawowa ziciyarta farmaki take tafashe da wani fitinannen kuka mai mugun k’arfi wanda yasa duk suka maida hankalinsu kanta yayin da Baffa yake dubanta da masifar mamaki Sailuba kuwa wani b’oyayyen murmushi take saki azahiri Kuma hawayene yake ta rige rigen fitowa daga idanunta ta bala in kalar tausayi ta taso ta durk’usa agabanta tareda rik’o hannayenta tana wani irin kuka mai cin rai tace.
“Dan girman Allah badan halina ba dan soyayyar da kikewa annabinmu muhammadur rasulillah (S A W) ki taimaka kiyimin wannan sadaukarwar na miki alk’awarin Maryam bazata tab’a sanin zafin cewa bata tareda mahaifiyar taba zan rik’eta da gaskiya da Amana zan kula da ita fiye da yadda bakiyi tunaniba kiyimin wannan temakon ‘yar uwata” ta k’arashe tareda zubowar wasu hawayen Mai uban yawa.
Wani irin tausayin tane ya rufe Baffa yasawa ransa Koda wannan ce kad’ai kwansa a duniya ya baiwa Sailuba ita halak malak ko ba komai Sailuba ‘yar uwarsa ce jininsa Koda baya raye ita mai rik’e masa ‘yarsa ne.
Ta ko Amina wani mugun kallo ta watsawa Amina kuma tasaki wani mugun tsaki mai k’arfin gaske tace”Allah ya baki naki kema maman Maryam shine sunan data rad’a mata tun bayan haihuwar Maryam amma kisani kome zai faru bazan iya baki ‘yata ba domin wannan ai zakunci ne ace an rabani da d’iyata wannan sam bazai yiyuba wallahi” ta k’arashe tana kuka bil hak’k’i domin yanayin kallon dataga Baffa yana mata shi yake nuna jin d’acin kalamanta, batareda ya k’ara duban inda takeba yacewa Sailuba
“Karki damu insha Allahu babu wani abu dazaki nema kirasa shi matuk’ar yayanki Baffa yana raye dan haka bazakiyi kuka rayuwarkiba” daga haka ya tashi ya d’auko Maryam dake d’akin uwarta tana baccinta hankali kwance ya dawo inda suke har lokacin Sailuba bata bar kukan datake ba yace.
“Gata nan na baki amanar ta ki kulamin da ita karki bari wani abun yasameta Kinga itake nan abinda Allah ya mallakamin a halin yanzu wannan kyautar ba kowa Allah yakewa irintaba nasan ko babu raina ke mai rik’e min ‘yatane dan haka bana so kisawa ranki cewa bake Kika haifi Maryam ba haka banaso tasan cewa bakece mahaifiyar taba”
Cikin wata irin razananniyar k’ara Amina ta sulale awajen ta fad’o k’asa sumammiya take suka yo kanta cikin tashin hankali suna jijjigata Baffa ne ya tashi da sauri ya kawo ruwa suka shafa mata take ta kawo ajiyan zuciya, zumbur ta mik’e tana wani irin kuka mai cin rai d’akinta ta shige da gudu yayin da Sailuba ta kalleshi tace ” Baffa ko mu maida mata da ‘yarta kar wani abun Kuma yazo yana dasamun jifa abinda takeyi”
“Karki damu zata rage kinsan dole ne taji babu dad’i ace ‘yarta guda d’aya tak an kyautar wanda bamu da tabbacin cewa tana da wani Kwan takakke bayan wannan musamman idan Kika duba irin yadda ta ringa samun cikin yana zubewa”
Ita ko Amina tana shiga d’akinta ta fad’a saman gado tana wani irin masifaffen kuka mai matuk’ar cin rai tasawa ranta kome zai faru wallahi bazata bawa wannan matar yar taba matar da bataso zuwan yarinyar duniyaba duk wani irin tuggu da ta dinga had’a mata wanda ya dinga sanadin zubewar gudan JININTA tana sane mutumin kuwa da baya son ganin kwanka sanyin idaniyarta a duniya ai baka da mak’iyi sama dashi mayafinta ta zara kawai ta fice agidan tana kallonsu har lokacin suna dining Baffa yana rarrashin Sailuba datace zata dawo mata da yarta.
Kai tsaye gidan su ta nufa tsabar rud’anin data shiga bai barta ta kula da malam dake zaune saman dakalin k’ofa ba ta shige d’akin Nanne wace fitowar ta kenan a wanka tana shirin zuwa duba surukar shamsiyya wacce ta sha ciwo Umma taje ta sake zuwa ita sai yau Allah ya nufa dake a tsarin malam baya yarda su fita rana d’aya sai dai d’aya taje d’aya ta jira.
Tagama zura hijabinta Kennan juyowar da zatayi taji fad’owa Amina jikinta tana wani irin mugun kuka mai masifar cin rai, take jikinta ya kama rawa ta rik’e ta da kyau tana tambayarta ta abinda ya same ta cikin tashin hankali domin tasan duk abinda yasaka Amina kuka to lallai abin yakai intaha.
Amina ta kwashe duk yadda sukayi da su Baffa ta fad’a mata cikin kuka ta k’ara da cewa ‘Kuma Baffa yace ko kallon yarinyar kar na K’ara you amatsayin ‘yata.
Wani fitinannen kallo Nanne ta kafe Amina dashi yayin da ziciyarta yake wani irin tasa tace
Taku ce maman Islam
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
????BA JINANA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 13
“Yanzun shi Baffan ne ya d’auke ‘yar yabawa kishiyarki akan me shi ya haifa Miki yar ko su sukayi Miki rainon da nak’udar wallahi bazai sab’uba bindiga a ruwa” sosai Nanne ta hau fad’a ta inda suka shiga bata nan suke fitaba sosai ranta yai azabar b’aci ganin fad’an bazai fisshe taba ta finciki hannun Amina tana fad’in”zo muje gidan dole su baki yarki haka akeyin kyauta da abun wani mugunta”
Tana bud’e labulan suka gabza karo da malam dayagama jin komai tayi saurin ja baya tana had’e rai danma kar ya dakatar da ita dan daga kallon irin kallon dayake binta dashi tasan cewa yagama jin komai ” muje ciki ko?”
Shine kawai abinda malam yace yana rab’a gefenta ya wuce had’e rai ta k’ara yi tana hararan bayan sa sai dai babu ikon musu dashi dan tun farko basu sabar Masa da hakan ba.
Waje ya samu ya zauna saman kujera mazaunin mutum d’aya yayin da Amina ta zauna agabansa ta sunkuyar dakanta k’asa ita Kuma Nanne ta zauna gefen gado fuskar nan babu alamun annuri ta masifar cin magani dan ma kar malam yace zai hanata zuwa d’aukar ma ‘yarta mataki.
Gane take takenta ne yasa malam sakin murmushi yace “Zahra kenan Zahra’u manya Zahra’u sarkin rikici dan Allah Zahra in kin girma kisan kin girma inbanda abinki ina ruwanki da harkar yara ‘yar nanfa tasace yana da iko akanta dan me Zaki goyi bayan rashin gaskiya to ban amince Miki zuwa ki zubar min da kima a inda nake da Martaba da daraja dan haka na kashe wannan maganar ke Kuma” ya fad’a yana nuna Amina karna sake hanin kinsa k’afa kin baro d’akin ki akan wani dalili mara tushe ‘ya dai tasace Kuma yayi abinda yake so da ita ace danme kar naji kar na gani kinji ko” sosai malam ya rik’a yi musu nasiha har zuwa sanda yai shiru Nanne ta sauke ajiyar zuciyata tace “nifa malam bawai ina goyon bayan Amina bane saboda anbama kishiyarta yarta ba domin da ace suna zaune lafiyane to da hakan mu kanmu saiyafi Mana dad’i amma kishiyarta muguwar makirace datasan kan kissa ta mugunta” nan Nanne ta rik’a bawa malam irin labarin da shamsiyya ta fad’a mata da irin bautuwar da Amina take a siyasance a hannun Sailuba.