BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 11 to 20

Ajiyar zuciya malam ya sauke yace “karku damu domin komai na Allah ne Kuma duk abinda yake damuwa hukuncin Allah ne dan haka kusa aranku duk abinda zai samu mamana daga Allah ne domin babu wani abu dayake samun bawa face da sanin Allah”

Sosai nanma ya kwantar musu da hankali sannan yayima Amina nasiha da hak’uri a duk halin data tsinci kanta hak’ik’a Allah baya barci, yace Nanne taje ta rakata Kennan Baffa yayi sallama’ bayan sun gaisa da malam kafin yace komai malam ya soma bashi hak’uri abisa shirmen Amina har Saida kunya ya kama Baffa ya dinga sunne Kai yana dad’a bawa malam sannan yace adad’a bawa Amina hak’uri domin ansan anyi mata ba daidai ba amma yayi hakanne dan samun had’in kansu.

Malam yace babu komai Allah yabada wasu masu albarka.

Tunda suka dawo gida Amina tayi masifar d’auke kanta daga garesu ta daina kulasu duk wani aikin gidan ta ajeshi tsakanin ta dasu sai ido hatta kicin na falonta take shiga, sosai hakan yake sosa ran Baffa shi da kanshi yasan cewa basu kyauta mata ba sun nuna son ransu kuma zata na ganin cewa dan Sailuba ‘yar uwarsa ce shiyasa ta nuna son Kai acikin al’amarin.

Da k’yar yasamu yasha kanta suka koma dai dai haka ma mama kamar yadda ta rad’a wa sailuba suka koma daidai amma Kuma bata Kara yarda tayi mata wannan uwar bautar ba.

Wata irin sangartacciyar rayuwa aka koya Maryam wani irin mugun gata ake gwada mata wanda babu wanda ta ragawa rashin kunya wa kowa sai anyi magana Sailuba tace ai yarinyace haka rayuwa taci gaba da tafiya an mugun tab’ara Maryam duk girman mutum bai wuce ta zageshiba.

Koda Nanne ta kula da yadda Amina ta watsar da Maryam da al amuranta fad’a ta Mata tace yau idan akace Maryam ta lalace kafin kowa yaji ciwon haka kece zakiji domin kece kika san zafinta ita adirenta ta ganta dan haka ita hakan bazai tab’a damunta ba domin batasan ciwontaba haka Nanne tayi ta mata maganganu tare da nuna mata illar kawar da kanta da tayi daga kan Maryam.

To Kuma duk yadda taso Jan yarta ajiki tareda nusar da ita hakan ya faskara see domin Sailuba ta wuce tunanin mai tunani akan komai musamman ta fannin makirci ta kware fiye da zaton me karatu.

Haka rayuwarta yacigaba a tab’arb’are babu kwab’a babu harara duk abinda take so shi ake mata a ta gefe guda kuma tun bayan da ta Kuma haifar yara maza guda biyu duk basu zo da raiba bata sake Koda b’atan wataba sosai abin ya dameta ga matsalar Maryam da Allah yayita da fitinar tsiya ga shegen rashin kunya ga d’an banzan tsokana abin ya masifar damunta amma sai takema yarta addu ar Allah ya shirya.

A b’angaren Sailuba kuwa tunda taga daga Kan wannan yara anja kusan shekara bakwai Amina bata k’ara Koda b’atan wataba hakan ba k’aramin faranta ranta yayiba dan haka ta watsar da duk wani nema da take akanta ta maida dukan wani asirinta akan iya Baffa shi kad’ai riba biyu ga Baffan ta ga Kuma Maryam data b’atar da duk wata hanya da zata gane cewa Amina ce mahaifiyar ta.

Lokacin da MD ya dawo ya tarar da irin tab’arb’are war da rayuwar Maryam yayi ga fitsara ga raini wa kowa ba k’aramin tashi hankalinsa yayiba ya dinga bin Ammey yana fad’an bata kyautaba databar rayiwar Maryam awajen wacce batasan ciwon haihuwaba amma sam Ammey tak,’i kula hakan tama daina sauraron say domin tasan cewa kotayi magana babu abinda hakan zai haifar sai fitina Kuma tun wataran da taga abin yana yawa tayi ma yarinyar fad’a ta zageta ta kuwa kamata ta zane ai kuwa ranar taga ruwan bala I a wajen Baffa dan rufe ido yayi ya tujareta har da mata iyaka da yarta abin ya k’ona mata rai sosai har Saida tayi zazzab’i saboda bak’in ciki shi kanshi Baffa da yaga kamar bai kyautaba yasa ya dinga rarrashin ta daga baya.

Da farko MD yaso jan Maryam ajiki amma Sailuba bata bada damar hakan ba domin da kanta ta dinga tusa tsanar Muhammad a zuciyar Maryam har taji duk duniya babu wanda ta tsani ta bud’a ido ta gani irinsa.

Tun yana daurewa halayyar tata har abin yafi k’arfinsa domin halin yarinyar ya wuce tunanin mai tunani, hakan yasa yai masifar tsanar wannan mugun halin nata yarinyar da ya ginu da tunanin yadda zai jata jikinsa ya gwada mata Koda gutsuren k’aunar da mahaifinta yake nuna masa amma ina makircin uwar rik’onta bazai bari hakan ya faruba.

Sanda Maryam ta cika shekara goma dai dai Amina ta Kuma haifo yaronta katon gaske sak Maryam har yaso yafi Maryam fari da manyan idanu, wannan haihuwa ba k’aramin gigita tunanin haj. Sailuba yayiba domin ta rigada tagama sawa ranta cewa Amina tagama haihuwa ita da k’ara haihuwa har abada, kamar yadda sabon bokan da suka sake ya fad’a Mata.

Tun kafin suna take tunanin hanyar dazata b’ullowa wannan yaron dan bata tab’a jin abinda ta tsana sama da wannan yaron ba duk iya yanda taso had a makircin ta akan yaron idanun Baffa ya rufe abinda ya k’ara d’aga hankalin Sailuba yadda atake Baffa yayiwa Amina kyautar wani kat’on gidansa na G R A sannan Kuma yaron wanda yayima hud’uba da Abdul Nassar yabashi companyns na takalma company data gama cin buri akai tagama tsara duk yadda zata yi ace anbarwa Maryam shine yau ake bama wani banza da uwar banzan lallai Baffa ya tarowa kansa

Ba k’aramin murna MD yai da haihuwar Abdul Nassar ba dan ko ba komai yasamu aboki duk da kasancewar sa mutum mara son hayaniya hakan bai hana sunyi wata irin shak’uwa da yaron ba.

Haka rayuwar Nassar yaci gaba da tafiya cikin tsantsar so da kulawar Ammey sa da Kuma bross d’in sa kamar yadda Baffa yasa su dinga fad’a masa.

Sosai Nassar yataso yaga yadda akema uwarsa cin mutunci a fakaici shima ya kuwa yace baisan wannan ba dan haka duk abinda akasa Maryam taiwa Ammey sai ya rama akan Mama tun suna had’uwa suyi ma yaron duka har zuwa lokacin da Maryam din ta fara rage wasu abubuwan domin daga yanayin yadda Ammey take tafiyar da al amuranta yasa ta gano nagarta da kyaun halin Ammey yasa ta sassauta mata duk da cewa ba wai ta dena dukabane.

Haka dai rayuwar yacigaba yayin da agefe guda MD yakasa jurewa fitsaran Maryam yasa duk abinda Masa yake kamata yayi Mata d’an banzan duka tun tana zaginsa idan ya daketa har azaba yasa ta daina sai dai tayi ta fad’a masa bak’ak’en magan ganu shima Kuma sai ta tabbatar databa da tazara mai yawa atsakaninsu ga wani tsinannen d’abi a da aka koya Mata na yawon club wanda mama takance tayi komai ba komai ubanta ya tara mata 

Hakanne yasa Maryam take abinda taga dama kud’i kuwa ko nawa take buk’ata za a bata batare da bin ba asin abinda tayi daauba Kuma Koda an bata yanzun anjima ta buk’ata wanda suka fisu Bata za ai batare da wani bin diddigiba.

Hakanne yasa Ammey dauk’e kanta akansu har zuwa yanzun da Maryam ta fara jan d’an uwanta ajiki ta dai ce aun daina fad’a to bari mu gani da gaske ne ko Kuma wani shirin ne Maryam da uwarta suka Kuma yowa

Muje zuwa

Daga taku

Maman Islam

بسم الله الرحمن الر حيم

*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

   FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*________________________????BA JININA BACE????

2021

                NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button