BA JINI NA BA CE Page 11 to 20

MAMAN ISLAM
Page 14
Cigaba
Suna shiga d’akinta Nassar yace “Adda ni nafasa game muje muyi kwallo kawai, kawai ko muyi basket kallonsa ta d’anyi tace “a a nak’i wayon saboda kasan kafini kwarewa anan ko” yace “to naji buga game d’in Allah yabawa mai rabo sa a”
“Hello k’awata akwai matsala fa wallahi ina cikin damuwa”ta d’aya b’arin haj. Zakiyya tace “mun shigesu wane irin matsala Kuma kinsanfa bana juran irin wannan k’ananun zantukan yanzun sai kisa cikina ya murd’a”
“Hmmm kedai bari k’awata wannan tsinanniyar matar Saida tasan yadda tayi ma Maryam asirin da gashi tana neman sawa Maryam tafi k’arfi na zokiga yadda take wani jan wannan shegen yaron ajiki wallahi karkiji zuciya na”
Itama Zakiyyan ajiyar zuciya ta sauke idan bata manta aikinsu na farko ba bokan ya tabbatar musu da cewa ba ko yaushe ne suke da nasara ba dole wani lokacin a jarrabisu da rashin nasara dan matar atsaye take itama bata sanya wajen addu a sannan babanta ma tsohon mugun matsafine” kujifa?
Sosai suka shiga neman mafita wanda daga k’arshe dole suka yanke komawa wajen tsohon bokan da suka daina zuwa tun tuni.
Maryam kuwa suna d’akin har lokacin suna buga wasa da Abdul sai rinto take masa da ya cinye saita ce ba hakaba tun yana hak’ura har shima yai zuciya ya tashi ta dubeshi “ina zaka?”
“Wallahi na daina wasan sai na cinye saikice ke baki yardaba kuma ke kike min rinto nadaina shike nan” yafad’a kamar zaiyi kuka tace “to shikenan k’anina zokaji wani abu” ya rank’wafo kamar zaijin ya kuwa d’auke wayarta daya gama fakonta ya haddace password d’inta, ai kuwa ya zuba da gudu ko takan Baffa da Ammey da har lokacin suke dining bai biba ya arce waje, can saiga Maryam d’in ta biyoshi tana fad’in “wallahi inbaka bani wayana ba saina fasa baka wannan abinda nace” ganin har ya fita itama tabishi da gudu yayin da iyayen suka bisu da kallo cikin sanyin rai.
Da gudu ya shige lambu itama ta rufa masa baya sam idanunta bai kula da dutsen ba sai data taka santsi ya d’ebe ta tafi zata fad’i tasaki k’aran firgita jinta ajikin mutum yasata sakin wani irin ajiyar zuciya.
MD wanda tun shigowar Abdul da gudu ya dawo daga duniyan tunanin daya tafi ganin Maryam ta biyoshi tana hayaniyan data saba indai antab’ota yasa ya maida hankalinsa kansu baisan ya akayi ya isota lokacin datayi sufa zata fad’iba shidai kawai yaganta ne kwance saman kirjinsa Maryam wacce sai lokacin ta bud’e idanunta ganin jikin wanda take tayi saurin tashi tare da sakin wani d’an uban tsaki, abinda yafi tsana a rayuwarsa ya fincikota da mugunta ta Kuma fad’owa jikinsa Saida tasaki k’ara saboda bigewan datayi da gwaiwar hannunsa, cikin b’acin rai yace “dawa kike? ni sa ankine da zakimin tsaki?”
Dubansa tayi taga har idanunsa ya sauya tasani Sarai idan tashiga hannunsa bazataji da sauk’i ba d’auke kanta tayi tana hararan gefe tace “ni ai ba dakai na keba da wancen nake” ta fad’a tana nuna dutsen daya tad’eta, duk da yanayin dayake ciki sai da abin yaao dariya yadan murmusa ya tun kud’eta daga daga jikinsa sai data kai k’asa ta na tashi kuwa ta galla masa harara da murgud’a baki tace dakai nakeyi me ka isa yimin yi yayi kamar zai kamota ta taka da gudu ta wuce cikin gidan.
Da yamma suka fito domin zuwa gidan malam gaba d’aya har Baffa wannan k’aida ne idan ya dawo sai yajema malam tare da dumbin alkhairansa mai tarin yawa.
Bayan sun gama gaisawa da malam Amina da Nassar sukayi cikin gidan yayin da Baffa ya tsaya anan suke dad’a gaisawa da malam anan malam yake tambayarsa ya kuwa lek’a Inna?
D’an sunkuyar da kansa k’asa yai yana sosawa cikin ladabi yace “ban Sami zuwaba har yanzu amma ina mata aike akai akai”
Malam yace “zancen banza kenan ance maka wai abin hannunka ne maganin matsalar ta karfa kamanta Kai kad’ai ne d’an da Allah yabata a duniya ina mai tabbatar maka tafi buk’atar ka akan duk wani abu da kake da Kuma Allah ne kad’ai yasan halin datake ciki akan hakan, dan haka nake umartarka daka daure kaje”
Shiru yayi cikin d’acin rai yarasa wannan masifa yarasa abinda yake damunsa shida mahaifiyarsa amma zuwa inda take ya gagaresa meke nan meyake faruwa da rayuwansa ne?
Maman Islam ce
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
????BA JINANA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 15
Sun jima sosai a wajen malam yana dad’a fad’a masa maganganu masu sanyaya jiki da karyar da zuciya sosai yaji babu dad’i shi da kanshi yana matuk’ar kewan mahaifiyarsa tsohuwar Allah ta ala amma ya kasa sauke hakkinta dayake kansa tsayin lokaci, har hawaye Saida yayi malam ya rik’a lallashinsa tareda nuna masa kuskurensa.
“Adda zo muje gidan su anty Halima dan Allah” hararansa tayi tace “bazanjeba ka manta dazu kasa Baffa ya hanani zuwa sayan kayan kwalliya Kaine kace na cika ta adin kud’i”
“Kiyi hak’uri dan Allah Adda na daina” da k’yar yasamu yasha kanta suka fito, yamma ce sosai ga uban hadari bak’i k’irin har tace su koma Nassar ya nace suka fito dai dai nan motan MD ya shigo sanye cikin kakinsa da alama ya dawo atafiya ne d’an tun ranan data k,wace suka had’u alambu basu k’ara had’uwa ba sai yau da murna Nassar yai wajensa yayin da Maryam ta d’auke kanta kamar bata gansa ba.
Kanta na k’asa batasan ganinsa, duk da kasancewar Nassar ya d’auke hankalin Shi da surutu amma dukkan motsinta yana ankare ta gefen ido yake k’are mata kallo yana mamakin yadda take da d’an Karen d’aukar Kai da mai da kai ba komaiba an riga an gama da ita ranan dayabar garin yanaji ana fad’a da ita akan ta zagi mai gadin kusa da su mama tana goyon bayanta akan wai da abin daya mata hakanan Maryam bazata zageshiba sai da dalili wannan abu ya bala in b’ata masa rai.
Sai dai masu Karin magana sunce hannunka baya rub’ewa ka kayanke ka yar dole zai koya Mata tarbiyyan da aka gaza bata tun farko amma yasani fitsara ne zaisha kala kala ita Kuma taci bak’ar wahala.
“Kira min Addanka Nassar” yafad’a cikin rashin sonaganar sa, sai da Nassar ya k’ara kallon MD dan mamakin aiken daya masa “bazaka bane” yafad’a cikin daka tsawa da gudu ya k’arasa “Adda kizo inji bross” wani banzan kallo Maryam ta watsawa Nassar kafin taja tsaki tace “ina wasa dakai ne dazaka zomin da wannan banzan sak’on?
To ka koma kace bazan”””””””””kafin tak’arasa taji d’all asaman leb’b’an ta da mugun k’arfi da sauri ta dafe bakinta tana kallon sa yadda yai bala in daure fuska saitaji wani irin shakkarsa ayau d’in, shikam k’ara tamke fuska yayi yace “wato ke maraya kunya ko kullum iskancinki k’ara gaba yake to ni d’in nan sai na gyara miki zama ke k’aramar mara kunyace wallahi kuma ku koma babu inda zaku fita da wannan hadarin”
Maryam wadda har idanunta ya fara ciki da kwalla ta juya batareda ta kalleshi ba har yana mamakin rashin mai da raddinta dan yasan hali saidata tabbatar takai tsakiya kafin ta juyo ta galla masa harara tace “kuma sai Allah yasakamin ban yafe ba” ya d’an taka kamar zai bita ta shige da gudu,