BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 11 to 20

Murmushi ya d’an sosa kansa aransa yace wannan saitata ba k’aramin aiki bane andai riga da an cuci uwarta ne an lalata Mata tarbiyyan d’iya.

Tana shiga falon taci tuntub’e da k’afar Ammey da ta mik’e tana zaune saman kujera saura kad’an ta fad’i Ammeyn ta tarota “ke lafiya kike wannan uban gudun saikace wata wacca aka biyo?”

Maimakon amsa saita fashe da kuka Ammey ta d’ago kanta saita ga lebanta a kumbure gashi har sun d’an tsatstsafo da jini “waya dakar miki baki har ya kumbure haka?”kasa bata amsa tayi sai sabon kukan data fashe da.

Nassar ne yace “wallahi Ammey bross ne ya dakar mata baki da k’arfi saikace yasami sa ansa”

Hararan Nassar Ammey tayi tace “haka nan dai bazai daketaba da abinda tayi masa inba hakaba bazai tab’a taba”

Hararan Ammey Maryam tayi sannan taja tsaki tabar wajen dama rashin kunyar ta bawai ta dainayi mata neba in babu Nassar awajen tana d’an tab’awa da kallo duka suka bita yayin ta shige d’akinsu mama tana can gidan haj. Zakiyya ta rasa tsiyar da suke k’ullawa agidan wannan haj. Zakiyyar hakanan ta tsani matar ko gidan ta zo sai maman tayi da gaske take gaidata.

Bayan wata uku 

Sakamakon jarrabawan su ya fito ba k’aramin farin cikin sakamakon Baffa yayiba haka Kuma haj. Sailuba tasa dole yasai mata mota matsayin gift d’in cinye jarrabawan datayi ko kad’an hakan baima Ammey dad’i ba amma bata da ikon magana tunda anyi mata iyaka da hakan amma kullum tana kaiwa mahalicci kukanta ba dare ba rana tana sane da cewa baya bacci tana fatan ya bimata hakkinta akan yadda ake d’ora mata rayuwar d’iya.

Haka ma muhammad baiso akaba Maryam sarkin rawar Kai motaba ta mama datake fita da itama bason ransa bane amma Baffa yace yayi hak’uri ya riga da yayi mata alk’awarin intaci jarrabawan duk abinda take so zai sai mata.

 Hakama b’angaren cigaban karatunta Baffa yace ta zab’i duk k’asar datake son yin karatu’ tace ita tace ita Dubai take so tana son gadon Baffa amma Islamic medicine sosai hakan yayiwa Baffan dad’i sai dai wannan karon Muhammad yayi nasara Dan cewa yayi k’anwarsa mace bazataje wani k’asa karatuba anan kusa dasu zatayi.

Wai Maryam batasan sanda ta fashe da wani mugun kuka ba tace “ai dama na dad’e da sanin cewa baka k’aunar mu nida mamana wai ma ina ruwanka da rayuwana ne da zakabi ka takura ka addabeni ni bana shiga huriminka amma ni duk kabi katakurawa rayuwata yadda ka tsane ni haka nima NA TSANEKA NA TSANEKA NA TSANEKA haka maganar ta yayi ta amsa kuwwa a kunnen tunda yake bai tajin maganar daya masa d’acin wannan ba sosai abin ya dake shi da sauri ya tashi da nufin binta Ammey ta dakatar dashi haka ma Baffa sukace ya k’yale ta yanzun tana cikin zafine.

Maryam bata san kukan rashi ba a rayuwarta an d’ora tane akan cewa ubanta yana da komai dan haka duk abinda take so zata samu hakan ne yasa tai masifar saka ranta da tafiya Dubai yayin da Mama take dad’a ingizata wannan dalilin yasa taji ta Kuma tsanar MD aranta fiye da yadda ta tsanesa abaya.

A b’angaren MD kuwa tunda ya koma d’akin sa maganar Baffa yake tayi masa Kai kawo “Muhammadu ka taimakemu kaja Maryam a jikinka ka rage wannan ‘yar tsamar dayake tsakaninku domin duk duniya baku da kamar junanku Kai kafi kowa sanin haka sannan in Mai k’ara jadadda maka alk’awarin d’an uwana Hassan bazai tab’a tashi a banza babkoda k’asa ta rufe idonsa babu abinda za a fasa.

Sosai abinda Maryam d’in ta masa ayau yai masifar tsaye masa arai bai tab’a jin d’acin abinda take masa irin na yau d’in ba ya jima yana Kai kawo kafin ya samu Kiran gaggawa daga office dan haka ya shirya cikin sauri ya fice

Tunda ga ranan bai k’ara had’uwa da itaba dan ko fitowa tayi ta jangoshi komawa take da gaske bata son ganinsa wani b’acin rai take tsintar kanta a ciki duk lokacin data yi arba dashi.

Shi da kanshi ya nema mata makarantar da ransa yake so sai da ya gama mata komai sai sa hannun da yazama dole ita zatayi da kanta sannan ya kawowa Baffa komai sannan yacewa Baffa indai yana gari to shine zaina kaita ya kuma d’auko ta hakan yasa hankalin Baffa ya fara kwanciya.

Maman Islam CE

بسم الله الرحمن الر حيم

*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

   FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*________________________

????BA JININA BACE????

          

2021

                NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

16

Koda Baffa yazo musu da maganar makarantar tsalle sukai suka dire kamar had’in baki sukace su indai abu daga hannun MD ya fito basa sonsa, ranan haj. Sailuba taga ruwan bala i wajen Baffa bata tab’a tunanin ya iya jaraba hakaba sannan a k’arshe yace matuk’ar tasaka Maryam ta bijirewa makarantar sai tasha mamakin sa badan tasoba ta lallab’a Maryam ranan Monday tayi shiri cikin tsananin fushi.

Cikin tashin hankali ta Kira haj. Zakiyya take fad’a mata yadda sukayi da Baffa da irin wutar daya bud’e mata abinda bai tab’a yimata ba tace “ni abinda yasa bana son kusancinta da wannan tsinannen yaron saboda” banji abinda tace mataba saijinai haj. Zakiyyar tana cewa”muci gabada shirinmu k’awata komai zai tafi yadda ya kamata itama Deedah can zataje dole ko bata so domin aikinmu yafi tafiya dai dai Kuma dole zasu zama k’awaye na irin mamakin nan ta hakanne aikinmu zaifi tafiya.

Haka dai sukaci gabada kulle kullensu wanda su kad’ai sukasan abinda suke shiryawa.

Zaune suke afalon suna d’an tab’a hira jefi jefi dan matuk’ar Baffa yana gari bazaka tab’a gane asalin halin Sailuba ba shiyasa Baffa yake ganin har tafi Amina son Maryam baisan irin wainar da ake toyawa agidansaba kuma bai tab’a ganewa ta kalan halayen yarinyar ba domin son dayake mata da kuma muguwar kisisinar haj. Sailuba bai bashi damar gane abinda take tafiyar dashi na rayuwarta ba domin ta toshe duk wata hanya da zai gane hakan da asirinta da kuma kissa.

Koda tagama shirin ta cikin wani bluen swiss mai matuk’ar kyau da tsada kasancewar ta mayyar kwalliya ba k’aramin ado ta tsarawa kantaba saikace wacce zata gidan biki.

Kanta tsaye b’angaren Baffan ta wuce dan har yagama shirinsa yau zai koma wannan karon China ya nufa dan shigo da wasu kaya dan haka shima cikin shiri tasame shi, ta d’an had’e rai tace “Baffa ina kwana?”

“Kin tashi lafiya merona?”

“Lafiya tace ganin shi cikin shiri tace Baffa tafiya zakayine?”

“Eh Maryam Kinga wannan karon na dad’e dayawa ga kayan dana zo dasu saura kad’an dan haka daga China zan wuce Dubai dan shigo da sauran kayan harda dogayen rigunan dana tab’a kawo miki to suma na d’an gwadasu suma naga sun tafi har ana ta cigiyarsu dan haka suma zan siyosu” sosai hakan yaima Maryam dad’i arai sai dai wannan karon bata nuna rawan kantaba tace “Allah ya k’ara bud’i da d’aukaka Allah ya kare mana ku Baffa daga dukkan abin ki dan fiyayyen halitta amen”

Sosai Maryam ta d’auko wasu daga hallayar mahaifiyar ta na yaba kyauta duk kankantar abu da kuma kyauta ga duk wanda take tareda dashi sannan bata da k’yamar wanda take ganin tafishi ko natane wannan halayyar yana matuk’ar burgesa.

“Baffa ya maganar motana kaga yau zan fara zuwa school Kuma bani da ko sisi a account d’ina mama ta rance bansan abinda mama take da kudiba ita bata ajiyeba kuma bata barni na ajiyeba saikace mai caca”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button