BA JINI NA BA CE Page 11 to 20

Sosai maganar ta yabawa Baffa dariya yace karki damu my dear zan bud’e miki sabon account komai da komai da sunana ATM kawai Zaki amsa duk sanda kikaso ciran kud’in sannan yanzun zan miki transfer dubu d’ari biyar sai ki kiyi amfani dashi kafin na dawo motarki kuma so nake ni da kaina na zab’o miki mai kyau da tsada” tace “Baffa ni kaga kalar da nake so ta fad’a” tana nuna masa fuskar wayarta zaro ido Baffa yayi sannan yace “wannan kikeso MAMAN malam tab’ wannan koni bazan iya lale million 25 nasai mota dan fariyaba anayi wutar duniya Maryam nasai miki ta 5 million inba hakaba sai dai ki hak’ura wallahi”
Ganin bazatayi nasaraba tace to Baffa amma kud’in dakace zaka zuba min yayi kad’an kaga wancan karonma kafin ka dawo har na dawo abin tausayi”
“Naji zan k’ara Miki d’ari biyu akai” tace “na gode Allah ya tsare mana kai kaje lafiya ka dawo lafiya”
“Amen ya Allah dota” daga hakan Baffa ya sallameta bayan ya bata dubu dari a hannunta kafinma ta k’araso ta b’oyesu ajakar ta har sanda ta sakko suna falon ta d’an kalli mama tace “mama bani kud’in makaranta zan wuce”
Maman ta d’an dubeta tace”Baffa bai baki bane?”
“Ya bani sun min kad’an”
“Je cikin jakana inajin baza a rasa canjiba” da sauri ta shige d’akin ta fito tana k’irga kud’in, sannan ta dubi maman tace “mamana na d’auka duka dubu ashirin da biyar ne” jin abinda tace sai da Ammey ta d’ago ta dubeta suka had’a ido ta kuwa galla mata harara ta d’auke kanta, mama tace “to Maryam ki kula da kanki kiyi abinda yakaiki domin babu mamaki ya kasance wannan shine zai kasance gatanki anan gaba”
“Ban gane me kikeson ceminba mama banason irim wannan maganan dan Allah mama”
Irin wannan maganan ya zama dole Maryam domin da sannu zaki iya rasa wani abu mai muhimmanci arayuwarki ko mu ko dukiyar ko dukanmu”
Yanzun ba iya Maryam ce take kalloan maman tata ba harda haj. Amina dataji gabanta ya tsinke take ta hau karanto hasbinnallahu aranta yayin da Maryam tabar gidan cikin sanyin jiki.
A jikin mota ta hango MD sanye cikin kakinsa da alama shima daganan office zai wuce ganin yadda yai masifar had’e rai sai da gabanta ya fad’i amma dake itama jan wuya ce sai ta had’e nata ran tak’arasa zata bud’e bayan motar tsawan daya buga mata yasa batasan lokacin data bud’e gaban ba sai tsintan kanta tayi kawai a zaune jikinta na rawa.
Sai da ya daidata zamansa sannan ya dubeta yace “ke baki iya gaida mutane bako, ita mahaukaciyar ‘yar rainon naki bata koya miki girmama manya bane?”
D’auke kanta tayi gefe tana k’unk’uni tare da hararan waje ya wani fincikota da k’arfi har Saida kanta ya bugu da gwaiwar hannunsa “me kike cewa ina wasa dake ne ko?”
Shiru tayi batare data tankasa saima hawayen daya ciko mata abinda tunda yake da Maryam bai tab’a ganina, karaya a tare da ita lallai duk abinda yasanya ta a wannan yanayin ba dan k’aramin abu bane.
Tunda yaga haka sai ya fasa hukuntatan ya tunkud’eta ta koma mazaunin ta ko kallonsa bata kumayiba har suka Isa makarantar ya fito itama ta fito har lokacin jikinta a sanyaye duk da rashin jinta sai yaji tausayin ta ak’asan ranshi amma Koda wasa bai bari hakan ya nuna akan fuskar Saba, har ta juya ya kirata ga mamakinsa saiyaga ta dawo ta tsaya a kusa dashi sosai yasan cewa da abinda yake damunta domin ya jima da sanin cewa indai tana cikin yanayin damuwa to ita d’in rak’umi da akalace sai yadda kayi da ita.
Dubu biyar yabata kamar bazata karb’a ba sai Kuma ta karb’a batareda ko kallon inda yake ba bare yasa ran zata gode tayi gaba abinta murmushi kawai yayi yabi bayanta suka jera yayin da idanu sukayi kansu duk inda suka gifta sai an kallesu an k’ara saboda tsabar kyau da kwarjinin su.
Sai da ya rakata ta gama komai kafin ya karb’i wayarta zaro ido tayi tana kallonsa nombobinsa ya saka ya kira ya d’auki nata daga haka ya mik’a mata wayanta yace “Allah yabada sa a”
Har ya shige motarsa tana tsaye tana kallonsa yana shiga ya juyo ganin tana wajen harara ya galla mata kafin yaja motar yabar wajen ajiyar zuciya tasaki tana juyowa wata matashiyar budurwa wacce batafi sa artaba tana tana k’arasowa inda take, tayi tareda mik’a Mata hannu sukayi musabaha tace “ni sunana Maryam Abdullah Abubakar kefa?”
Zaro ido Maryam tayi tana kallonta kafin tasaki wani k’asaitaccen murmushi tace “ni Kuma sunana Maryam Baffa Abubakar” itama Maryam kallonta tayi da mamaki tace mata” badai Baffa Abubakar mai gidajen mai ba?” Jinjina mata kai Maryam tayi sannan tace “shine kina wane b’angaren ne?”
Tace “Islamic medicine” itama Zaro ido tayi tace ai nidake b’angaren mu d’aya tace suka tafa tareda rik’e hannun juna suna murmushi Maryam Abdullah Abubakar tace “da alama kema sabuwace ko?”
“Eh yau na fara zuwa ”
“Ni kuma jiya Kinga Ashe bani kad’ai nayi missing 2 weeks ba” Maryam tace “au ke jiyama kikazo Kennan?”
“Eh wallahi” haka dai sukayi ta hira har suka k’arasa cikin ajin.
Ranan basu hutaba daga wannan malamin ya fita wani zai shiga wuni gudana na ranan farkonta amakaranta bata da wani huta, Koda ta koma gidama agajiye take wanka kawai tayi ta fito neman abinci dan wata fitinanniyar yunwa takeji ko samun damar cin abinci basuyiba.
A dining ta had’u da Nassar shima shigowarsa Kennan dan shima nasu makarantar tun safe sai karfe shida suke dawowa shine makarantar da Maryam tagama wanda acan tayi sauka tareda sauran litattafai na addini Arabic ne da boko a had’e amma akwai mugun tsada.
Sun fara cin abincin kenan MD ya k’araso wajen sanye da kayan shan iska tree queter wando da riga mai yankakken hannu irin iya kafadan nan farare kar.
Zama yai yana opposite d’in Maryam yace “d’an zubamin abincin nima yunwa nike ji sosai” yayi hakanne ak’ak’arinsa nason janta ajiki kamar yadda Baffa ya buk’ata, kallonsa tayi da mamaki dan a saninta ko abinci yazo ci yagansu ita da mama a dining d’in ya hak’ura yau Kuma ya da ahaka sai dai ko kallonsa batayi ba taci gaba dacin abincinta.
MAMAN Islam CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
????BA JININA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 17
Kafe ta yai da manyan idanunsa yayin datai bala in d’auke kanta tayi kamar bata san da zamansa awajen ba ganin haka yasa yajanye nata abincin yafara ci shima cikin d’aure fuska.
Dagowa tayi ta dubeshi ta ko ina bataga alamar wasaba dan haka takai hannu zata d’auki ruwa shima ya dafe hannun batareda ya kalleta ba haka Kuma bai daina cin abincin saba janye hannun ta tayi ta mik’e batare data tanka Masa ba tabar wajen’ bin bayanta yayi da kallo har ta shige d’akin ta, kai tsaye toilet ta shige ta d’auro alwala tazo tagabatar da sallar magriba bayan tayi addu o i sosai sannan tafara karatun alqur ani mai girma har zuwa lokacin da aka kira sallar isha sannan ta rufe qur anin tayi ta addu o’i har zuwa sanda aka shiga masallaci tabi jam ‘i daga nan cikin d’akin ta duk abinta bata sanya da addu a sam bata da wasa a wannan fannin.
Nassar ne ya lek’o ganinta ninke sallaya ya koma da gudu tana kiransa amma bai dawo ba, can kamar wajen mintuna uku sai gashi ya sake dawowa da sallamar sa ya shigo ta d’ago tana mallonshi tace “da gulmane yasa ka lek’o ka koma kamar w””””””””””” ragowar maganar ne ya mak’ale sakamakon ganin wanda ya biyo bayansa take ta maida kallonta ga Nassar tana hararan sa murmushi ya mata tareda salute nata ya juya jin kiran da Ammey tayi dan haka ya wuce da d’an tsallensa.