BA JINI NA BA CE Page 11 to 20

Juyowa tayi asanyaye har yayiwa kansa zauni asaman kujeran gefen gadonta “k’araso ki zauna hira nazo tayaki” wani kallo ta watsa masa amma batace komaiba sai uban bugu da ziciyarta yakeyi sai kawai taci gabada gyaran kayanta data soma tunda safe batasan tashinasba sai jin hucin numfashin sa tayi daf da ita a d’an firgice ta juyo saura kadan ta fad’a jikinsa saboda yadda ya matsota kamar zai shige jikinta tana k’ok’arin janye jikinta yayi saurin dafe kafad’unta ya kafeta da idanunsa mai firgita masu kallonsa d’auke kanta tayi gefe tana tura baki tareda k’unk’uni “me kike cewa nida nazo muyi hiranmu nayaya da k’anwa shine zaki shareni ki hau aikin nasan ba dan Allah kikeyinsa ba”
Bata iya tace masa komaiba saboda kusancin dayake tsakaninsu hakan yasa takasa wani kwakwaran motsi har jikinta ya soma d’an rawa rawa, wani murmushi ne ya kwace masa ganin tsoro k’arara kwance cikin idanunta,sakinta yayi ya koma inda ya taso yace “zoki zauna labarin abinda ya faru a makaranta yau zaki bani, sannan me da me aka koya muku duk abinda baki gane ba Kuma ni zakizo ki tambaya”
Ita dai tsabar mamakinsa ya hanata tankawa domin tasani cewa duk duniya babu wacce yatsana sama da ita da mamanta gashi yanzu Kuma yazo yana wani shige mata anya ba wani muguntar yake shirya mataba Kai ita Kam tana kokwanton wannan shige matan da yake.
Shi Kam duk yadda yaso janta da hira takasa sakewa dashi saima shakkunsa dayake hangowa a kwayan idanunta amma babu komai shima duk da badason ransa yake biye matanba zai daure yaci gaba har sai yaga ta saki jiki dashi.
Washe gari da wuri tayi shiri ko Kari bata tsaya tayi ba duk a shirinta na tserewa MD bata son abinda zaina had’a dashi dan ta bala in tsanar say wallahi har cikin zuciyar ta, sai dai ta makaro domin tana fitowa ta hangoshi jikin motarsa a tsaye ga draiver agefensa shi Kuma hankalinsa yana kan wayarsa yana faman latsawa.
Har ranta taji sanyi dan tayi tunanin shi zaisa yakaita dan haka a nutsenta ta k’araso tazo d’an gefensa taja ta tsaya batareda ta tankawa kowa cikinsu ba mai gadin ma datake gaidawa yau dan karta gaida Muhammad yasa taki gaidashi, shi Kam ko ajikinsa saima mota daya bud’e mata yace shiga, babu musu ta shiga driver ya shiga ga mamakinta sai gani tayi ya zagayo tadayan b’arin ya shigo’, d’ago kai tayi da niyyar kallonsa suka had’a ido d’age mata gria yayi “ya dai?” ya yace yana kallonta d’auke kanta tayi kamar bataji me yace ba tunda suka shiga ya maida hankalinsa Kan computer yanason k’arasa wani aiki kan ya isa office.
Yau ta riga Maryam zuwa dan da wuri ta fito yau ma kamar juya 5k yabata batason dogon magana yake had’a ta dashi dan haka yauma amsa kawai tayi ta wuce yabi bayanta da kallo har ta b’acewa ganinsa ajiyan zuciya ya sauke sannan ya juya ya shiga mota driver yaja.
Tafiya take a nutsa tana tuna maganar da sukayi da mama yanzun kafin ta fito inda take ce mata”Maryam kiyi yadda kikeso kiyi abinda kikaga dama rayuwa bashi da tabbas inke kece yau gobe wanin kine abinda yake hannunka zai iya kwacewa ya koma hannun wani sannan rayuwa takan sauya mai bud’i ya koma talaka, shi kuma talaka ya koma me k’udi dan haka kiyi amfani da lokacin ki sannan kiyi amfani da damarki dan duk lokacin daya kubce miki bazaki sake samun irinsaba” sosai maganganun maman yake tsinkar Mata zuciya tabbas tafi kowa sanin halin mama bata maganan banza tunda ta dage akan wannan akwa k’arkarfan dalilinta haka nan yauma dazata fito dubu hamsin ta bata duk da wannan ba komai bane awajen maman amma tana mamakin yadda take bata kud’ad’e akai akai har dubu d’ari biyar tana bata musamman intasan tana da wani casu ko shagalin k’awayen ta’ tana tsaka da wannan tunanin wanda yai matuk’ar d’aukan hankalinta taji tayi karo da abu kafin ta d’ago dan ganin waye an d’auke ta da wani matsiyacin mari wanda yasa saida tasaki jakarta da wayarta suka tarwatse awajen amatukar fusace ta d’ago sukayi ido biyu “me na maka dazaka mareni?” tayi masa tambayar hannunta dafe da kuncin ta “ubanki Kika yimin dan uwarki hanyar ta ubankice da zaki taho kina mana rangaji har ki buge mutane”
Itama fusata tayi tace saidai ubanka dan uwarka hanyar ta inaga naka ubanne ya ginata d’an iska wawa jaki dabba kuma wallahi ina mai tabbatar maka sainaga waye ubanka ak’asar nan sanaga g”……….kafin ta k’arasa ya Kuma d’auke da wani mugun marin take jini ya balle mata ta hanci da gefen bakinta durk’ushewa tayi awajen saboda jirin daya fara kwasar ta shima tsuganawar yayi agabanta ya d’ago hab’ar ta ya kalli cikin kwayar idonta yace kije ki turo duk uban da kike tak’ama dashi”
Duk da bak’ar azabar daya gauraye mata fuska haka bai hanata “furta cewa zaka gani ina mai tabbatar maka cewa saikaga gatana wallahi zakasan ni katab’a saikayi nadamar zuwanka duniya yau” ina jira ‘yan mata ya fad’a tareda barin wajen take duk mutanen da suka cika wajen suka watse basuyi mamakin d boy ba domin takadirin d’an iska ne ya addabi kowa amakarantar gaba d’aya kowa tsoronsa yake hatta da malamai ma basu da ikon hukunta KAMAL ABBA AL HASSAN d’a d’aya tilo ga mahaifinsa alh. Abba AL HASSAN wanda yasamu dukkan dama da sake yake yadda yadda dama arayuwarsa.
Saida kowa ya watse sannan Maryam ta k’araso wajen d’ago fuskar Maryam tayi yadda taga yayi kaca kaca da jini ga gefen idonta har yayi kwanciyar jini batasan sanda ta fashe da kukaba tace “ke kuwa name sake me ya had’a ki da wannan azzalumin d boy d’in wanda bashi da mutunci ko kadan jifa yadda yadda ya mayar miki da fuska?”
Bakin ciki bai barta ta ce komaiba sai wayanta data Mik’o mata bayan ta cire code “kiramin mamana” shine kawai abinda Maryam ta iya cewa daga haka ta yanke jiki awajen ta fad’i a sume, take Maryam ta Kuma rud’ewa jikinta ya kama rawa garin ta kira mata maman ta dannan no MD wanda yai save da MY LOVELY BROSS yayi hakanne dan tsokana sai akayi rashin sa a ko dubawa ma batayi ba.
Shiganea office kenan babu dad’ewa kiran yashigo saida yai matuk’ar mamakin ganin kiran nata domin yasan ba k’aramin abune zai saka Maryam kiransa zaima iya cewa tunda suke da ita bata tab’a kiransa ba, kamar kada ya d’aga sai Kuma yace baisan dalilin kiranba bari ya d’aga yaji ko wani abunne.
Memakon muryanta muryan wata daban yaji tana kora Masa abinda ya faru cikin tsantsar tashin hankali ransa ne yai wani irin mummunan b’aci take jijiyar kansa tayi wani irin rud’u rud’u tsabar azabar fushi mik’e wa yayi a fusace yana kiran waya yai waje ko takan driver bai biba ya figi motar da mugun gudu yayin dayai magana cikin d’acin rai ta waya.
Cikin kankanin lokaci ya isa makarantar har lokacin tana jikin Maryam tana faman girgizata yayinda mutanen da suka dad’a dawowa ganin Maryam ta sume wasu na bada shawarar akaita asbiti wasu na fad’in akaita gida tunda ansa mata ruwa a fuska bata farko ba.
Cikin takun izza da isa ya k’araso wajen fuskar nan tasa babu d’igon rahama ya k’araso mutane suna ganinsa sanye da kaki tare da rubutun matsayin sa ajikin wannan d’an k’arfen da suke rubuta matsayin mutum ajiki an rubuta LIEUTANANT GANERAL MUHAMMAD BAFFA ABUBAKAR kafin kice me mutanan sun watsa, bai tsaya bin ba asiba ya sab’i ‘yar uwarsa Maryam ta rufa masa baya.