BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 11 to 20

Daga taku har kullum MAMAN Islam CE

بسم الله الرحمن الر حيم

*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

   FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*________________________

????BA JININA BACE????

     2021

                   NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMANA ISLAM

Page 18

Asbiti mafi kusa ya nufa da ita ransa amasifar b’ace aransa yana ayyana irin hukuncin da zaiwa wannan yaron dan yasha alwashin saiya gane kurensa tunda ya tab’a masa ‘yar uwarsa.

Acan makaranta kuwa anfita da Maryam Kennan wani abokinsu ya k’araso wajen su d boy yace “abokina kaga yawan sojojin da sukazo suka tafi da wannan yarinyar kuwa?”

Wani banzan kallo d boy ya watsa masa “to sai me dan tasan wani daga cikin sojoji Allah yasa bakin bindiga tasani kafa riga kasan koni waye Man kaf k’asar nan mutum bai fi biyu zuwa uku ba suke da damar iya hukuntani dan haka zanci haba da yin yadda naga dama ni kad’ai ne awajen ubana kuma yatara min shegun so kaga dole na warwasa son raina”

“Kasan d’ayar wa daka kuwa?” 

“Koma ‘yar uban waye dole gobe taji tsoron bin hanyar danabi”

Man bai tsaya sauraron ba yace “yar gidan BAFFA ABUBAKAR ce fa”

Duk da cewa gabansa yayi mugun fad’uwa amma Saida yace “wane banza ne haka har girman ikonsa yakai na ABBA AL HASSAN be?” Kafin ma Man yabashi amsa moticin da suka shigo na sojoji kusan guda shida suka faka agefensu ak’alla sunkai su ashirin ko ma sama su kansu malaman makarantar tunda sukaga wannan gangamin sannan ba wani taro suke ba suka tabbatar babu lafiya.

K’arasowa sukayi inda su d boy suke wani daga cikinsu yace “waye kamal d boy anan wajen?” 

“Lafiya kuke nema na ko naci ban biyaba ne har aka yo mun gayyar masu gadi haka”

Wata irin damk’a d’aya daga cikinsu yayi masa turoshi gaban sauran da mugun k’arfi har saida yai baya zai fad’i suka wani talle masa k’eya suka cakume gefen wandansa suka jashi zuwa jikin motarsu. 

“Kunsan koni waye kukema wannan wulak’ancin? wallahi zakasan ni kuka tab’a dukanku sai kun rasa aikinku sai kunyi nadamar abinda kukayimin” duk cikinsu babu wanda ya tankashi har suka figi motocinsu da mugun gudu sukabar wajen take hayaniya ta kaure kowa da abinda yake fad’a wanda ya raina kuwa hakan ya musu mugun dad’i ko ba komai an karya alkadarin sa.

“Ba wani mummunan rauni tajiba b’acin raine yasa ta suma amma mun shawo kan matsalar sai dai gaskiya ku dunga kiyaye shigarta irin wannan b’acin ran dan zai iya jawo babbar matsala” wannan shine bayanin shine bayanin da Dr yaima MD. 

Bayan ya fito a office d’in Dr d’akin dataken ya dawo tana zaune ta jingina bayanta da d’an k’arfen gadon har lokacin bak’in cikin abinda d boy yai mata bai gama sakinta ba sannan taci alwashin saita rama Koda hakan zai haifar da ko wacce irin fitina.

Hannu kawai taji yana yawo saman fukarta tayi saurin d’ago kanta’ ganin MD tayi cikin wani irin masifaffen fushi wanda bata san yana da irinshi ba, saida yagama share mata hawayen da suke ta faman gudu sannan ya maida hannun inda yatsun d boy sukayi rud’u rud’u wajen yayi wani irin ja “me ya had’a ku da har zai kamaki yayi miki irin wannan dukan saikace wata yarsa”

Jin yanayin da yai maganar yasata d’ago ta d’an kalleshi ganin babu wani alamun wasa yasa ta kwashe duk abinda yafaru ta fad’a masa jikinsa har wani tsuma yake tsabar b’acin rai.

Mik’ar da ita yayi yabata mayafinta da takalmanta ya kama hannunta sukayi waje basu zame ko inaba sai inda yasa aka kai d boy kafin yaje yayi mugun laushi mari uku kacal yayiwa Maryam amma shi yasamu mari kala kala fiye da kala d’ari tuni kamannimsa suka sauya banda bulalar dayashi dan cewa yayi karsuyi masa dukan wasa dama yana ciki da ubansa Abba AL HASSAN wanda suke ta fafatawa dashi akan wani case da suke zarginsa.

Sanda suka shiga wajen tuni d boy ya jima da suma domin ba k’aramin jin jiki yayi ba duk da mugun haushin sa akan abinda yayi mata saida yabata tausayi ganin yanayin daya shiga balle itama mace mai matuk’ar tausayi da rauni take ta fashe masa da kuka tace ita tayafe dan Allah ya rabu da d’an mutane kar su masa illah, ganin yadda ta d’aga hankalinta yasa yace kar tadamu dama d’an gargad’i ne kawai sukayi masa dan gaba ya kiyaye yasan cewa duk matsayinsa duk abinda yake tak’ama bakowa zai tab’a ya kwana lafiya ba.

Daga nan gida ya wuce da ita lokacin haj. Sailuba ta fito haraba tanama driver magana zasu fita motansa ya ahigo sarai tasan motarsa ne yasa ta d’an dakata dan tanason masa gargad’i akan ‘yarta duk da cewa Baffa ne ya bashi dukkan dama.

Ganin Maryam ce tafara fitowa daga motar yasa tai bala in had’e rai mugun kallo ta rik’a binta dashi har ta k’araso inda take tsaye ganin irin shatin marukan dake kwance saman farar fatar fuskar ta yasa a rud’e takamo fuskar da duka hannayenta tace “baby wanne azzalumin mara imaninne yayi miki wannan d’anyen aikin, wane la’anannen ne wanda bazai gama da duniya lafiya ba, nan dai ta zage tana ta zuba ruwan rashin arzik’i duk a tunanin ta MD ne yayi mata domin dama shine yake iya mata dukan dabata isar d’aukan mataki ba sai dai ruwan tujara da rashin mutunci koda taji cewa bashi bane hakan baisa tayi shiru ba sai datayi mai isarta ranan fitar dabata samu tayiba Kennan.

Ita kanta Ammey ganin irin zaluncin da akayiwa Maryam d’in sai da taji ajikinta amma bata tankaba kamar ko yaushe idone nata amma har kullum bata fasa yiwa ‘yarta Adda a ba.

_________________________

B’angaren abokan d boy kuwa ana barin wajen dashi d’aya daga cikin abokansa ya bugawa alh. ABBA AL HASSAN waya ya sanar masa, take ransa yai masifar b’aci cikin tsawa yace”wane me zarrar ne yake da k’arfin gwaiwar kama d’ana wanene shi wane me tsautsayin ne lallai inason sanin wanene shi”

“Dad yar gidan BAFFA ABUBAKAR ya daka yau amakaranta shine yayanta ya turo aka kamashi” innalillahi,wa inna ilahi raji’un shine kawai abinda Abba AL HASSAN ya iya fad’a kafin ya zube saman sofa dake office d’in lallai yau Kamal ya janyo masa wata sabuwar masifar da baisan ta hanyar da zai magance ta.

MAMAN Islam CE

بسم الله الرحمن الر حيم

*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

   FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*________________________

????BA JININA BACE????

2021

                 NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 19

Yajima yana gabza bala e kafin ya fice daga office d’in cikin tashin hankali,kai tsaye gidansa ya nufa lokacin haj. Maimuna tana hakimce saman kujera ta d’ora kafa d’aya saman d’aya mai aikinta tana durkushe agabanta da alama wani umarnin take bata.

Tana ganin shigowarsa ta sallami mai aikin sannan “sannu da zuwa alhaji lafiya naganka tun kafin lokacin tashin yayi”

“Na gaji nagaji nagaji haba dan masifa wallahi maimuna kin haifi masifa kin haifi fitina haka kawai ina zaman zamana zai je ya d’auko min masifar da bazan iya magance taba wallahi ba ruwa d’an iskan yaro haihuwar asara t”””””””””’ dakata malam Kaine haihuwar asarar ba d’ana ba me yai maka zaka zo kasashi gaba da masifa ai duk wannan tsinannen bakin nakane yake binsa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button