BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 11 to 20

Daga nan Kuma suka nufi wajen masu saida kayan abinci A A taga Maryam ta d’auki babban buhu na shinkafa da k’arami sannan ta d’auki taliya carton biyu haka makaroni da cous cous da semonvita irin buhunnan mai guda sha biyu shima guda biyu manja man gyad’a Maggi kanshi saida ta d’auki carton guda banda sauran spacies data d’iba ita dai A A kasa daurewa tayi tace “name sake nasandai abincin gidanku trela ake kawoshi me zakiyi da wannan abin da kike ta loda?” 

“Ba damuwarki bane” cewar Maryam datakewa mai shinkafar maganan ko zasu samu motar da zai kwashe musu dukan kayan? dan adaidaita yayi musu kad’an.

“Akwai ‘yar k’ur k’ura wanda shi dama aikinsu Kennan d’iban kaya sukai maka duk inda kakeso’ ya fad’a yana kwalawa wani kira.

Tun tambayar da tayi mata tace ba damuwanta bane bata k’ara tofa nataba abinda ya Kuma d’aure mata kai shine ganin motar bai faka ko ina ba sai k’ofar gidansu da mugun mamaki ta rik’a kallon Maryam wacce ta d’auke kanta batare data bari sun had’a ido ba.

Suna tsaye har aka gama shiga da kayan abinci sannan ta sallami mai motar suka bi mai d’aukan kayan na k’arshe, shima ta sallame shi yayinda suna shiga suka tadda Umma da Abban Maryam da shima shigowarsa Kennan gidan aka fara shiga da kayan daya fara tunanin ko b’atan kai masu kai kayan sukayi amma yana ganin Maryam da Maryam sun shigo ya dingabinsu da kallo fuskarshi da alaman tambaya.

” Ku zauna mana Abba”

Maryam ta fad’a tana zaran buta tayi bayan gida, sam Maryam batada k’yamar mutane musamman inkana da tsabta dake it’s mutum ce mai tsananin tsabta da k’yamar k’azanta, tana fitowa tayi alwala tayi d’akin Umman su A A ganin haka yasa itama Maryam tayi alwalar tabita d’akin.

Tana fitowa tanemi waje ta zauna tana gaida Umma da Abban kafin ta kalli Umman tace “nifa yunwa nake ji Umma yau bross ko kari bai bari nayi agidaba wai ya makara a office”

Kallon mijin nata tayi yayin da yayi mata alamar data bata abinda suke dashi,shi kuma ya saka takalmansa yayi waje Umma Kuma ta nufi kicin ta kawowa Maryam wake da shinkafar da suka dafa da salak da tumatur da cocomber, ta aje mata ta koma domin kawo mata ruwa sai ga Abba ya shigo da ruwan roba da lemo harda dafaffen kwai tunda yasan me aka dafa agidan.

Sam bata wani nuna bak’unta ba taja abincin taci ta k’osh har tana santi ita kam Maryam zuba mata ido tayi tana kallonta batareda data iya cewa uffan ba saida ta gama ta wanko hannunta ta dawo tasha lemon da ruwa sannan tace.

“Abba wannan kayan abincin nakane kai na siyowa dan Allah Abba kada ka k’ara zuwa kayi dako insha Allah idan Baffana ya dawo zansa yabaka jari ka fara business kaima insha Allah Allah zai dafa maka”

Rasa bakin magana Abba da Umma sukayi suka rik’a kallon Maryam da tsabar mamaki dama Maryam taji sanda yake cewa saida yai dako ranan sannan ya samo musu abinda zasuci?

Sosai Abba ya gode mata sannan yayi mata fad’an abin yayi mugun yawa tace “Abba wannan ba komai bane akan idan da ace Baffana na fad’a wa shi ya doramu akan wannan tsarin nida ‘yan uwana” addu’ar da Abban Maryam ya rik’a yiwa Maryam da zuri arta harsaida yasata hawayen farin ciki itama.

Sai bayan la asar ta baro gidan ta kamo hanyar nasu gidan dake suna da tazara sosai sai yamma ta dawo maimakon Kuma ta shiga gida sai kawai ta shige gidansu MM wani class mate d’inta wanda har yau suna mutunci dashi kasancewar su unguwa d’aya.

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button