BA JINI NA BA CE Page 21 to 30

“Yau Kuma yada makara beaty malamin nan fa kinsan bashi da kirki kuma gashi saura 10 min mushiga kuma kinsan Koda 1min ya rigaki bazai bari ki ahigaba” cikin damuwa tace “ganinan besty”
“Wai kina ina need?”
“Zan fad’a Miki idan na shigo”
“To kiyi sauri dan Allah”
“Insaha Allah”
Tana kashe wayar yana k’arasowa yana duba agogon hannunsa ta wani kalleshi tayi kicin kicin da rai, murmushi ya d’an yi batare da yace komaiba ya tada motar lokacin da suka isa tuni malamin ya fara da kusan 10 yana faking tace ” maidani gida”
Kallonta yai da son k’arin bayani tayi masifar had’e rai tace “to meye amfanin barina tunda anriga an shiga kuma malamin baya barin kowa ya shiga muddun ya riga ka shiga” ta fad’a tareda zubowar hawaye sai da ya d’an kalleta na kusan 7 second kafin yama hannunta har department d’in nasu yayi sallama abakin hall d’in wanda ya lek’o ne yasa MD rik’e baki yace “kana ruwa yaro dama Kaine kake furgita mana kanne haka?”
Shima da mamakin yace “MD kana duniya gaskiya bamuda kirki zumunci yayi karanci me yafaru kake cewa ina firgita muku k’anne?” Maryam MD ya nuno masa “na d’an biya da ita office amsar wani muhimmin sak’o ina ajeta ta fashe min da kuka wai na maidata gida kariga ka shiga” dariya m Bash yayi yace
“Yarran ne koya sukaga wallenka sai su rainaka” ya fad’a yana dosar inda Maryam take yayin da MD ya biyoshi yana magana a waya.
Da sauri Maryam ta d’an russuna tace “good morning sir” ga mamakinta taji yace morning dear how fa maza wuce aji karki k’ara biyewa wannan yayanki ya makarar dake” ya fad’a bayan ya tambayi ya take batareda ya bari ta bashi amsa ba da alama yadda yai maganar akwai sanayya tsakaninsu da yayannata.
Da sauri ta doshi ajin inda ta hango Maryam tana ta faman lek’e ta window ta d’an kai mata dundu tace “me kike nema haka kamar zaki tsinka wuya tsabar lek’e?”
Ajiyar zuciya Maryam ta saki tace “ya akai yabarki kika shigo?”
“Uhm bross nefa ya makarar dani yana direni nasa masa kuka””””” nan ta kwashe yadda sukayi ta fad’a mata.
Bayan sun fito a lacca ne Maryam ta d’an dubi k’awar tata tace “besty yau ni naga masifa da tashin hankali ganin ido na,kai soja bala I ne wallahi besty”
“To yau kuma me ya had’aku keda sojan naki nasan dai dashi kike wannan maganar”
“Uhm besty wai ashe jiyan nan da muna hospital bross turowa yayi aka kama d boy karki ga yadda yasa yaransa suka mai dashi wallahi sai da nayi kuka”
“Ke banza ce wallahi besty mutum yayi miki irin wannan yarfin dan an bi miki hakkin ki shine har zai baki tausayi? bakisan d boy ba’ bakisan waye shiba wallahi da bross bai masa hakaba ya rik’a tunda yaga yayi na farko yaji dad’i haka halinsa yake”
Ajiyan zuciya ta sauke tace Allah ya kyauta,yauwa dear kikace Abba yana harkan dillancin gidaje ko?”
“Eh me yafaru?”
“Gida nake son siya besty”
” Ke kuwa besty duk yawan gidajen ku me zakiyi da wani gidan?”
“Bakiji me kikace ba beaty a maganar ki, kinsaka jimlar ku nawa ni kad’ai nakeso”
“To shikenan kamar yaushe kike buk’ata sai muje”
“Ki kira wayarsa idan da dama mu wuce daga nan idan babu damuwa tunda Kinga yanzun bamu da wata lacca”
“Yadda Kika ce besty hakan za ayi”
Daga nan direct unguwar su Maryam dake tayima Abbanta waya ya dawo yana jiransu sai da suka fara gaida mamanta kafin tayi mata iso har d’akin Abbanta sosai kwarjinin sa yaima Maryam dan daka ganshi kaga kamilin mutum mai cikar Kamala da mutuntaka bayan sun gaisa Maryam ta fita ta basu waje.
Kallonta malam Abdullah yace “yarinya me sunan kine?”
Tace “sunana Maryam Abba murmushi Abba yayi yace “d’iya tace ashe” itama murmushin ta saki wanda ya k’ara mata kyau.
“Maryam tace kina son ganina Allah yasa lafiya?”
“Eh Abba lfy dama ina son siyen gidane to shine nakema Maryam magana tace kana harkar gidaje”
Kallonta Abban Maryam yayi na d’an lokaci yana nazarinta sannan yace”ke yar waye ne ‘yata?”
“Baffa Abubakar” ta fad’a atakaice sosai ya jinjina take mamakin yadda akai tasamu k’udi ya d’auke tunda yanajin irin labarin jita jita cewa yarinyar tana mugun b’arin k’udi sannan akwaita da kyautar girma irin na mahaifinta sannan ansakar musu k’udi suyi yadda suke so, kasancewar su Kennan yaransa.
Kallonsa ya mayar kanta yace “to ‘yata kamar wanne kike buk’ata?”
Abba na baka zab’i mai kyau nake so wanda bai gaza 7 million ba” da mamaki yake kallonta kafin yace “shikenan ‘yata insha Allah zanyi miki kamar yadda zanyiwa Maryam” daga haka Maryam ta bashi dubu goma tace “Abba ga wannan ayi cefane”
Da k’yar tasamu ya karb’a dan shi d’in ba irin masu zarmewar zuciya bane.
Ba a wani dad’e ya samo mata gida mai kyau aka yi ciniki ta biya batareda sanin kowa nataba tabar komai awajen Abban aminiyar tata.
Tunda ga ranan dataganta da wasu ‘yan k’udi masu nauyi sai tasai abinda tasan duk lokacin data tashi zata siyar ta samu k’udinta.
Shin wai duk meye dalilinta nayin hakan muje zuwa daga
‘yar mutan YAKASAI
MAMAN Islam CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
????BA JININA BACE????
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 21
Haka tacigaba da karatunta cikin nutsuwa tun tana tunanin maganganun maman har tasaba ta daina saka abun aranta amma hakan baisa ta daina siyan muhimman abubuwaba aduk lokacin data ganta da wasu ‘yan k’udi masu nauyi, yayinda wani irin shak’uwa mai ban mamaki ya shiga tsakaninsu da name sake d’inta dan haka bata da aminan daya wuce Maryam da Halima.
Abangaren d boy kuwa da farko saida yaci alwashin d’aukan fansa Abban sa ya taka masa burki yace”kul dan ubanka karkaja min mutuwa kwanana basu K’are ba wannan yaron da kake ganinshi bashi da ruwan mutunci ko kadan dan iskane nake bafad’a maka nagaban kwatance dan haka ka nisanci wannan yarinyar domin ba ‘yar kowa bace face’yar Baffa Abubakar”
Saida d boy ya razana dajin abinda Abban nasa yace domin kaf yankin nasu babu wanda baisan waye Baffa Abubakar ba saboda tarin dukiyar da Allah ya hore masa da d’umin karamcin sa ga bayin Allah, sannan agefe guda yasha mamakin yadda take rok’on yayanta da ya k’yale shi haka duk da yadda ake fad’an rashin mutuncin yarinyar take yaji duk wani burinsa akan d’aukan fansa ya ruguje saima k’ok’arin son kulla alak’a da ita.
Agidan su Maryam kuwa babu abinda ya sauya sai tsarin yawon inda yanzun haj. Zakiyya ce take zaryan zuwar musu wanda idan suka shige d’aka har mantawa ake dasu dakehaj. Amina babu ruwanta da ahiga abinda babu ruwanta bata tab’a sanin wainar da suke toyawaba.
Yayin da MD ya diga ayar tambaya akan wannan ziyarar takawar wannan matar mara yankewa hakan yasa batareda da sanin kowa ba ya nemo CCTV camera saida yabari ranan sun fita gantalin bin malamansu da suka saba yasa aka jona aka saita komai tareda recording d’in duk abinda zai rik’a faruwa akaf gidan ta ko ina har d’akin Ammey batare datasan anyi hakanba.