BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 21 to 30

Rannan MD ya kawota makaranta dake sauri yake abakin get ya sauketa sannan yace idan lokacin tashinsu yayi ta fad’a masa zaisa driver ya maidata gida yau yana da wani meeting wanda sai dare yake tunanin zasu dawo k’ala batace masaba kuma dama yasan basatace d’in ba, bai jira komaiba yaja motarsa da azabar gudu yabar wajen.

A hankali tafara takawa zuwa bakin get d’in tunda tafara zuwa makarantar shekara d’aya kenan da d’an wani abun bai tab’a ajeta anan d’in ba sai yau, ta kusa kaiwa bakin k’ofar kamar yadda ta saba koda yaushe sai ya kaita har parking space na makarantar sannan zai ajeta ya juya.

“Hey hey” taji muryan wanda bazata tab’a mantawa ba arayuwarta domin shine mutum na farko da babu wanda ya tab’a yi mata irin tozarcin da yayi mata, batasan lokacin data saki wani matsiyacin tsaki ba ta juya yayin da shi kuma yayi saurin shan gabanta da motarsa, a mugun fusace ta d’ago ta watsa masa wani mugun kallo sanda yake fitowa daga cikin motar.

Yana k’arasowa bata bari ya fad’a mata wani abuba tayi saurin cewa “wai kai wane irin mutum ne mara tunani wanda baisan darajan kansaba bare na waninsa?

Yau kuma takeni kake sonyi komai?

Wai dan Allah me yasa wasu mutanen baau da tunani ne kwakwalwarsu irin na kifine?

Yo inba hakaba ni banga dalilin gamin kifi da gada ba dazaka wani zo ka shamin gaba ina cikin tafiyana idan kuma hukuncin farko ne bai ishekaba akwai wanda sukafi wannan sai ka jira.

Duk abinda take fad’a bai katsetaba saida yabari tagama maganar ta kafin yace ‘Amincin Allah yatabbata ga sarauniya kuma shugabar masu yafiya, ba wani abune yasa na tareki anan ba sai dan na k’ara neman yafiyarki abisa abinda ya faru duk da nasan cewa saboda ke wannan boss d’in yayan naki ya k’yale ni amma duk da haka ina mai kara neman afuwarki na miki alk’awarin ko kallon banza bazai k’ara had’a ni dakeba pls pls pls” ya rik’a maimaitawa yayin da tayi masifar d’auke kanta ta juya da nufin bar Masa wajen batasan ya akayiba sai kawai ganinsa tayi zube agabanta basa gwaiwoyinsa yana cigaba da rok’on yafiyar ta bai ko damu da yadda mutane suka fara taruwa awajen ba.

Zaro idanu tayi ganin yadda ya zube saman gwaiwoyinsa ga mutane da abin kallo baya musu kad’an har sun fara taruwa awajen tayi saurin cewa “meye haka dan Allah jifa har an fara taruwa anan katashi”

“Ni ba damuwana masu kallona ba damuwana kawai kice kin yafemin”

“Tashi dan Allah” ta fad’a cikin sanyin murya “zantashi ne kawai idan kince kin yafemin”

“Na yafe maka amma bisa wani sharad’i to tashi” tasake fad’a can k’asan mak’oshi da sauri ya tashi yana fad’in”na gode na gode sosai ko wane irin sharad’i ne ki fad’a na miki alk’awarin tunda dai kin yafemin” fad’a yana binta lokacin data fara takawa cikin makarantar,bayan yabawa d’aya daga cikin abokansa mukullin motarsa suna takawa a hankali yayin da ta fara ce masa.

“Gaskiya yakamata ka gyara halinka da d’abi unka ba abune me kyau ba kowa ya rik’a maka shaidar baka da mutunci babu wanda ka ragawa har akai ga matakin da kowa zai fara jin tsoronka sam wannan zalunci ne babba dan Allah ka gyara kaga ni d’innan dakake gani duk abinda kake ji dashi nafika ko ranan ma shammata na kayi banda haka bazakayi nasara akainaba sai dai ni bana shiga harkan wanda bai shiga nawaba dan haka kaga ko makarantar nan banda kawa sai A A” 

“Nasani sam ban kyautaba kuma na miki alk’awari insha Allah daga yau nima babu ruwana da sabgar kowa”

” Allah yasa” ta fad’a atakaice tana wucewa department d’insa.

Yana tsaye har ta shige murya k’asa k’asa yace “tamin Allah yasa tasoni nidai tamin badan komai ba sai dan nutsuwa da ajinta Abba kayi suruka irin wacce kake so ‘yar wani wanin ma wanda yai suna aciki da wajen k’asar nan”

(Su Kamal d boy daga sannu sarkin fawa lol????????????)

Yau kam da wuri suka koma gida dake lacca d’aya ke garesu suna gamawa babu wani jinkiri Maryam ta nemi da A A ta rakata banki tana son bud’e sabon account, da mamaki AA take dubanta kafin tace “ke kuwa name sake duk yawan asusanku wanda ba ayi miki iyaka dasuba sai kin bud’a wani?”

Bazaki gane bane sam mama bata barina da k’udi ita zata bani kuma ita zata dawo ta rance na rasa abinda mama take da k’udi duk yawan kyauta irin na Baffan mu wallahi A A Saida mama ta kureshi” haka dai suka tafi tana bata bad habits d’in mamanta wanda abin yake masifar damunta ta kuma rasa dawa zata zanta taji sanyi saifa yanzun dataji ta aminta da ita.

Har sukaje suka bud’e account kud’ad’en da Maryam ta zuba a account d’in saida abin ya bata tsoro yayin da Maryam ta dinga mata dariya daganan tace Maryam ta rakata kasuwa zatayi siyayya sai da suka fara zuwa tasiyi kayan kwalliya da turarukanta dake Maryam mayyar turarece zai wuya ka kusance takaji bata k’amshi domin ita d’in ‘yar gayuce tagaban kwatance hakan yasa take da masifar farin jini Saidai halinta bai barinta shiga sabgar mutane domin bata da kirki ko kad’an.

Daga nan Kuma suka nufi wajen masu saida kayan abinci A A taga Maryam ta d’auki babban buhu na shinkafa da k’arami sannan ta d’auki taliya carton biyu haka makaroni da cous cous da semonvita irin buhunnan mai guda sha biyu shima guda biyu manja man gyad’a Maggi kanshi saida ta d’auki carton guda banda sauran spacies data d’iba ita dai A A kasa daurewa tayi tace “name sake nasandai abincin gidanku trela ake kawoshi me zakiyi da wannan abin da kike ta loda?” 

“Ba damuwarki bane” cewar Maryam datakewa mai shinkafar maganan ko zasu samu motar da zai kwashe musu dukan kayan? dan adaidaita yayi musu kad’an.

“Akwai ‘yar k’ur k’ura wanda shi dama aikinsu Kennan d’iban kaya sukai maka duk inda kakeso’ ya fad’a yana kwalawa wani kira.

Tun tambayar da tayi mata tace ba damuwanta bane bata k’ara tofa nataba abinda ya Kuma d’aure mata kai shine ganin motar bai faka ko ina ba sai k’ofar gidansu da mugun mamaki ta rik’a kallon Maryam wacce ta d’auke kanta batare data bari sun had’a ido ba.

Suna tsaye har aka gama shiga da kayan abinci sannan ta sallami mai motar suka bi mai d’aukan kayan na k’arshe, shima ta sallame shi yayinda suna shiga suka tadda Umma da Abban Maryam da shima shigowarsa Kennan gidan aka fara shiga da kayan daya fara tunanin ko b’atan kai masu kai kayan sukayi amma yana ganin Maryam da Maryam sun shigo ya dingabinsu da kallo fuskarshi da alaman tambaya.

” Ku zauna mana Abba”

Maryam ta fad’a tana zaran buta tayi bayan gida, sam Maryam batada k’yamar mutane musamman inkana da tsabta dake it’s mutum ce mai tsananin tsabta da k’yamar k’azanta, tana fitowa tayi alwala tayi d’akin Umman su A A ganin haka yasa itama Maryam tayi alwalar tabita d’akin.

Tana fitowa tanemi waje ta zauna tana gaida Umma da Abban kafin ta kalli Umman tace “nifa yunwa nake ji Umma yau bross ko kari bai bari nayi agidaba wai ya makara a office”

Kallon mijin nata tayi yayin da yayi mata alamar data bata abinda suke dashi,shi kuma ya saka takalmansa yayi waje Umma Kuma ta nufi kicin ta kawowa Maryam wake da shinkafar da suka dafa da salak da tumatur da cocomber, ta aje mata ta koma domin kawo mata ruwa sai ga Abba ya shigo da ruwan roba da lemo harda dafaffen kwai tunda yasan me aka dafa agidan.

Sam bata wani nuna bak’unta ba taja abincin taci ta k’osh har tana santi ita kam Maryam zuba mata ido tayi tana kallonta batareda data iya cewa uffan ba saida ta gama ta wanko hannunta ta dawo tasha lemon da ruwa sannan tace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button