BA JINI NA BA CE Page 21 to 30

“Abba wannan kayan abincin nakane kai na siyowa dan Allah Abba kada ka k’ara zuwa kayi dako insha Allah idan Baffana ya dawo zansa yabaka jari ka fara business kaima insha Allah Allah zai dafa maka”
Rasa bakin magana Abba da Umma sukayi suka rik’a kallon Maryam da tsabar mamaki dama Maryam taji sanda yake cewa saida yai dako ranan sannan ya samo musu abinda zasuci?
Sosai Abba ya gode mata sannan yayi mata fad’an abin yayi mugun yawa tace “Abba wannan ba komai bane akan idan da ace Baffana na fad’a wa shi ya doramu akan wannan tsarin nida ‘yan uwana” addu’ar da Abban Maryam ya rik’a yiwa Maryam da zuri arta harsaida yasata hawayen farin ciki itama.
Sai bayan la asar ta baro gidan ta kamo hanyar nasu gidan dake suna da tazara sosai sai yamma ta dawo maimakon Kuma ta shiga gida sai kawai ta shige gidansu MM wani class mate d’inta wanda har yau suna mutunci dashi kasancewar su unguwa d’aya.
MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
???? BA JININA BACE????
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 22
Bata zauna ba data tadda jm bayanan nayi b’ata last page jm zance na manta nace mm, tana zuwa bakin get taji mai gadi yana cewa “gatanan yallab’ai” MD daya gama rud’a driver da bala i saboda kawai yace tun biyu saura su Maryam suka bar makaranta kuma alhalin ba ama turashi ba sai wajen biyar saura shine fa MD ya hana shi sakat da masifa sai da ya koma makarantar har sau biyu.
Sannan kuma Ammey ta tabbatar masa da cewa tun fitar da sukayi tare bata dawoba amma kar ya damu wannan ba komai bane a wajen su dan takan fi hakama awaje, sosai ransa ya b’aci da jin abinda Ammeyn ta fad’a masa ya fito Kennan cikin wannan halin mai gadi da ba shine driver ba da ya had’a ya hasu sakat yace ga Maryam d’in nann
Duk zubawa get d’in ido sukayi yayin da Maryam ta shigo hankalin ta kwance babu wani damuwa tattare da ita, tana tafe cikin nutsuwar da Koda yaushe ka ganta zaka ganta tattare da ita.
Ran MD ne yai mugun b’aci cikin bak’in ciki ya k’arasa inda take wato shi yana nan hankali tashe ita Kuma tana can yawon gantalin ta hankalin ta kwance’ wata irin fincika yayi Mata da mugun k’arfi har saida ta saki k’aran azaba, jakarta da wayarta sukayi nasu waje yayin tayi taga taga zata fad’i yayi saurin tareta ta fad’a jikinsa.
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke jin ta cikin jikinshi take ya ji wani irin abu ya tsarga masa tundaga tsakiyar kansa har zuwa babbar yatsarsa ta k’afa.
Ita kam Maryam wani irin takaicin jinta ajikinsa ne ya kamata batasan sanda hawaye ya sulalo mata ba saboda bak’in ciki kwace jikinta tayi daga nasa tace murya k’asa k’asa “ban yafe ba d’an iska kawai aidama Halima tace duk wanda yake irin aikinka to manemin mata ne anje neman na bariki ba asamuba shine akazo latsa k’anwa dan abin kunya tur” ta fad’a tare da fashewa da kuka.
Tunda ta juya tabar shi nan tsaye yake cikin suyar ran kalamanta tunda yake babu wanda ya tab’a fad’a masa maganar daya k’untata masa irin yau ba,amma sosai abin ya rik’a sukar k’irjinsa temakon da Allah yayi masa cikin rad’a tayi masa duk wannan wulak’ancin da cin fuskar.
Sai dai hakan baisaka yajanye alk’awarin da yayiwa Baffa da Ammey ba yayi musu alk’awarin zai ja Maryam ajikinsa yanda zasuyi sabon da duk abinda zaisa ta bazata tab’a Musa masaba ta hakane Ammey take ganin zasu samu hanyar gyarawa Maryam zama.
Bayan an idar da sallar issha suna d’akinta ita da Nassar tana tayashi assignment d’in da yazo dashi saiga sallamar shi abakin k’ofar ba k’aramin fad’uwar gaba ta tsinci kanta aciki ba d’azu bayan tagama masa fitsaran ta dawo d’akin tace sam saitaga bata kyauta masa ba kome ya mata ya kamata yaci darajan shi na d’an uwanta JININTA.
Bata samu damar amsa masa ba sai Nassar ne ya amsa masa ya k’araso gefen da take ya zauna daf da ita tanaji Nassar yana gaidashi takasa had’a ido dashi bare wani gaisuwa ya had’asu.
“Nine d’an iska mai bin mata ko?”
Ya tambaye ta cikin wani irin murya mai kashe jiki wanda hakan yasata jin wani irin babu dad’i “kayi hak’uri bross dan Allah” maganar ya kwace mata batare data shiryawa hakan ba.
Sosai ya kafeta da idonsa wanda sukayi wani irin kyalli saboda kwallan daya cikasu, tunda yake babu wanda ya tab’a gasa masa bak’ar magana irin nata.
Jin shirun yayi yawa yasa ta d’ago idanunta dake duk’e kan littafin Nassar daya jima da ficewa daga d’akin,ba k’aramin fad’uwa gabanta yayiba ganin kwallan daya ciki idanunsa sai dai bai basu damar zubowaba saboda nayasan taga logonsa amma maganar gaskiya yaji zafin maganar ta ainun wanda dama dan yaji zafin tayi masa.
Rasa yadda zatayi masa wani maganar tayi sai kawai ta fashe masa da kuka wanda zan iya kiransa da kukan shagwab’a, take ya k’arasa zaman durshen agabanta tareda kamo hannunta yace “haba k’anwarta me kuma nayi miki banfa yi miki ko mai ba” ya k’arasa maganar cikin rawar murya domin har ga Allah jiyai kukan yana mugun tab’a masa zuciya.
“Kayi hak’uri” ta k’ara fad’a masa cikin muryan kuka “nayi” yafad’a mata da sauri cikin rawan murya sannan ya d’an dubeta yace “k’anwata na miki wani tambaya mana amma ina son dan Allah ki fadamin gaskiya tsakaninki da Allah”
“To” kawai tace masa tana faman goge hawayen da suke zubo mata har lokacin “to ki daina kukan haka mana dan Allah kinji” yafad’a yana share mata hawayen data rasa dalilin k’in tsayawarsu.
“Wai me yasa kika tsaneni ne?”
Yayi mata tambayar dayafi komai ci masa rai tun ranan data furta masa ta tsanesa har yau baidaina jin amsa kuwwar abin cikin kunnen saba sosai abin ya tab’a shi.
“Ai nima baka sona nida mama ka tsanemu kafi son Nassar da Ammey kanawa mama rashin kunya agabana baka dukan Nassar agaban Ammey amma ni kamar jaka haka kake jubgata ko dan kaga Nassar d’an d’akinku shiyasa ni kake nuna min ‘yan ubanci” ta fad’a cikin zubowar sabon hawaye, maganar ta na k’arshe ya mugun bashi tausayi har baisan sanda yasa hannu yajata jikinsa ba kamar jira take kuwa ta fad’a tareda sakin kuka irin mai cin rannan.
Dagajin yanda take kukan yasan akwai abinda yake damunta wanda ta barshi aranta takasa fad’uwa kowa, saida yabari ta d’an yi kukan da d’an yawa kafin ya soma d’an bubbuga bayanta har saida yasamu tayi shru da k’yar.
“Me yasaka ki kuka?” ya tambaye ta cikin sanyin murya, “ku kullum Ammeynku tana tareda ku tana kulawa daku duk abinda kukeso tanayi muku bata yawan fita unguwa bare tabarku cikin kad’aici, amma ni kullum mamana tana gidan k’awarta haj. Zakiyya danayi magana sai tabani k’udi ko tace bari ta had’a min wani d’an party bathday d’ina kuwa ko manta date d’in batayi dan Allah bross k’udi ne yake maganin ko wane matsala?”
Ta K’are maganan da tambayar abinda yake matuk’ar damun ranta,
“A a” yabata amsa cikin tausaya mata domin shima ya fahimci wannan abun yafara damunta hakan kuma ba k’aramin dad’i yayi masa a rai ba ko babu komai tunkafin ya fara tunanin hanyar da zaibi dan shan kanta ta yadda zajata jikinsa su kulle har akai ga maganar da ake son k’ullawa wacce babu wanda yasani dagashi sai Baffa sai kuma Ammey da Baffan yake jin tana da hak’k’i akan tasan komai.