BA JINI NA BA CE Page 21 to 30

“Amma Maryam bamune muka tsaneki ba kece Kika tsanemu bakya mutantamu da Ammeynmu ko kad’an har zaginta fa kikeyi taya kike tunanin zamu mutuntaki bayan bakya mutanta mana mahaifiyar mu?”
K’are maganar dayi mata tambayar wanda nan take ta gano kuskurenta amma Kuma sai tace “ai mama tace kada nasake nayi sabo da ‘yan uba dan muddun nace zan dinga mu amalantar ku to babu abinda zaisa baku kashe niba tunda Kuna ganin agabanku Baffa yake nuna yafi k’aunata akan ku, kuma tace Ammey muguwace tun ina jaririya taso kashe mata ni kuma tace Ammey ce take asiri take had’a ta fad’a da Baffa shiyasa kullum yake mata fad’a baya bata k’udi saidai inya ajiye ta turani d’akin sa na d’ebo mata mai yawa amma baya isarta saita had’a danawa.
Tsabar tashin hankalin jin wannan mugun zantukan baisan sanda ya zube ak’asan wajen yace “maman?”
Yafad’a gamida zaro ido har saida yanayin sa ya mugun tsoratata.
Pls manage data taku har kullum
MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
????BA JININA BACE????
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Wannan shafin nakune gaba d’aya kuyi yadda kuke so
MUHAMMAD KAREEM
HAYATU BABA ZUBAIRU (YAYA HAYAT)
ITS ABBAS
Allah yabar kauna
Page 23
Jikinta take ya hau rawa tace “wa lla hi haka tace min, shi yasa kaga nima bana son Ammeynku.
Kasa magana yayi da hannunta da ya kama ya rik’e gam cikin nashi, idanunsa kuwa kad’awa su kayi suka yi wani irin ja,
Me wannan matar take nufi?
Takasa kula da amanar data dauka, Kuma tana son raba hanta da jini wannan ba adalci bane, zalunci ne babba, ke baki kula da yarinya ba, sai ma d’ora ta da kikayi akan wata turba mara b’ullewa.
“Zaki abota dani?”
Ta tsinci muryarsa cikin wani irin yanayi batasan lokacin data d’ago kai ta dubeshi ba sai dai bata iya tace masa komai ba ganin yadda ya kafeta da runannun idanunsa
“Uhm?”
Ya k’ara tambayar ta again babu amsa sai faman murza idanunta take da d’aya hannun da bai rik’e ba.
“Kema Ammey mamanki ce, ta tsinci muryar shi yana rad’a mata a kunne daga yau zamu rik’a shiga d’akin ta muna hira tare dake, kuma kema duk abinda kike so ki tambaye ta zata baki, kuma tama fi sonki damu idan kina musu ki gwada”.
Ya fad’a yana cigaba da murza hannunta dake cikin nasa.
“Mama bazata barni ba ta tsaneku” ta fad’i abinda tasan kullum maman tana tusashi agabanta, wanda tasan hakanne har cikin ranta.
“Ai bazata sani ba saboda kinga kullum bata zaman, gida Kinga kafin ta dawo munyi hiranmu, bawai ki rik’a shigowa d’aki, ke kad’ai ba, Kinga tunani sai ya miki yawa”
Ya fad’a yana kallon ta, tabbas abinda ta fad’a gaskiya ne, tunani yana damun sosai wani lokacin har sha daya mama tana kaiwa agidan hajiya zakiyya.
Shi kam zama ya gyara tareda zuba tagumi ya kafeta da idanunsa, yayin da tausayin ta ya game mai jiki,yana mai jin haushin kansa, na yadda tun farko bai jata a jikin sa ba bare har yasan damuwar ta.
“Zaki iya abota dani inzama amininki wanda zaki dinga fad’awa dukkan wani damuwar ki wanda zai dinga magance miki duk wani matsalar ki da yardan ubangiji?”.
Ya sake mata tabayan shi na farko,
“Idan mama tagan mu tare akwai matsala” ta fad’a masa haka, matsayin ta na wacce tafi kowa kusanci da mama dan haka tafi kowa sanin halinta.
“Karki damu Baffa bazai bata damar raba masa kanmu ba, kinsan burin ko wanne ubane ya ga kan yaransa ya had’u” ya fad’a yana d’ago hab’ar ta yana kallon, cikin idonta.
“Shi kenan na amince ta fad’a cikin sanyin murya”
Ihun murna ya saki tareda rungumeta”na gode my happiness na gode my Lovely sis dan Allah daga yau ki daina wannan had’e min ran baya min dad’i”
Ya fad’a mata a hankali “to” tace masa daga haka ta maida hankalinta kan aikin da suke da Nassar, tayata yayi suka gama aikin, daga haka ya rik’a janta da hira.
Waahegari motar ta ya iso, motar da Baffa yace bata gift idan taci jarrabawa, tun tana maganar motan har sai datayi fushi ta daina maganan bata san cewa mak’alewar motar daga MD bane shi ya hana saboda rawan kanta, yanzun ma sai yana yi yana sa mata ido sosai.
Washe gari kuwa tun kafin ya fito tuni ta shirya ta bar gidan a sabuwar motan ta sai da ya fito yaga Abdul Nassar yana shiga cikin motar da yake kaishi makaranta.
“Kai ina Adda?” Nassar ya tambaye shi “tab’Adda yanzun ai ta jima a schl, kasan cewa tayi bari tayi sauri ta tafi kar ka fito ka hanata kace Kai zaka kaita”.
Murmushi MD yayi Yana shafin sumar kanshi daya sha gyara, daga haka ya juya ya shiga motarsa security d’insa yaja shi suka wuce.
Uhm su o o anyi abun kai yaushe rabon duniya tunda bross ya dawo ya hanata sakat hatta motar mama da take hawa sai da ya hana ta k’arfin bala i, dan haka yau take jinta cikin wani irin farin ciki.
Tunda ta doshi cikin makarantar ido ya koma kanta domin motar tayi mugun d’aukar hankalin mutane, da yawan su basuyi mamakin ganin wacce ta fito daga motar ba domin ansan tafi k’arfin, wacce ta ninninka wannan ma, dan da yawa wasu suna mamakin yadda bata da motar kanta sai dai akawo ta.
Maryam kuwa da gudu tazo ta rungumeta tace “eye had’uwa ta iso kenan” ta fad’a tare da k’arasawa tana shafa motar, wani k’awata taccen murmushi Maryam ta saki tace “humm kinga wannan bross d’in namu sai a hankali, nasan wallahi shiya hana akawo min motar amma Baffa yafi shekara da biyan k’udinta”
Itama murmushin tasaki “ina ganin akwai wani abu tsakaninki da bross d’in nan”
“Kamar ya?
“Kamar yadda na gani bross sonki yake Maryam”
Manyan ta bata amsa
“Humm baki da hankali kin tab’a ganin inda akayi aure uba daya shifa d’an Ammey ne”
“Ammey shekarunta baikai ta haifi kamar bross dinku ba ki dai k’ara bincike”
“Humm kawai tace batare data d’auki abin serious ba.
Haka dai abubuwa suka cigaba da faruwa cikin k’aramin lokaci Maryam tayi wani mugun sabo da ‘yan gidansu batare da sanin maman taba wacce ta mik’a dukkan yarda da imaninta wajen malaman tsubbu da ‘yan bori dan haka bata da masaniyar cewa tufkar da take yi ta cikin gida ya gama warewa tas.
Wata rana kamar yadda akasaba “Zakiyya takaiwa Sailuba ziyara akan yadda suka kasa fahimtar jina ta waya,
“Nifa nagaji da wahala so nake na watsata tabi duniya ta lalace ta zama k’asaitacciyar karuwa bana buk’atar akai ga d’aura wannan auren”
“Humm Sailuba kenan wani lokacin kwwnyar ki atoshe yake wallahi, banda ke da abinki idanmma zatayi auren taya zamu bari tayi auren hutu?”
“Ni auren ne ma bana son tayi kwata kwata, so nake rayuwar ta ya wulak’anta fiye da duk wani wulak’antacce a duniya.
Tofa
Muje zuwa
Daga taku maman islam
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
????BA JININA BACE????
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Shafinki ne wannan’yar laleta SA’ADATU USMAN MUSA (ISLAM)
Allah ya rayamin ke tareda dukkan yayan musulmi badaya