BA JINI NA BA CE Page 21 to 30

Almustapha Usman Musa shalele na kenan kuma nagaban goshi Allah ya tsaremin ku.
Page 24
“Kina bani ciwon kai Sailuba nifa komai da kike gani da mugun shiri nakeyin sa, Kuma bana bawa na kusa dani damar gane akwai wani abu a cikin raina dan haka zai wuya kiga idan nayi, abu ayarda ni d’in ce nayi saboda babu fuskan da za a gane hakan, ke kuwa gajan hak’urin ki kawai ya isa tonaki, Kinga alhajina da kike ganinsa bansa me shi da sauk’i ba saboda mugun taurin Kai da Allah ya d’ora Masa, shi yasa kuma kikaga bana masa ta dad’i, domin naci bak’ar wuya kan nasame shi, sannan Kuma kina ganin har yau tak’i amincewa ta saurari Deedah shegiya mai kafirin wayon tsiya na rasa dalilin da yasa bata Sona”
Ta K’are dogon sharhin ta da k’orafin yadda Maryam take masifar d’auke mata kai ‘yar dariya haj. Sailuba tayi kafin tace” ashe kin manta da cewa nonon wannan shegiyar ‘yaalaman tasha, kai wannan mata ta zame min annoba a rayuwata nasa ta yadda zanyi maganin tsinanniya”
“Hum ai irin su idan dubunsu ya tashi cika saikin ji kamar kiyi musu kuka wallahi” cewar haj. Zakiyya cikin ya tsina fuska
Sun jima suna k’ulle k’ullensu.
Tana tunkaro gidan ta tuna da yadda bross ya rik’a kwala mata kira tanaji ta d’iba da gudu dan kar ya hanata fita, tunda suka sam d’an hutun nan ya wani sa mata ido yanzun ta lura aikin ma ba sosai yake zuwa ba sai jifa jifa damma yanzun Allah yasa ko ba kowa zata shiga d’akin Ammey suyi ta hira yadda Ammeyn take mata ne yasa ta jinjinawa k’aryar mamanta da tace Ammey muguwace ko kad’an bataga hakan ba saima wani irin mugun shak’uwa daya soma shiga tsakaninsu da Ammeyn ganin yadda take mata.
Sam ta manta da yadda ya rik’a kiranta ta gudu kanta tsaye ta shigo gidan har da yar wakar ta, daman tun fitar ta yake dakon dawowar ta.
Tana shigowa taji anyi ram da ita ya damk’e ta a bazata taji an rik’o ta sai abin yabata tsoro ta bud’e baki zatayi masa ihu yayi saurin toshe bakin da hannunsa yace “wa na kama?”
Sam ta manta da abinda ya farun dan haka ta hau rarraba ido tana neman hanyar gudu, gane hakan da yayi ne yasa yaja hannun ta zuwa Pat d’in shi.
Dan” Allah bross kayi hak’uri banjika bafa”
“To in bakiji ba taya kikasan mai ya faru wato bakijin magana ko my happiness?” ya fad’a yana kallon yadda tayi tsuruvtsuru shi wallahi dariyama take bashi, yadda duk ta koma kamar wadda ta aikata wani babban abu tun ranan da suka shirya yake kiranta da wannan sunan hakama Nassar ya daina kiranta da Adda ya koma my happiness.
Shiru tayi ba tare da ta tanka ba dan in bata ga dama ba itama wani lokacin muguwar muskila ce sai kayi ta magana tak’i tankaka.
“Kina jina ko?” Ya k’ara sanda yake bud’e k’ofar falonsa, Maryam da take shirin bashi amsa kasawa tayi saboda ganin irin had’uwa da tsaruwan falon kasa daurewa tayi tace “wow gaskiya nima bari Baffa ya dawo wajena daban nima nake so kamar naka”
Ta fad’a tana shigewa cikin falon tana lumshe ido saboda daddad’an k’amshi da sanyin da ya bugi hancin ta sai da ta gama k’arewa falon kallo sannan ta juyo ta dubeshi”waye yake gyara maka wajennan?”
Ta tambaye shi saboda yadda taga wajen kalkal kamar d’akin mace.
D’an murmushi ya saki ya shafi fuskar ta “Ni nake gyara abuna indai ina so yamin yadda nakeso amma yanzun tunda gaki na dunga maleji danaki ko?”
Ya K’are da tambayarta, d’an tura baki tayi gaba cikin shagwab’a tace “hum um ai tunda maneji ne kawai kaci gaba da abunka,
Zo kiga ya fad’a yana jan hannunta zuwa saman benan dake falon, ta bishi har zuwa d’akin baccin shi take taga gado lafiyayye mai kyaun gaske “gyaramin zakiyi yau bani da lafiya” ya fad’a mata yana kallon yanayin ta, kafin ya juya ya fita, tana ganin fitar sa tayi wani irin sufa ta haye gadon tana wuntsilawa, wani irin taushi taji kamar auduga aranta kuwa fad’i take wallahi da sake bari Baffan ya dawo nima komai irin na bross na ke so ji gadonsa dan Allah kamar na wani yar sarkin ta k’ara nutsewa akan gadon.
Shi kam Muhammad har ya sauka ya tuna wayarshi da yabarta tun d’azun saman madubinsa dan haka ya koma ya dan d’aukowa nan ya shagala da kallon yadda take ta faman tsalle tsalle sam bataji motsin shigowarsa ba sai dai maganar sa taji.
“In kin gama Ammey tana kiranki” yafad’a yana d’aukar wayar shi datake saman meerrow ya juya ya fice ya barta batare da ya Kuma kallon inda take ba,
Ita kam sai da ta gaji dan kanta kafin ta gyara har bandaki sai da ta wanke masa kafin ta fito baya falon wani d’aki data gani ak’asan ta lek’a kawai sai taga computers da yawa aciki Maryam da Karam bani sai kawai ta shige kafin takai ga tab’awa sai gashi ya shigo kamar an jeho shi.
Ganin abinda take k’ok’arin yi yasa yai masifar had’e rai yace “me kika ajiyemin aanan” ya fad’a cikin dakakkiyar muryasa data sanshi da ita tun asali.
Maryam da kwata kwata bataji motsin saba sai maganar sa yasa ta juyo a d’an firgice ganin yanayin sa yasa jikinta ya kama rawa tace “nazo ne naga ko kana nan sai banganka ba shi ne shi ne
“Shine kika zo duba ajiyar da kikayi anan ko?”
Ya tambaya a dake take jikinta ya kama rawa ganin yadda yanayin sa ya koma kamar bai tab’a dariyaba
Muje zuwa
MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
????BA JININA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 25
“Ni ka dai na min irin wannan Kal lon” ta fad’a a d’an tsorace cikin rawan murya, k’ara tamke fuska yayi yace ” tambayar ki nake me kika ajiya anan?”
“Dan Allah bross ka matsa na wuce kar Mama ta dawo bata ganni ba” ta fad’a idanunta na cikowa da kwalla tana nadamar shigo masa d’akin data lura kamar na sirri ne.
“Kar ki min kuka idan ba hakaba tattaka ki zanyi yanzun anan” ya fad’a cikin dakewa.
Take ta had’iye kukan, tana jiran yabata hanya ta wuce, Saida ya gama hukuntata da mayun idanunsa kafin yaja kunnenta da d’an k’arfi yajata zuwa bangarensu.
Fashewa tayi da kuka domin bada wasa yaja mata kunnen ba sannan Kuma ya k’ara da muguntar murd’ewa, ai Nassar yana hangosu yayi saurin ficewa daga gidan daman ya lura yau yayan nasu akan tsini yake.
Shigan su yayi dai dai da sallamar Mama wadda dawowar ta kenan taga yanda yake ja ma ‘yar ta kunne cikin bala i tace “kai bak’in mugu azzalumi mai tayi maka’ ko kuma muguntar daka saba ne ya motsa sakar mata kunne kar ka tsinka azzalumi mugu”
Ta fad’a tana daga bakin k’ofar atsaye dan tana masifar shakkar sa domin idan ya juye bashi da mutunci acewar mama kenan.
Shi kam yi yai kamar baijiba saida yagama jigata ta kafin ya hankad’a ta jikin uwar ta ya juya ya fice, yana jiyo yadda take ta surfa masa ashar tana tsine masa ya saki wani murmushi mai ciwo yana shafa kwantacciyar suman kansa.
Alwala yayi ya fice masallaci domin lokacin anfara kiran sallar magriba.
Acikin gida kuwa bayan Mama tagama tujaranta ta juyo Kan Maryam tace “ke kuma me kika Masa yake neman lahanta min ke?”
Cikin kuka Maryam tace “wai dan na shiga d’akin compute sa shine fa yazo ya kamani shine tun acan yafaramin bala I”