BA JINI NA BA CE Page 21 to 30

A firgice tace “na shiga uku ni Sailuba me yakaiki d’akin wannan d’an iskan?
Baby me had’inki dashi dazaki je d’akin shi?
Kodai kin fara shiga sabgarsa ne baby ki rufamin asiri kada ki ruguzamin shirin daya kusa kammala”
Da mamaki Maryam take duban maman nata ganin yadda ta fita hayyacin ta daga cewa ta shiga d’akin MD anya babu wani mugun abinda maman take k’ullawa kuwa?
Girgizata haj. Sailuba tayi da k’arfi tace “Maryam ki fad’a min yaushe kika fara mu’amala da Muhammad?
“Mama ba d’an uwana bane?
Maryam tayi mata tambayar cikin mamaki kafin taci gaba da cewa mama dan Allah ki fad’a min illar hakan naga kin rud’e ko zai iya cutar danine?”
Tayi mata tambayar tana mai wani irin kafeta da ido, take haj. Sailuba ta dawo hayyacin ta tace “ba haka bane baby kinsan in mace da namiji suka keb’e to na ukun su shed’an ne shiyasa kikaga ina kaffa kaffa dake”
Cikin k’osawa da zancen tace “babu ma abinda zai faru insha Allah mama, kuma ni ban tab’a shiga d’akin ba sai yau” boyayyar ajiyar zuciya ta sauke tace “to kar ki k’ara”
“Naji tafad’a tana shigewa d’akin ta domin harga Allah zancen ya gara gundurar ta.
Itama haj. Sailuba tana shiga d’akin ta ko maganar salla bata tsayiba ta lalubo no haj. Zakiyya ya doka mata kira,jim kad’an bayan ta daga babu sallama babu komai tace,
“Na shiga uku na na lalace” cikin rud’ewa haj. Zakiyya tace “lafiya k’awata me kuma ya faru daga rabuwanmu yanzu yanzun?
“Zakiyya’yar iskar yarinyar nan tana neman lalata mana shiri, nace zanyi maganin ta kin hana wallahi zata rusamin shirina na shekara goma sha bakwai adai dai lokacin danake hango nasara na kusantoni”
“Wai duk me yafaru kike irin wannan zantuka kamar na sambatu?” Haj. Zakiyya ta tambaye ta cikin sauri domin tanason tasan abinda ya firgita k’awar tata haka.
Batare da wani jinkiri ba haj. Sailuba ta kwashe duk abinda yafaru daga dawowar ta gidan ta fad’a mata ta k’ara da cewa “inajin tsoron kar su rusamin tsohuwar gabar da na dasa atsakaninsu tsayin shekaru,adaidai lokacin da nake son yarinyar ta kasance mara””””” da kata haj. Zakiyya tayi saurin katse ta “wai kina tantama akan aikin sabon bokannan ne?”
Haj. Zakiyya tayi mata tambayar cikin son karfafa mata gwaiwa” bana shakka amma ina tsoron tugun uban shegiyar matar nan kinsan shima tsohon d’an tsubbu ne”
“Karki damu k’awata idan yanzun yatashi mu atafe muka kwana” nan taci gaba da karfafa mata gwaiwa akan mugun shirin su.
Tana shiga d’akinta ta yi gaggawar shiga wanka domin ana shirin shiga massalaci ne lokacin, wanka tayi ta d’auro alwala ta fito d’aure da tawul bata tsaya wani shafe shafe ba ta zura doguwar riga ta saka hijab ta haye saman abin salla.
bayan ta idar da sallar ne tayi zikiri da sauri ta tashi ta cire rigan ta hau shafe shafe kafin tagama har an kira Isha kasancewar lokacin magriba ya kwace mata sosai.
Sai da ta gabatar da sallar tayi karatun alqur ani mai girma kafin ta shirya cikin wasu riga da wando masu masifar kyau da daukar hankali farare kar, sai wani bluen rubutu da aka yi agaban rigar ONLY FOR YOU shine abinda aka rubuta, wandon kuma da kad’an ya wuce gwaiwar ta kayan sunyi masifar yi mata kyau ta taje dogon gashin kanta tayi parking d’inshi takawo wani bluen Vandana ta sakawa kanta ba d’an k’aramin kyau tayi ba haka nan ta hauyiwa kanta salfie da wayarta.
Tana cikin d’aukan kanta a hotunan MD da Nassar suka shigo d’akin tana ganin MD tayi masifar d’aure fuska, saboda abinda yayi mata d’azu, murmushi ya saki yana shafar gefen face d’inshi.
K’arasowa yayi kusa da ita ganin haka yasa ta maida kanta kasa tana wani cin magani, kafeta yayi da ido yanajin kamar ya had’iye ta tsabar masifar kyuan da tayi masa,
Hannu yasa ya d’ago habanta ya manna mata kiss a goshi kafin amshe wayan ya d’an rab’a ta da jikinsa kad’an ya soma d’aukar su hotuna.
Nassar yace “wow gaskiya bross kunyi kyau sosai kamar wasu masoya” da sauri ya dafe bakinsa saboda kallon dayaga MD yana masa fuskansa d’auke da wani irin murmushi.
“Nima ayi dani Nassar ya fad’a yana shiga tsakiyar su haka suka kasance ashiriri ce yayin da halin na Maryam ya motsa dan bata kula MD ba saboda abinda yayi mata.
Suna haka wayan Muhammad yai k’ara yana ganin layin Baffa na nageria yai saurin d’agawa”Allah ya temaki Baffa na” cewar MD yana sakin wani k’awataccen murmushi, duk shiru Nassar da Maryam sukayi jin MD ya ambaci Baffa
“Kuzo ka d’auke ni ina airport” shine abinda Baffa yace wa MD ya katse kiran “yeee” MD yafad’a da d’an tsallensa,duk suka kafeshi da ido kafin Nassar yace
“Baffa ne ya dawo?”
Hannu ya mik’a masa suka tafa “dad’i na dakai gane wa” inji MD yana murmushi “zo muje mu d’auko shi” yafad’a yana kama hannun yaron
“Nima zani” ya tsinkayo muryanta d’an juyowa yayi ya kalli kayan dake jikin ta sai kuma ya d’an girgiza mata kansa “gaskiya bazamu iya jiran har ki canja kaya ba yafad’a yana d’aure fuska”
“Dan Allah after kawai zan d’ora akai” ta fad’a cikin marairaicewa
” Minti biyu ya fad’a suna ficewa rik’e da hannun Nassar.
Taku ce MAMAN Islam
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
????BA JININA BACE
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 26
Jikin mota ta same su sai zance Nassar yake zuba masa yayin da shi kuma hankalinsa yake kan phone d’insa yanata faman latsawa.
Kamshinta ne yasa shi saurin d’agowa ya kafeta da ido yayin da zuciyar sa ya hau wani irin bugawa har d’an rawa rawa jikinsa ya soma abinda bai tab’a faruwa dashi ba.
“Muje” ta fad’a cikin fad’uwar gaba saboda shegen kallon dataga ya kafeta dashi, aranta tana bitar kalaman Mama anya ba wani abun ta hangoba kuwa?
Take raya hakan aranta sanda take shiga cikin motar, “my princess dan Allah kintaho da wayarki ki aramin?”
Cewar Abdul Nassar da ya zuroda kansa ta b’angaren datake,
“Kayi me dashi?” ta tambaye shi batare da ta d’ago ta kalleshi ba
“Boy zan kira anty dan Allah”
Kafin tace mai wani abu wayan yayi k’ara hakanan taji gabanta ya fad’i ganin no ba suna da mamaki aranta tace waye Kuma yake kirana ?
“Ki daga mana” take tsinkayo muryansa,
Dagawar tayi ba tareda ta k’ara kallonshi ba kafin tayi magana taji ance
” Amincin Allah yatabbata agareki yake saurauniyar kyawawa” wani irin murmushi ne ya sub’uce mata, zuwa yanzun ta fara sabawa da halin d boy wanda yabi ya mak’ak’ale mata ga d’anbanzan iya kalami me sanyaya Rai”
“Tareda kai ma aboc………..wani irin burki da MD ya take ne yasaka tayi wani tsalle ta gwaru da murgin motar wayar Kuma bata fad’i ko ina ba sai saman cinyarsa.
Hannu yasa ya d’auke wayar ya zurata acikin aljihun sa ya ya zagayo a zuciye yace “zoki ki fice min a mota” da mamaki ta tsaya kallonsa domin bataga abinda tayi masaba da zaiyi irin wannan fusatar haka lokaci guda “zoki fita nace malama” ya fad’a cikin wani irin buga tsawa, ai batasan lokacin data fito cikin wani irin rawar jiki ba, tana kallonsa ya koma yaja motar sa da wani irin matsiyacin gudu ya bud’e ta da qura, agogon hannunta ta duba tara saura batasan lokacin data fashe da wani irin kuka ba ta daga kai tana kallon sama yadda wani irin hadari ya murtuke bak’i k’irjinta ta dafe dayake wani fitinannen bugu tace “na shiga uku ni mero, me kuma nayiwa wannan mugun mutumin da zai ajeni anan” ta fad’a afili cikin muryan kuka yayin da aka wani irin kece da ruwa mai mugun k’arfi ga Maryam da mugun tsoron hadari bare ya sauketa a wannan wajen da babu kowa sannan babu gida kusa, jitai wani irin tsanar shi ya dawo mata sabuwa dal, tafara takawa a hankali yayin da take kuka sosai jikinta na wani irin rawa.