BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 21 to 30

Nassar kuwa ganin yadda bross d’in nasu yake wani irin tuk’in ganganci yasaka yai tsuru abayan mota yayin da tausayin Maryam ya cika ransa domin baiga abinda tayi masaba zai ajeta wajen da babu kowa sam bai kula da hadarin ba sai zuban ruwa yaji wanda yasa MD ta ka burkin dole.

Fashewa da kuka Nassar yayi da mugun k’arfi kafin yace fili “shikenan Addana ta mutu” yafad’a yana kuka sosai kafeshi MD yayi sosai kafin yajawo yaron jikinsa yana cewa “kai me kace?”

Memakon ya amsa masa sai cewa yayi”me tamaka bross zaka ajeta inda babu kowa ita kad’ai idan wani mugun abin yasameta fa?

Gashi kuma tana tsoron ruwan sama sosai idan ana ruwa babu inda take fita”

Sosai gabansa ya fad’i da maganganu yaron har baisan sanda ya tada motar batareda ya Kuma cewa komai ba ya figeta yana maijin haushin kansa akan abinda yay mata duk da cewa har lokacin zuciyar sa masifar zafi yake masa na yadda yaji tana magana da wani wanda yarasa me yasashi jin hakan?

Ita ko Maryam fara takawa tayi a hankali cikin wani irin tsoro jin yadda wajen yai tsit babu komai sai k’aran zubar ruwa yayin da zuciyar ta yake wani irin bugun dayasa jikinta rawa sosai tayi nisa da inda ya ajeta sosai tana tafi tana share ruwan dayake feso mata afuska wanda yake wanke hawayen dayake tafaman zubo mata babu ka’k’k’autawa.

Yana cikin tuk’in kiran Baffa ya k’ara shigowa faking yayi a gefe kafin ya d’aga “karka zo naga garin da hadari na hau tixi” abinda Baffa ya fad’a kenan ya kashe wayar batare da yace komaiba, saboda kar Baffa ya gane halin da yake ciki.

Sanda yazo inda ya sauketa ta ya rage gudu sosai zuciyar sa ya buga dan ganin bata wajen yayin da Nassar ya kuma fashewa da kuka dan a tunaninasa wani abun ne yasamu ‘yar uwarsa.

“Dalla malam ka karka damemu ka rufe mana baki d’if ya d’in ke bakinsa saboda yadda yaga bross d’in yai wani irin canza kama fuskar nan tayi wani irin ja yayinda ya soma zargin kansa akan abinda yayi mata sam baiga kyautawar saba ko kad’an.

A hankali ya cigaba da jan motar yana d’an duddubawa ko zai ganta Maryam wacce taci kuka ta k’oshi ga d’an banzan dukan da ruwa yake mata wanda yasa wani mugun zazzab’i ya saukar mata lokaci guda ta sami gefen hanya ta zauna tana ta faman shashshek’a.

“Gata can bross” Nassar wanda shima yaci kuka ya k’oshi ya fad’a yana nunota tana zaune kan wani dutse data gani abakin hanya jikinta yana wani irin rawa.

Da mugun gudu ya bud’e motar ya fita yana cewa Nassar kar ya fito a cikin ruwan nan, bak’aramin sanyin jikinsa yayi ba ganin yadda ta had’e Kai da gwaiwar ta tana faman shashshek’a, a hankali ya durk’usa agabanta ya dafa kafad’anta.

D’agowa tayi a mugun firgice domin batayi tunanin ma zai dayiba asanin datayi mai na tsantsar rashin mutunci sannan kuma tasan ba wai yana sonsu bane kamar yadda mamanta ta fad’a Mata.

Wani irin kallo ta watsa masa da idanunta da sukayi wani irin ja wanda har lokacin basu daina zubo da ruwa “sorry” ya fad’a can k’asan mak’oshi cikin d’an rawa rawan murya “sorry for what?” ta tambaye shi cikin tsantsar b’acin rai da bak’in cikin abinda yai mata.    

“Zo mu tafi” ya fad’a yana kallon yadda ruwa yake tsiyayo Mata tundaga kanta yana kwanrawa kayan jikinta duk sun wani lafe mata ajiki dake ruwa ake tsugawa bana wasa ba, banza tayi dashi kamar bataji me yace ba.

“Dan Allah” ya k’ara fad’a kamar maijin tsoro, yayin da shima sanyin ruwan yafara ratsashi ” ba ruwana da kai kar ka k’ara shiga harkana babu ni babu kai mugu kawai” ta fad’a cikin rawan murya sosai yayin da wani irin sanyi yake k’ara shigarta hatta hak’orinta yana jin yadda suke bugan juna

“Dan Allah” ya k’ara fad’a kamar zai mata kuka mak’e mai kafad’a tayi tace “um um na tsan……….wani irin fisgota yayi kafin ta k’arasa ya had’e bakinsu waje guda yana mata wani irin shan mugunta sai da ta raina kanata kafin ya sakar mata bakin cikin wani irin b’acin rai yace “sai wancen dan iskan saurayin naki ne baki tsanaba ko?

Ni kikewa wannan abun akan na nuna b’acin raina akan kina kula wani banza can daban ko na gode” ya fad’a muryan shi na d’an rawa kad’an.

Sai yanzu ta gane dalilin dayasa ya gane mata wannan bala in yabarta a cikin tashin hankali da tsoro jitai ranta ya dad’a mugun b’aci zuciyar ta ya wani irin dakewa ta mik’e kawai ta kama tafiya dan taci alwashin bazataje a motarsa ba “ke meye haka?” ya fad’a cikin d’an tsawa tsawa ko kallon inda yake batayi ba taci gaba da tafiya.

Duk irin yadda yaso rarrashin ta abin gagara yayi hakan yasaka shi tattare hannun riga ya sunkce ta tana wuwulla k’afa tana komai ya nufi mota da ita

Plss manage

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button