BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 31 to 40

Bud’e motar yai ya wulla baya kusa da Nassar sai uban kuka take jijiyan kanta sunyi wani rud’u rud’u fuskar nan tayi jajur tsabar kukan da takeci.Shiru Nassar yayi yana kallon yadda Adda nashi take kuka ga ruwan dayake ta faman diga daga jikinta rawan da jikinta yake kawai ya tabbatar masa da akwai zazzab’i atare da ita.

MD tuk’in yake amma ba acikin nutsuwa ba domin ba k’aramin bugun zuciyar sa kukanta yake ba ko kad’an baiji dad’in abinda yayi mataba sai dai ko kad’an zuciyarsa ta kasa amsar laifin ganinsa bai kamata ace ta tsaya magana da wani k’aton agabansa sosai abin ya masa zafi aransa, wata zuciyar Kuma cemai tayi inbanda abinka kasan waye da har zakayi saurin fushi haka “zai wuce d’an iskan mate d’in nan nata” ya fad’a asarari Kuma da k’arfi, duk suka bishi da kallo har Maryam datake kuka sai data tsagaita jin yadda ya bugi sitiyarin da mugun k’arfi.

Suna zuwa gida taba tsaya amsar wayanta ba ta balle murfin motar tayi cikin gida da gudu tana shashshek’a ta wuce mama da Ammey a falon duk suka bita da kallo, saida tasawa d’akin key tasan sarai sai Mama ta biyota jikak’k’un kayan ta cire ta shiga ta had’a ruwa mai mugun zafi har lokacin rawan sanyi take sosai ta shige cikin ruwan tana faman sauke ajiyan zuciya sai da ta gasa jikin ta sosai kafin tayi wanka ta fito ta shafa mai ta haye gado ranan bata had’u da Baffanta duk da irin yadda tayi kewansa.

Washe gari ma bata fito da wuriba sai da ta gama duk nuk’u nuk’un ta sannan ta salla wanka ta ta tsara kwalliya mai kyau da d’aukan hankali ta fito cikin nutsuwar ta duk suka bita da kallo har tayi wani fayau da ita.

Baffa ya dubeta yana murmushi ya mik’a ta hannu”zonan ki zauna, ya fad’a yana nuna mata gefensa nayi kewan ku sosai yarana” ya fad’a yayin da tasako hannunta cikin nashi ya zaunar da ita a kujeran kusa dashi.

Tunda ta fito ya kafeta da ido sai yaga ta k’ara masa wani fitinannen kyau, gaida iyayen nata tayi, kamar ta share shi sai kuma ta gaidaahi cikin sanyin murya amsawa yayi yana k’ureta da ido, tai masifar had’e rai tana had’a tea.

Su Mama suna gama karyawa suka bar wajen suka koma falon Baffa da akwai abinda suke son tattaunawa.

Yana ganin fitar su ya ture nashi abincin ya kwantar da kansa saman tebur d’in yana binta da wani fitinannen kallo Nassar na ganin haka ta d’auke ragowar abincin sa yabar wajen.

Gaba d’aya ya takura da wannan banzan kallon nasa sai dai bata son tayi abinda zai gane hakan, kasa cin abincin tayi sai ruwan shayin da take ta karb’a tashi yai ya dawo kusa da ita kofin shayin ya karb’a daga hannunta ya zauna ya kai bakin ta, d’auke kanta tayi tareda k’ara tamke fuska.

“Kiyi hak’uri dan Allah, ya jikin naki?” ya fad’a yana shafar gefen fuskar ta, banza tayi da shi idanunta yana cikowa da hawaye ko abinda d boy yai mata bai sosa mata rai kamar na MD ba.

Juyo da fuskar ta yayi kusa da shi yana k’ara kai mata abincin bakinta “karki min kuka, kiyi hak’uri dan Allah” ya fad’a cikin sanyin murya, batare da tace k’ala ba ta yunk’ura zata bar masa wajen ya daka mata tsawar dayasa ta koma ta zauna batare da tasan tayi hakan.

“Wallahi yanzu sai na tattaka ki dan kinga ina lallab’a ki shine kike neman ki kawo min rainin hankali karb’i dalla malama” ya fad’a yana kai mata abincin baki ganin yanda yai kicin kicin da rai yasa ta bud’e bakin ya zuba mata abincin haka ya dinga bata tana karb’a tana hawaye har saida ya tabbatar ta k’oshi kafin ya bata ruwa tasha ya kama hannunta ta suka nufi part d’insa.

Duk jiya bai iya runtsawa ba saboda tunanin abinda yayi mata iya binciken sa nason gano dalilin yi mata haka amma amsar d’aya ne tayi waya da wani agabansa dalilin fushin sa akan hakan simple words INA SON TA duk ta yadda ya juya al’amarin amsar d’ayace abin ya masifar tayar masa da hankali bai tab’a tunanin hakan daga zuciyar saba sam batayi masa adalci ba kuma ta zalunce shi tayi mai abinda zai hana shi cika alk’awarin daya daukarwa Baffa, dan iya jiya kawai ba k’aramin tashin hankali ya shiga ba ganin halin data shiga sosai ya bama kansa laifi akan abinda yayi Mata.

Suna shiga falon ya zaunar da ita saman kujera ya zauna kusa da ita ya kamo hannunta yana murzawa a hankali wanda hakan yasa taji wani irin yarrrrrrrr ajikinta da k’arfi ta k’wace hannunta ga mamakinta sai ji tayi yace “bani da lafiya” shine abin taji ya fad’a cikin wata irin murya wadda take taji wani irin kasala ya rufeta saboda salon dayai maganar kasa ce masa komai tayi sai ma k’asa da ta maida kanta tana faman cukwaikwauye gefen d’ankwalin doguwar rigan da yake jikinta

“Ni kaina bansan abinda yasa nayi miki hakan ba princess nasan ban kyautaba abinda nayi, abin yayi mugun damuna na rasa yadda zanyi na kasa runtsawa saboda neman dalilin da yasaka nayi miki hakan, sai dai dalilin dana samo bai min dad’i ba ko kad’an Maryam” ya k’arasa da kiran ainihin sunanta wanda sai yaune ta tab’a jin ya kira sunanta iya tsawon rayuwar ta, sai taji wani iri aranta sai dai bata d’ago kaiba bare tace wani abu.

Ga mamakinta sai ya kamo fuskar ta ya juyo da ita saitin tashi ta d’an kafe shi da ido yadda taga yayi mugun yin kalar tausayi idanunsa da ta kalla kuwa sai da gabanta yai masifar fad’uwa da sauri ta mai da kanta k’asa.

Abinda ya k’ara bata tsoro yadda ya zame ya durk’usa agabanta yana kallon cikin idonta yace “dan Allah princess in rok’i wani alfarma a wajen ki?”

Yadda yayi matan ne yasaka batasan sanda ta d’aga masa kai ba alaman shi take sauraro ” dan Allah princess ina so na zama amininki na k’ut da k’ut yanda komai zakiyi sai kin sanar dani nima duk abinda zanyi sai na sanar dake sannan dan Allah yaron jiya kar ki k’ara d’aga kiran shi namayi blocked d’insa dan Allah kimin wannan”

“Aini bazan iya abota dakai ba kai mugune baka da tausayi daman ai su sojoji basu da imani shi yasa na tsan”……….bai bari ta k’arasa ba yayi saurin rufe mata baki da hannunsa cikin sanyin murya yace “zokiji Allah na daina daga yau bazan kara b’ata miki rai ba” 

Idan na tabbatar da hakan sai na zama friend d’in naka amma ni yanzun banyin abota dakai yasin dan zaka iya kashe ni wata rana ai dama Mama tace komai dad’in ka da ‘yan ” ke”

Ya buga mata wani shegen tsawa “wallahi kika Kuma min zancen d’an ubannan sai na sab’a miki kammani yanzun nan haba kin ishe ni da wani’yan uba’yan uba’yan uban…………ya dank’aro k’aton asher ya dank’ara kafin yaci gaba da fad’in duk wanda yasa miki wannan tunanin jakine shi dabba ne mai kwakwalwan kifi Kuma daga yau ina so kisa aranki cewa baki da wani d’an uba duk uwa d’aya uba d’aya muke agidannan tashi ki fita” ya fad’a cikin daka mata tsawa yana nuna mata k’ofa ai da gudu ta fella cikin rawan jiki dan yanayin sa ba k’aramin firgita ta yayiba.

Komawa yayi saman kujeran da ta tashi ya zauna tare da kwantar da bayansa yana fitar da wani mugun huci me azabar zafi aduniya bai tab’a ganin matar daya tsana kamar Sailuba ba ya tsane ta ya tsane ta ya tsane ta har baisan yadda zaiyi ba

MAMAN ISLAM CE

بسم الله الرحمن الر حيم

*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

   FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*

1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button