BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 31 to 40

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*________________________

????BA JININA BACE????

2021

                 NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

. page 28

Tana shiga d’akinta ta mai da k’ofar ta rufe kamar ance ya biyota ne, k’arasawa tayi bakin gado ta zaune tareda dafe k’irjinta da har lokacin bai bar bugawa ba ta “jarababbe kawai mutum babu abinda ya aje sai masifa ta fad’a tana kwanciya akan gadon bata jimaba kuwa bacci yayi awon gaba da ita.

Tunda ya zauna ya lumshe idanunsa zuciyar sa na masa zafi, so yake kota wane hali sai ya raba Maryam da haj. Sailuba domin wannan matar bata da maraba da matar shed’an muguwar hatsabibiya ce tasan takan mugunta shi kansa yana tsoron shirin da take kan ‘yar mutane domin yafi kowa sanin cewa ba rainon banza haj. Sailuba tayi wa Maryam ba dan bata aikin banza shi yasa yake son ko ta wane hali ya yakice Maryam daga jikinta kafin ta kai ga halaka ta.

Ganin zaman sai k’ara bijiro masa da wasu irin tunaninka yake yasa yai wanka ya bar gidan.

A falon Baffa kuwa bayan sun gama d’an tab’a hiransu kamar yadda suka saba Baffa ya d’an dubi matan nasa yace “yau ina so naje k’auye ba kuma zan dawo yau d’in ba sai Allah ya kaimu gobe”

A matuk’ar firgice haj. Sailuba ta d’ago tana duban Baffa cikin tashin hankali yaushe tayi wannan saken ca take ta riga da tagama da babin wannan tsohuwar me shegen taurin kan tsiya ai kuwa zata gyara mata zama yanzu dai ba ta ita take ba ta wannan ‘yar matsafin mutumin da aiki baya cinta take.

A fuska ma nunawa tayi tafi kowa murnan zuwansa a bad’ini kuwa ji take kamar tayi ta ihu domin har ga Allah tun lokacin da Inna ta bada shawarar ayi mata kishiya ta sha alwashin sai ta d’an d’ana mata guba fiye da wacce ta d’an d’ana mata.

Sai da ya fara zuwa wajen malam Babba kamar yadda ya saba yauma saida ya bashi rubutu yasha ya shafe jikinsa sannan yake bashi a duk lokacin dayake gari, kafin ya sanar dashi zaije ganin gida ba k’aramin dad’i malam yajiba domin hasashen shi yazama gaskiya cewa Baffa rabashi ake son yi da mahaifiyarsa shi yasa yaji sam baya son zuwa, amma duk wanda yake wannan abun sam bai kyautawa kansa ba.

Bayan fitar Baffa babu jimawa itama ta shirya ta fice bata zame ko ina ba sai wajen bokanta kasancewar haj. Zakiyya sunbar k’asar da mijinta yasa batama tsaya b’ata lokacin tab’a ta wuce abin ta.

Bayan tagama korawa bokan ta bayanin aikin da take son yayi mata ya jima sosai yana zane cikin k’asa kafin ya d’ago ya dubeta yace. “akwai abubuwa da yawa wanda kika jima kina k’ullawa duk tunaninki basa yiyuwa?”

Ya fad’a yana kallonta, shiru tayi domin batayi tunanin aikin da take yana ciba dan bata ganin nasara a ciki.

Aikin ki yana ci kuma abubuwan da kike sunyi yawa kuma duk ta sigar da kika d’auko hanyar wargaza komai tanan zai wargaje zaki sha mamakin rana da lokaci da waje amma kuma akwai cin amana da bayyanuwar asirinki daga baya daga wajen mutum mafi kusa dake wannan shine ki tashi kije da baya banda waiwaye daga yau bazai k’ara zuwa wajen uwarsaba sai dai ita tazo shi da garin nan sai dai yaje gaisuwar ta bayan ta rasu.

Tunda takwanta take waau irin mafarkai marasa kan gado sosai take jujjuya kai tana gumi babu abinda yafi rud’a ta sai tsintar kanta da tayi a wani a hali mara dad’i tana cikin jujjuya kai kamar wacce aka tasa ta bud’e ido a firgice, sai da tayi addu’ar tashi a bacci kafin ta mik’e cikin tashin hankali ta hau karanto hasbinnallahu wani imal wakil sosai abin ya tsaye Mata arai.

D boy ne a office d’in babanshi suna hira yake sako masa maganar Maryam Abba AL HASSAN yace ” ‘yar waye?”

” ‘yar Baffa Abubakar ce”

” Kai k’arya ne wallahi badani ba ka rasa wa zaka d’auko min a matsayin suruka sai k’anwar wannan bom d’in wallahi ba isa ba baka isa ba nace dan ubanka”

“Ni wallahi Dad ita nake so dan haka banga wanda ya isa hanani aurenta ba waima Dad meke tsakaninka da yayannata ne naga ko sunan su kaji saika firgita?”

“Ban sani ba dan uwarka kuma muddun nine ubanka ban yafe maka auren wannan irin masifar ba”

” Muddun kaga ban aure taba ka tabbatar mutuwa nayi amma kai baka isa hanani auren taba wallahi” ya fad’a cikin dukan teburin tsakiyar su cikin murgud’a baki kamar wani sa ‘ansa,

Wannan ba komai bane a wajenshi dan al amarin gidan Abba AL HASSAN babu tarbiyya ko kad’an da gaba d’aya sun gama sangarta d’an nasu kasancewar shi kadaine d’an da suke da.

“Tunda haka kace to wallahi babu ruwana duk abinda ya biyo bayan ka kar kasawa ranka cewa na san ka dan wallahi ko kallon inda kake bazanyiba.

“Ba damuwa” Kamal ya fad’a yana ficewa daga office din

Plss manage

Daga taku MAMAN ISLAM CE

بسم الله الرحمن الر حيم

*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

   FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*________________________

???? BA JININA BACE????

       

2021

               NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 29

Wanka tayi ta tayi alwala dake lokacin an fara kiran Azhar dan haka tana gabatar da sallar ta shirya tareda daukar bag d’in ta ta fito babu kowa a falon sai Ammey.

“Ina zaki haka?” Ammey ta tambaya tana kallon fuskar ta dayake cike da damuwa’ kamar bazata tanka mataba sai kuma tace “shopping” kamar maijin tsoro tayi maganar”

“Zonan” Ammey ta kirata kallon Ammeyn tayi kamar tayi mata gardama sai kuma ta karasa kusa da Ammeyn ta zauna ta d’an jingina jikinta dana Ammeyn,abinda bata tab’a yiba iya tsawon shekarun datayi a hannun haj. Sailuba batama samu anbar ta taje inda take ba bare ta rab’etan.

Wata irin ajiyar zuciya Maryam ta sauke mai k’arfin gaske lokacin da ta kwantar da kanta jikin mahaifiyar ta ita kanta Ammeyn sai dataji wani iri aranta bata san sanda wasu irin hawaye suka zubo mata ba tayi saurin gogewa dan kar tagani.

Duk inda uwa take ko a ina ne ko a wane hali take ta fita daban hakanne ya kasancewa Maryam jitai wani irin nutsuwa na shigarta tareda wani d’an Karen sanyi da ya dirar mata lokaci guda alamun zazzab’i keson kamata.

Haka nan batasan dalil ba kawai taji ta kama hawayen da batasan ko na menene ba tun iya hawayen ne har tafara shashshek’a, a rud’e Ammey ta d’ago fuskar ta tana kallon yadda take shashshek’a kallon lips d’inta tayi yadda suke rawa sosai batasan sanda ta k’ara k’ank’ame ta ba tana d’an buga bayanta kad’an kad’an batare da tace komai ba domin tasan tabbas itama idan tayi magana nata kukanne zai fasu.

Sai da suka shafe ak’alla mintuna uku kafin Ammey ta d’ago ta ta fara share mata hawayen “me yake damunki?”

Ta tambaye ta ahankali kamar tana jin tsoron wani yajita tace “Ammey jikin yafi na Mama dad’in kwanciya kuma ga d’umi,dan Allah Ammey nima ki rik’a rungumeni kamar yadda kike wa Nassar”

“Naji amma sai kin fad’a min abinda yake damun ki kwanakin nan, na lura kina da damuwa keep ki fad’a min koda ahawaran da zan baki” kallon Ammeyn ta dingayi babu k’ak’k’autawa yayin data ta dinga jin wani abu mai sanyin gaske yana ratsa ta, tunda take da maman ta bata tab’a tambayar ta damuwanta ba sai dai idan taganta a damuwan ta d’ebi manyan kud’ad’e ta bata tace taje ta kore damuwan ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button