BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 31 to 40

” Ina jinki’yar albarka maza ki fad’amin ki d’auka cewar kina fad’awa mahaifiyar ki ne kima sa aranki cewa ni mahaifiyar kine zan miki maganin duk wani damuwaki a duniya,wanda kuma yafi k’arfi na zan fad’a wa ubangiji na”

Ammey ta fad’a tana saurin goge hawayen daya zubo mata dan kar ta gani Muhammad dayake tsaye bakin k’ofar tun sanda Ammey ta kira Maryam ya saki wani boyayyar ajiyar zuciya aransa yana fatan Allah ya karya ak’adarin haj. Sailuba.

“Ba komai” ta fad’a a hankali “kwai baby command fad’a min kinsan babu kyau d’a ya rik’a wa mamansa k’arya” batasan sanda ta rushe da kukaba tace “Ammey k’udi sune maganin ko wane matsala?”

Ta tambaye ta abinda yafi komai damunta a rayuwarta

” Injiwa? 

Duk wanda ya fad’a miki wannan k’arya yake ko waye yana yaudarar kine kawai, amma akwai abinda k’udi bai isa yayi maka shi ba da yawa ma a duniya dan haka duk wanda ya fad’a miki hakan yayi karya ya fad’i son ransa ne kawai”

Ta fad’a tana shafa kanta nan “Mama ce koya ta ganni a cikin damuwa sai ta d’ebi manyan kud’ad’e ta bani tace zasuyi min maganin ko wace irin matsala a duniya” duk da cewa tasan zata iya jin abinda yafi haka daga d’iyar tata ma amma hakan sai yayi masifar d’aga mata hankali tace

“Tana iya miki kyautar nawa lokaci guda?” Ta tambaye ta cikin tsantsar tashin hankali “har dubu d’ari biyar cash tana bani tace muje mu kama waje muyi d’an kwarya kwaryan walima wai na jikina ma su mori arzik’in ubana”

“Kina yi?” 

Ammey ta k’ara jefo mata wani tambayan “da inayi amma yanzun tara k’udin nakeyi da sukayi yawa na sai gida kuma da wasu kusan 7 million a d’akina har sani fa take na d’ebo mata k’udin Baffa kinsan baya k’irga wa yake ajiyewa”

“Innalillahi wainnailahi raji un” shine abinda Ammeyn ta fad’a cikin tashin hankali “Allah sarki Nanne da Anty shamsiyya yau ga abinda kuke fad’a min yana shirin faruwa tayi maganar cikin zubowar wasu zafafan hawaye.

Da sauri ta share hawayen tace”kin yarda dani zaki iya bani ajiyar duk abinda kika mallaka?” Ta tambaye ta cikin rawan murya

” Eh Ammey me zai hana ta bata amsa yayin da wani irin sanyi yake kwaranya aranta

“Yayanku fa?” ta k’ara tambayar ta

“Tab’ni bazan bashi ba mugu ne gashi masifaffen tsiya ta fad’a tana hararan gefe.

Murmushi Ammey tayi shi kanshi Muhammad dake bakin k’ofar maganar ta ya bashi dariya dan haka ya d’an murmusa yana shafar k’irjinshi a hankali kamar wanda wajen yake masa ciwo

“Kece baki gane halinsa ba amma yana da kirki sosai kuma zai kula daku sosai koda ace yau babu Baffa baku da sama dashi SHINE GATANKU”

Tab’e baki tayi ta mik’e tana cewa “anjima zan kawo miki A T M d’ina Mama bata san dashi ba saboda shegen kashe k’udin ta idan ta sani duk saita rance kuma ba biyana take ba, tunda kince kin yarda dashi sai ki bashi zan had’a shi kuma da na siyi gida ta hanyar sa wallahi ya cinye kwandala ta bazai yi ciwon kai ba biyana zaki”

Duk yadda yaso dauerwa saida ya fashe da dariyan maganta domin ta bashi dariya sosai wallahi, ita kanta Ammeyn murmushi take kafin tace “yanzun to ina zaki naga ko abinci baki ciba”

Eh banjin yunwa zanje shopping, ina Nassar ya rakani?”

“Za daiki siyan kayan zakin da kika saba maza muje yau nima na fanshi hajiyan tunda bata nan muje na baki da kaina tunda ta gama shagwab’a ki”

Sai taji ta kasa yi mata musu tana zuba mata abincin kafin ta fara bata MD ya shigo wajen da sallama Ammey ta d’ago ta dubeshi ganinsa da kayan gida tace “yau kuma ina uniform d’in?”

“Banje office ba yau?” Ya fad’a yana zama facing d’in Maryam datai wani kicin kicin da rai, murmushi ya saki lokacin da ya juyo da hannun Ammey santar bakin sa ya amshe abincin da ta d’ebo zata kaima Maryam baki, bata san sanda ta b’alla masa wata shegiyar harara ba ta juya ta kalli Ammey a marairaice tace Ammey”

“K’yale shi baby in yasa tsiya yanzun zan korashi amshi maza kici ki k’oshi kinji yarinyar kirki ta fad’a tana bata, sosai taci abincin, tunda take zata iya runtsawa cewar bata tab’a samun farin ciki irin na yau a rayuwarta ba sai taji Ammey ta bala in kwanta mata arai.

tana gamawa tasa tusio ta goge bakinta ta zari mukullin motar ta”sai na dawo Ammey”

“Baki ba Ammeyn ta fad’a tana mik’ewa ta k’arasa kusa da ita kanta ta dafa tayi mata addu’a sosai kafin tace “Allah ya tsaremin ke ki kula da kanki ki kare mutuncin ki domin shine Martaba ki”

Wani irin sanyi Maryam taji aranta ta rungumeta ta tace “na gode sosai Ammey dan Allah ki rik’a min haka please” 

“Kullum nake miki haka amma ba kusa da kusa ba amma ko yaushe kece farkon wacce nake fara yiwa addu’a kafin nida kaninki da sauran makusanta na”

“Allah Ammey?” Maryam ta tambaya ciki farin ciki tare dajin yadda matar tak e k’ara bin dukan jikinta, dama haka halin Ammeyn yake amma mama tace muguwa ce.

MAMAN ISLAM CE

بسم الله الرحمن الر حيم

*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

   FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*________________________

???? BA JININA BACE????

2021

                NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 30

Rungumeta ta k’ara yi tace “na tafi Ammey na”

“Sai kin dawo’yar albarka”

“Nima zan rakaki zaki siyamin chocolate?”

Yayi mata yadda Nassar yake mata, batasan sanda ta saki murmushi ba ta fice a daga wajen cin abincin, binta yayi shima domin yi mata rakiya.

Tayi zaton shi zai jasu, sai kawai taga ya bud’e wajen mai zaman banza ya k’ame abinsa, tura baki tayi tana d’an hararansa ta gefen ido, sarai ya ganta sai ya mai da kansa gefe yana d’an murmushi hakanan yanzu komai tayi burge shi take.

Sai da ta zauna ta sakarwa mai gadi k’aton hon wannan ba sabon abu ba ne awajenea sam indai zatayi tuk’i batayin na nutsuwa tun lokacin data ke a matsayin Maryam ba yanzun da ta zama mero ba lol????????????

Shi kanshi Muhammad sai da yai mamakin ganin yadda ta wani figi motar da masifar gudu bai san sanda ya juyo yana kallonta ba “ke baki da hankali ne?”

Ya fad’a lokacin dayaga ta kusa fad’awa wani d’an rami dake tsakiyar titin data hau tayi wani irin kaucewa ramin 

“Princess tsaya” ya da sauri yana dafe kan sa da duka hannayensa.

Babu musu ta nemi waje ta faka dama da biyu ta keyi dan ya amsa banda son banza tana tare dashi d’in zata zauna ta jashi????????????

Canjin wajen zama sukayi ya amshi tuk’in yana fad’in”naga alamun ke kin shirya mutuwa ni kam gaskiya bana so na mutu banyi aure ba”

Ya fad’a cikin barkwanci.

Murmushi kawai tayi bata tanka masa ba, sai ma wayar ta data d’auko ta bud’e data tana chat da friend d’inta tana duba no d boy babu shi kwata kwata a jerin contact d’in ta da gaske yake ya goge.

D’an kallonsa tayi sai akayi sa a shiama ya wago yana kallonta ta gira ya dage mata alamun ya dai?

D’auke kai tayi tana tuna hargagin sa na d’azu akan mama wani lokacin bata cika ganin lafim su ba domin halin mama sai mai hak’uri.

Kusan sau uku tana kamashi yana kallonta kuma duk sanda zasu had’a ido sai yamata alaman yadai? 

Sai kawai ta hak’ura bata k’ara kallonsa ba har suka isa sper market d’in da yawanci anan suke siyayya duka ‘yan gidansu.

Bayan ya samu waje ya faka ya bud’e ya fito sannan ya zagayo ya bud’e mata bayan tagama gyara mayafinta ta fito a hankali ya Mai da motar ya rufe ya kama hannunta suka fara jerawa cikin wajen.

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button