BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 31 to 40

Duk inda suka gifta sai idanu sun bisu saboda masifar kyawunsu da kuma yadda sukayi macin d’in da mutane sukayi da juna.

Sunzo shiga shi Kuma d boy sun zo fita shi da abokansa ya gansu sai da gabansa ya fad’i ganin ta tare da wannan gwaskan yayan nata ya wani kafesu da ido har suka k’araso inda suke, sai lokacin ma Maryam ta kula da d boy ta d’an saci kallon MD wanda gaba d’aya hankalin sa yake kan wayar sa.

Sai da tagawa d boy hannu ne shi kuma kamar wanda akace ya d’ago sai kawai yabi hannunta da kallo lokacin shima d boy ya d’ago mata tare da wani irin mumushin farin cikin ganin da yayi, kafesu yayi da wani fitinannen kallo zuciyar sa ya hau wani fat fat fat ko ko kad’an bai damuwa da labarin mutane amma ko cikin miliyan sai ya fidda d’an jakin mutumin can, kuma ko da ace shi bai son Maryam wallahi datayi mu ‘amala da wancen gwamm ace masa ta mutu ne shi zai fi masa sauk’i.

Sam bata kulla da kallon da yakafe d boy da shi ba amma shi d boy yana ankarewa take jikin sa ya hau rawa ta ina zai manta da wannan basumuden mutumin wanda babu abinda ya ajiye sai mugunta tsantsar ta, kafin Maryam tayi wani motsi d boy ya b’acewa ganinta, ta d’ago kai da zummar yiwa MD magana yadda taga yayi kicin kicin da rai sai da gabanta ya fad’i ta d’auke kai aranta tana tunanin anya wannan bashi da aljanu?

Duk abubuwan data siya shine ya biya k’udin, suka fito daga wajen har lokacin babu annuri atare da shi dan haka taja bakin ta ta tsuke bata k’ara kallon inda yake ba.

Mai makon ya wuce gida kai tsaye taga ya d’auki wani hanya daban amma dake haushin sa take ji bata dube shi ba bare tayi masa tambayar inda zai kaita, har suka isa wani d’an madaidaicin gida mai kyau ya faka motar a k’ofar gidan ya fita ya kwankwasa aka bud’e masa wanda m Bash ya ganine yasashi hangame baki

“Amma dai b’atan hanya kayi ko MD” m Bash ya fad’a yana d’an rik’e baki, harara MD ya zafga masa yace “aini gwanda ni na kawo maka ziyaran kai yaushe rabonka da inda nake? Kuma yanzun ma ba wajenka nazo ba wajen madam nazo tana dai ciki ko?”

” Hum tana ciki mana ina zata bayan gani yawo ai sai ku manyan gwaraye”

Harara ya galla masa batare da yace masa koma mota, har lokacin bata saki ranta ba hannunta kawai ya kama batare da yace mata komai ba ya nufo gidan.

Ido ta d’an waro lokacin da suka tunkaro gidan, yayin da shi kuma ya sakar mata murmushi,itama murmushin tayi masa ta d’an rusuna ta gaida shi kafin ‘ yace ta wuce ciki,

Kallo MD ya bita dashi har ta shige kafin ya maida hankalin sa kan m Bash da yafe shi da ido’

” Muje man munafiki ka wani zubamin ido kamar zaka cinye ni” murmushi m Bash yayi kafin yace “SON TA KAKE KO?”

“Na fad’a maka”

“Sai ka fad’amin gashi nan ina ganin sa acikin idanunka”

” Hum abokina ban san sanda yarinyar nan tayi tsalle ta daki zuciya naba lokaci guda sonta yamin wani irin kamu wanda har ya fara tab’a wasu daga cikin al’amurana na yau da gone”

“Ka fad’a Mata?”

“Ban fad’a mataba”

“Me yasa?”

” Inajin tsoron kar tace bata sona duk da nasan cewa idan nace ina sonta ko bata so sai an bani ita”

“To kajarraba Mana”

Ta yaya bazan iya ba ina matuk’ar jin tsoron kada tace a a” ya fad’a cikin tsananin damuwa sosai

Sosai m Bash yaji yana jin tausayin abokin nasa dafa kafad’ar sa yayi yace “abokina kada ka bari ya huce” daga haka yaja hannunsa zuwa cikin gidan. 

Har Hajara matar m Bash ta tarb’eta duk da cewa bata santa ba amma ta cika mata gabanta da kayan makulashe suna d’an tab’a hira sama sama dake Maryam bata da bak’unta sam.

Kusa da ita MD ya zauna yana kallonta tare da tunanin ta yadda zai fara taranta da maganar musamman idan ya tuna irin kallon da take masa.

Ji ta ta takura da kallon daya takura masa dashi d’agowa tayi ta d’an kalleshi kafin ta kauda kanta tana hararan gefe

Taku ce MAMAN Islam

بسم الله الرحمن الر حيم

*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

   FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*________________________

???? BA JININA BACE????

    

2021

              NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 31

Kayan da Hajara ta aje mata ya kalla yaga babu abinda ta tab’a, sai ya d’an dubeta yaga yadda take ta faman hararan gefe ta wani turo baki gaba baisan sanda ya saki murmushi ba, yasa hannu ya d’ago hab’an ya kafeta da wani shegen kallo.

Ganin haka yasa m Bash ya janye matarsa suka bar musu falon, kasa daurewa kallon nasa tayi sai kawai tayi saurin rufe idanunta.

“Waye shi?”

Ta tsinci muryarsa yana mata tambayar da bata san inda ya dosa ba kallonsa take da alaman tambaya a fuskar ta itama?.

“Wanda ya d’auke miki hankali a sper maket?”

Yanzu kam kallon shi take da madaukakin mamaki, yadda yai bala in d’auke mata kai har kawo zuwansu nan batayi tunanin zai kula da hakan ba.

“D boy ne yaron daya dakeni a schl”

“Meye hadinki dashi?”

Sai data d’an K’are Masa kallo, irin kallon dayake binta dashi sai kace wani tsohon maye yasa tayi saurin d’auke kanta.

“Mutunci ne tsakanina dashi?” 

Ta amsa tana jan tsaki aranta ganin yadda ya fitineta da kallo.

Juyo da fuskar ta yayi saitin tasa ya k’ura mata ido yana mamakin furucin ta lallai ta sauya ba dan kad’an ba tunda har ta kula d boy wanda yagama wulak’anta ta a bainar jama’a.

“Amma baki da zuciya princess, mutumin da ya gama gurza miki rashin mutuncin a tsakiyar makarantar ku ke yamzun har akwai wani mutunci da zai had’a ki da shi?”

Shiru tayi saboda kallon da yake mata ya masifar ta kurata dan har jikinta ya d’an soma rawa rawa.

“Ni kadaina min wannan kallon” ya tsinci muryanta da yayi can k’asa sosai tana fad’a, kallon ya cigaba da binta dashi yayin da ya dad’a kusanto da fuskarta daf da tashi wanda har suke iya jin saukar numfashin juna.

Take jikinta ya kama rawa ta soma k’ok’arin kwace fuskar ta daga hannunsa, sai dai bai bata damar hakan ba dan ya rik’e ta gam

“Babu abinda yafi min dad’i kamar kallon ki kuma hakan yana saukar min da nutsuwa sosai, dan Allah Kar ki haramtamin kallon fuskar ki yin hakan zai cutar dani sosai.

Yanzu kam gaba d’aya ta ware idanunta akanshi Al ‘amarin bross d’in nasu ya fara bata tsoro anya bai samu wani ciwon ba kuwa?

Yadda yake mata d’innan gaskiya ya kamata a bincike shi

“Zaki iya min wani alfarma?” 

Ya tambaya yana cigaba da kallon ta kuma har lokacin bai saki fuskar ta ba,

“To kasakar min fuskana sai muyi maganar”

Kamar zai ce wani abu sai kuma ya fasa ya sake tan kamar yadda ta buk’ata, ya kwantar da kansa jikin kujeran da suke kai yana maida numfashi.

Kafe shi tayi da ido aranta tana mamakin yadda yake da zallar kyau da mugun kwarjini.

Tana tsaka da kare masa kallon ne ya ware idonsa akanta yadda take binsa da kallo ya bashi mamaki

“Yadai yarinya? Irin wannan kallo haka ai sai kisa naji kunya” ya fad’a yana d’an gyara zamansa.

Ai kuwa wani irin fitinanniyar kunya ne ya kamata yadda ya kamata dumu dumu tana K’are masa kallo da k’arfi ta runtse idonta gam gam, yasaki wani murmushi ya d’an matsa daf da ita batayi aune ba sai ji tayi ya sakar mata wani kasalallen kiss a idanunta ai da sauri ta yunk’ura zata gudu bisa ga tsausayi sai taci karo da kayan da Hajara ta ajiye mata tun d’azu, saura kad’an ta kife wajen yayi wani irin fisgota ta fad’o jikinsa, wani irin ajiyar zuciya suka sauke atare.

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button