BA JINI NA BA CE Page 31 to 40

K’ank’ame ta ya kumayi acikin jikinsa yana sauke wani irin numfashi wani irin abu na mai yawo acikin jikinsa ji yai wasu irin hawaye suna k’ok’arin zubo masa wanda bai san dalilin faruwar su ba.
“Zaki aure ni?”
Ta tsinci muryarsa da yayi wani irin mugun sanyi, a wani irin firgice ta d’ago kai tana kallonsa, har lokacin idanunsa a rufe suke gashi ya wani irin cukwaikwauye ta, shikenan hasashen ta ya tabbata yayanta yana da matsala banda haka ina aka tab’a auren JINI D’AYA?
K’ok’arin kwatar kanta ta soma amma ko gezau saima k’ara rik’e ta da yayi
“Ki bari mu fahimci juna dan Allah princess ina son na aureki zaki aure ni?”
Ya kuma k’arasa zancen da tambayarta, jitai hankalin ta yai masifar tashi take maganganu Maryam wanda su yi dad’ewa ya soma dawo mata inda take ce mata
“Da kyar inba sonki wannan bross d’in naku yake ba yadda yai mugun saka miki idonnan da alama dai bazai bawa wani daga waje damar d’auke masa wannan tsaleliyar budurwar ba”
Sanda maryam tai maganar hararan ta tayi tace “da alama kin sami b’acewar tunani name sake banda haka babanmu fa d’aya da kike wannan zancean aman babu tashin zuciya” ta k’arasa tana wani irin kallon Maryam d’in da kuma yin kamar da gaske aman zatayi.
A lokacin murmushi Maryam ta sakar mata tace “ai lokaci zai nuna kuma kinsan lokaci baya k’arya”
“Hmm amma wallahi name sake ban tab’a tunanin kina da tab’in hankali ba sai yau”
“Zaki ce na fad’a miki wallahi kallon SO bross yake miki bana sister ba kuma zaki tabbatar da magana na wata rana”
Ji tai wani irin fad’uwar gaba ya rikito mata lokaci guda ta ware idanunta akanshi tayi wani mugun tureshi da k’arfi ta mik’e daga jikinsa, ta doshi hanyar fita hankali tashe.
Shima ji yai hankalinsa yayi mugun tashi ya bita yana kuranta bata ko juyo ba bare yasa ran zata amsa sai ma wani maganar na Maryam da yake dad’a dawowa kanta a yanzun.
“Ki duba da kyau Ammey batayi shekarun da zata haifi mutum kamar bross ba sai dai ko k’aninta kuma idan kinje gida ki tambayi Mama”
Tsayawa tayi a jikin motar MD ya k’araso yana kallon ta hankali tashe’ yayin da Hajara da m Bash ma suka fito domin yadda MD yake kwala kiran Maryam princess princess ba na lafiya bane sai dai duk nacin m Bash wajen son jin abinda ya had’a su babu wanda ya tanka musu
Da k’yar Maryam ta iya d’ago idanunta da sukayi mugun ja tsabar damuwar daya kawo mata farmaki lokaci guda ta kalli Hajara ta daga mata hannu har da murmushin k’arfin hali tayi mata.
Shi ko MD bai iya yace komaiba ya figi motar da mugun k’arfi,duk da yadda hakan ya kad’ata yadda taga yana musu ganganci da rayuwa, amma bata d’ago ba saima mai da kanta datayi k’asa batare data shiryawa hakan ba wani fitinannen kuka ya kwace mata, wani irin wawan burki ya taka wajen wasu bushiyoyo ya faka ya kafeta da ido kafin a hankali ya d’ago da kanta yana kallon yadda take rusgar kuka sai kace wacce aka ce mata Baffa da Ammey ne suka mutu
“Ki rufamin asiri dan Allah ki tausayawa zuciya ta ki daina kukan nan haka”
Kallonsa ta kumayi yayin da kukan ya dad’a kwace mata wanda shi kukan nata yafi komai d’aga masa hankali
“Pls” ya fad’a a hankali amma ina bata saurare shi ba “dan Allah” ya kuma fad’a a hankali yana d’an janta kusa dashi ya soma share mata hawayen da k’yar yasamu tayi shiru amma bata ce masa kanzul ba.
Har sukaje gida bata k’ara yarda ta tanka masa ba duk irin yadda yake rarrashin ta kuwa,
Yana fakawa ta balle murfin motar tayi cikin gida da sauri ko kayan da suka siyo bata tsaya d’auka ba, binta yayi da kallo har ta shige kafin yasaki wani irin ajiyar zuciya mai k’arfin gaske.
Har lokacin Mama bata dawo ba dan k’ofar ta yana nan a yadda ta barshi da zata fita wani irin mugun tsaki tasaki wanda yasa Ammey dake fitowa daga d’akin ta zata shiga kicin, da kallon mamaki Ammey ta bita ganin yadda tayi mugun fita a hayyacin ta.
“Ke lafiyar ki ‘kalau ina yayan naki?”
Ammey ta k’arasa tana tambayarta ta fad’awa tayi jikinta tare da fashewa da kukan da yake ta cinta, rik’o ta Ammey ta yi hankali a tashe tajata zuwa d’akin ta zaunar da ita tayi abakin gado ta d’ago kanta tana share mata hawayen kafin tace
“Me yafaru, ko wani abunne ya samu yayan naki?”
Girgiza mata kai Maryam ta yi ” to me ya faru?” ta k’ara tambayar ta hankali tashe ” Ammey kece kika haifi Muhammad?”
Maryam ta tambaya tana kafe Ammeyn da idanunta da suka kad’a sukayi jajur,
“Me ya faru da har ya daga hankalin ki haka kike min wannan tambayar? ji dan Allah yadda ki koma ji yadda idanunki yadda suka kubura tsabar kuka, bana san haka karki karamin irin haka ji yadda kika tashi hankalin ki nima kika tayar min da nawa?”
Duk abinda yafaru ta kwashe ta fad’a wa Ammey, wani irin sanyi ne ya kwaranya mata arai ta rungumeta tana fad’in “yanzu ke dan wannan abun kike tayar da hankalin ki ai wannan ba abun tada hankali bane Kinga shikenan zai samu mai kula dashi ko”?
Ammey ta d’igawa dogon sharhin ta aya “kamar ya zai samu mai kula dashi ban gane ba Ammey?”
Eh kinsan Abban ku Hassan?”
Na garin su Inna?”
Itama ta tambaye ta
“Yauwa d’iyar albarka shifa ina d’an sa da matarsa ta haifa ta mutu ta barshi?”
“Ba ance yana k’asar waje karatu ba?”
“An fad’i hakane kawai saboda wasu dalilai amma ba kowa bane face Muhammad”
Idanu Maryam ta zaro duka waje tana kallon Ammeyn da madaukakin mamaki
” Hum shine” Ammey ta fad’a tana daga mata kai ganin irin kallon da Maryam take mata.
Nan ta bata labarin MD kamar yadda Baffa ya bata tundaga haihuwar sa da mutuwar mamansa wanda ko abinda ta haifa bata sani ba da yadda Inna ta raune shi har ya girma da yadda matan banansa suka soma azabtar da shi duk da cewa ba gida day’a suke ba har dai MD ya fara wayo ya daina zuwa gidan har zuwa d’auke shi da Baffa yayi har yanzun da yazama wani abun sosai Maryam taji tausayin sa yayi wani irin kamata Allah sarki bawan Allah shi baima tab’a ganin mahaifiyar sa ba ta ayyana aranta “Allah ya jikanta da rahama” ta fad’a tana share guntun hawayen da ya zubo mata
“Amen” Ammey ta fad’a tana shafar kanta kafin tace “maza jekiyi wanka kiyi salla kinga lokacin ta ya shiga Kuma yanzun hajiya zata iya shigowa tunda magriba yayi kar ta ganki anan”
Batace komaiba ta fice a d’akin.
Taku ce
MAMAN ISLAM
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
???? BA JININA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 32
Tana fitowa daga d’akin daidai shigowar haj. Sailuba, idanunta k’yar abakin k’ofar Ammey dan sam bata son had’uwa da kowa wannan shine sa ar aikin ta na yau tana ganin Maryam da bata kula daga inda ta fito ba ranta yai masifar b’aci babu makawa wannan la’a nanniyar yarinyar ta b’ata mata shiri.
Tsawa ta buga mata tace “ke dan ubanki daga ina kike bana hanaki mu a’mala da wadannan matsiyatan ba?”
Da kallon mamaki Maryam ta bi mama wadda tun kafin ta kai karshen maganar ta ta gano kuskurenta tayi saurin fuskewa dan kar ta gano ta, amma duk da haka sai da Maryam ta hango tsantsar tashin hankali atareda maman tata.