BA JINI NA BA CE Page 41 to 50

“Muhammad yakamata ka gane halin wannan matar ina rok’on ka daga yau komai zai faru kada ka k’ara cewa komai ka barta komai lokaci ne dan haka wata rana sai labari” sosai taci gaba da da tausar shi har ya kammala, itama Maryam ta tubure sai da ta bata itama kafin su bar wajen ta bisu da kallo.
Hannunta da Baffa ya kamo ne yasa ta juyo babu wannan walwalan dayaga tana yima yaranta yanzu, ya d’an murmusa yace “haba maratussaliha dan Allah ki saki ranki tun jiya ake fushi dani na takura da yawa” ya fad’a yana murza hannunta dake cikin nashi.
“Ai Baffa na lura baka Sona ko dan ni ba yar uwarka bace shiyasa kake nuna babanci muraran atsakanin mu”
“Dan Allah ki daina wannan batun Amina ta wallahi nima wani lokacin karkiga yadda abin yake damuna kawai dai tashin hankali ne bana so yasa kikaga ina biye mata”
Amma Baffa shekara ashirin sau d’aya ka tab’a bani kujeran nan ban tab’a cewa dan me ba yanzun ma nagane abin ba na K’are nane dan haka wallahi akan wannan komai zai iya faruwa”
“Dole na baki Amina tunda baki tab’a yi min haka ba sai yau dan haka komai zai faru kece da wannan kujeru na bana” nan dai yaci gaba da tausarta har yasamu ta d’an sakko sukaci abincin tare.
Kai tsaye suna fitowa d’akinta ta dosa dan yau tana buk’atar zuwa gidan su Maryam tana shiga suma suna shigowa yi tayi kamar bata gansuba sai da ya k’araso kusa da ita ya d’an dafa kafad’anta ta juyo ta harareshi.
Murmushi ya d’an saki ya sumbaci goshin ta bai ce komai ya juya ya fice daga d’akin ta raka shi da ido kafin ta juya tacigaba da shirinta.
Taku ce
MAMAN ISLAM
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
???? BA JININA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 34
Cikin atamfa riga da sket kamar ajikinta aka dinka rigar tsabar yadda tayi mata d’as a jikinta, bata wani yi kwalliya mai yawa ba duk kuwa da yadda take da son kwalliyar, mayafin da ya dace da kayan ta dauka ta saka ta saka takalmi mai mugun tsini Allah yayi mata son takalma masu tsini ta fito d’as abinta.
Dukansu juyowa sukayi suka kafeta da ido ba k’aramin kyau tayi ba,kasa daurewa MD yayi sai da ya taso ya d’an matso kusa da ita yace,
“Bakiyi kyau ba” dan hararan sa tayi tace ” ai daman badan kai nayi kwalliya na ba bare ka kushe” murmushi yayi tare da mata gwalo domin yasan taji haushi ai kuwa ta k’ufula ta wani had’e rai, ta juya ta wuce d’akin Ammey karab sai a idon mama da ta fito zata fita jitai wani irin fitinannen tashin hankali yakawo mata farmaki da k’arfi tace “ke gidan uwar wa zakije ne” ta fad’a tana kafe Maryam da wani irin kallo.
Ba Maryam ba hatta MD da Nassar sai da suka zabura suka zuba mata ido, ita ko Maryam babu wani shakka ko tsoro tace “haba Mama wallahi har kin bani tsoro irin wannan ihun haka kamar aradu?”
Wani irin tuk’uk’i ne ya tokare haj. Sailuba ta kafe Maryam da wani shegen kallo zuciyar ta yana suya yaushe Maryam ta sami damar fad’a mata magana haka lallai in batayi wasa ba wata rana sai Maryam ta zageta anata haukan tunanin kenan.
Amma azahir cewa tayi “ni nake ihun bab? wai ma tukun me zakiyo ad’akin matar nan bana hanaki mu a’mala dasuba?”
“Hummm mama kenan ai duk randa babu ke dole itace uwata, ko baki tab’a tunanin hakan bane? kuma kadafa ki manta mama ba a raba hanta da jini mun riga mun had’u babu yadda zakiyi tunda ta haifa kin haifa dole ne itama ta sarara agidanna dan Allah mama ki daina irin wannan abun bashi da amfani ko kad’an haba”
Fashewa kawai haj. Sailuba tayi da kuka saboda tsabar tashin hankali da bak’in ciki kasa yi mata magana tayi har ta shige d’akin Ammey tana kallon ta.
MD kuwa wani irin annushuwane ya kamashi sanda Maryam ke fad’awa haj. Sailuba magana wani arnen murmushi kawai yake saki, yana ganin Maryam ta shige d’akin Ammey ya k’arasa kusa da haj. Sailuba yace “hajajju makkatu me kike tunanin zai faru duk ranar da wannan yarinyar tagane cewa ke ba uwarta bace uwar rik’o ce?
Ya zakiji lokacin da tasan cewa mahaifiyar ta kike sawa tanawa cin mutunci da wulak’anci
Me zai faru idan tasan cewa ba dan Allah kike rok’on taba kina rik’on tane saboda wani banzan dalili naki mara amfani?
Hhhhhhhhhhhh kad’an kika gani Sailuba domin Allah baya bacci”
Babu kunya haj. Sailuba ta kuma fashewa da kuka tana kallon MD kafin tace “hummmm Muhammad kenan na maka alk’awarin bazan bar hakan yafaruba sannan kuma ina Mai farin cikin sanar dakai cewa komai ya kusa zuwa k’arshe rayuwar Maryam zaiyi wulakantar da babu wani rayuwa da zata kai tata lalacewa zata bi maza zata yi shaye shaye zata yi sata zata zama abin kwatance da misali na miyagu da munanan halayya”
Sosai gabansa ya fad’i da jin furucin ta domin yasan zata aikata fiye da hakama jiyai hankalinsa yai masifar tashi ya dubeta da tsantsar b’acin rai yace “Allah ya fiki yafi waninki Sailuba kuma duk abinda kike tak’ama dashi insha Allah hakan ki bazai cimma ruwaba”
Wata shegiyar dariya ta saki tace “zaka gani zaka kuma tabbatar muzuba nidakai shege ka fasa” daga haka tayi waje hankali a tashe.
Sosai maganganun ta suka tsaye masa rai sai dai kamar yadda yake tsaye wajen yiwa Maryam Adda a ya zama dole ya k’ara zage damtse.
Maryam kuwa tana shiga d’akin Ammey ta rufeta da fad’a akan maganganun da taji tana sakarwa haj. Sailuba tace mata koba komai matsayin uwa take awajen ta dan haka ta rik’a sanin irin maganan da zata fad’a Mata.
“Nifa Ammey indai akan kune babu abinda zaki fad’a min na fahimta matar da bata da lokacina sai na gantali kullum tana tafe a hanya ita ba kasuwanci ba ba komaiba, ai wallahi duk laifin Baffa ne da yasake mata haka dayawa shiyasa take iskancin ta son Rai”
“Ungo nan Ammey ta yiwa Maryam tace “idan har da gaske kina ganin mutunci na kamar yadda kika fad’a to kada ki sake kinji ko?”
“Naji Ammey, ina Baffa shi nazo nema”
“Lafiya kike neman Baffa?”
Bata b’oyewa Ammeyn komai ba ta fad’a mata tana son bawa baban k’awarta jarine ya fara sana a, sosai hakan yayiwa Ammeyn dad’i arai taji dad’i ya kasance yarta tana da zuciyar tausayi dan haka Ammeyn ce da kanta ta bawa Maryam dubu d’ari tace “gashi idan Kuma bai isaba kimin magana sai na k’ara miki?”
Rungumeta maryam tayi tace “na gode Sosai Ammey na Allah yaja da rai ta sumbaci Ammeyn tayi waje da sauri tana fad’in saina dawo”
Sosai Ammey ke jin dad’in yadda yarinyar ta soma sakewa da ita ta rage wannan d’an banzan yawon dayake sanyata fargaba da damuwa musamman idan haj. Sailuba ta dawo taga bata nan ko zata kwana basata tuhumeta taji inda taje ba.
Tana fita suka gabza wani uban karo da MD ai kuwa taji zafi sosai shima haka duk suka dafe wajen suna kallon juna kafin Maryam ta galla masa harara ta wuce tana sosa goshinta.
Da sauri yasha gabanta ya tsaya yana d’an diddira k’afa irin na shagwab’a yace”ni Allah Allah Allah sai ki bigeni kuma ki wuce babu hak’uri ni sai na rama” yadda yayi maganar dole abin yabata dariya batasan sanda ta saki murmushi ba tace “sorry”