BA JINI NA BA CE Page 41 to 50

Daga haka ta wuce kuma shan gabanta yayi yace “ina kuma zaki?”
“Gidan su Maryam ta bashi amsa dan har ga Allah sauri take ta tsai da baban Maryam yau baifita nema ba dan haka yakamata taje akan kari
“Wanda kike siyayyar nan awajensa?”
Ta tsinci muryarsa tana shirin fita “Eh shi”
Ta bashi amsa tana ficewa da sauri ya bita ya rik’o hannunta yana kallon ta tace “dan Allah yaya sauri nake sai batamin lokaci kake”
“Muje mana naganshi idan ya cancanta da amanar da kika bashi saiya cigaba da kula da su idan Kuma ba haka ba sai na amso ko?”
Sanin cewa sunyi maganar da Ammey yasa bata musa masa ba suka jera suka shiga motar yaja suka bar gidan.
Maman Islam ce
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
???? BA JININA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 35
Saida tasa kashi suka biya wani spermaket ta d’an musu siyayya, dan Allah yasani hakanan Allah yasaka mata tausayin iyayen Maryam, saboda yak’i nin su da kamewar su hakanan sun iya babun su, dan malam Abdullah mutum ne jajir tacce tsayayye, akan iyakansa bai yarda da zubar da daraja da kimar gidansa ba, haka kuma baya daukar raini ko kad’an dan haka hatta iyalinsa suna shakkar sa saboda sam bai yarda da wulakanta kai ko zubda mutunci ba.
Yadda suke shiga cikin lungunan unguwar yasha mamakin yadda Maryam tasan wajen dan koshi dayake namiji bai tab’a yowa ta area dinba sosai ya rink’a binta da kallo yana mamakin ta.
Sai yanzu yake gane asalin halinta mai kyau ne irin na mahaifiyar ta wancen halin na aro ne wanda aka d’ora ta akai bisa wani dalilin mara tushe da makama.
Ita duk wannan kallon dayake binta dashi sam bata kulaba dan hankalin ta yana kan wayar ta suna chat da Halima sai yanzun ta d’ago dan taga ko sunkai inda ta kwantato masan ai batasan sanda tasaki kara ba ta maida hankalin ta kanshi ganin suna shirin taka wani k’aton dutse, shima da sauri ya taka burkin da sai daya janyo hankalin wasu daga cikin masu wucewa dake cikin unguwa be.
Harara ta galla masa kamar idanunta zasu fad’o tace “to kasheni ka huta tunda ka gaji da ganin rayuwata”
Murmushi ya d’an saki kafin ya d’an shafi fuskar ta yace “ina son ki princess dan Allah ki soni my happiness” hararan ta kuma masa kafin ta d’auke kanta yasa hannu ya kuma juyo da fuskar nata saitin sa ya kafeta da ido,
.”dan Allah ki kalle ni nasan zaki yadda da abinda nake fad’a miki har zuciyana ne” bata musa masan ba ta d’an kalleshi na kamar 1 mint take taji ta fara d’an tsuma tsuma tasoma k’ok’arin kwace fuskar ta amma ya hanata damar hakan da sauri ta runtse idonta dan bazata juri kallon wannan fitinannun idanun nasa ba.
Murya na rawa tace ni kaina ya k’age ka sakar min fuskana, kuma ka daina yimin wannan kallon mayun” murmushi ya d’an saki kafin yace “indai akanki ne baby ki kirani lasan ma ba maye ba da da yadda zanyi na tsaga jikina na sakaki da tuni na jima da yin hakan na huta’ dan Allah baby karki gujeni, idan kika gujemin hakan yana nufin abubuwa da yawa ciki harda rayuwana”
Yanayin da yayi maganar yasa dole ta kara bud’e idanunta akanshi yadda taga idanunsa sun koma ba k’aramin tsoratata abin yayi ba sunyi wani irin mugun ja ga wani kyalli kyalli alamun ruwan hawaye ne suka kwanta masa aciki, wani irin tausayin sa ne ya kamata tace
“Zaka iya aurata koda ace bana sonka?
Sosai maganar ta ya dakeshi, zaka iya aurata koda ace bana sonka?
ya sake maimata tambayar a zuciyar sa kenan akwai wanda take so Kennan tunda bata son shi?
Wani irin ajiyar zuciya ya sauke kafin yace
“Baby wa kike so?
“Babu”
Ta bashi amsa atakaice sannan ta d’ora da fad’in ba kaine kakori muhseen ba yaron dayake masifar Sona kamar zaiyi hauka tundaga ranan yake masifar tsorona bama kaiba ko a hanya ya ganni wallahi canja hanya yake”
Sosai maganar ta ya masa zafi a zuciya amma sai ya daure tunda shine mai nema dole ya sauke duk wani zafin ransa gefe ya nemi masalaha
“Kina son muhseen d’in?
Ta tambaye ta cikin tsantsar zafin rai dana zuciya.
“Ni babu wanda na tab’a jin ina so arayuwata shima muhseen d’in saboda nacinsa da rashin zuciyar sa yasa na tausaya masa na fara kulashi” baisan sanda ya wani fisgeta ta fad’a jikinsa ba ya wani k’ank’ame ta atare suka sauke wata irin ajiyar zuciya kafin yasoma magana cikin sanyin da shi kansa baisan zai riskeshi a wannan lokacin ba yace
“Na amince baby zan aureki koda ace bakya sona nasan dole wata rana zanyi nasara zan mallake ki KE DA ZUCIYAR KI”
“Ya jima yana zubar mata da sak’onnin da suka cunkushe masa zuciya suka hanashi sukuni, bai tab’a sanin da akwai rayuwa irin wannan ba rayiwar da zaka kasa katab’us ka kasa sukuni ba sai da ya had’u da jarrabar SO wanda ya hanashi sakat yake sanyashi kasa baci cikin dare ya kasa runtsawa tsawon dare ya zubda hawaye ba adadi duk asanadin SO”
Tun bata fahimtar maganganun sa har ta fara fahimta sanadin da jikinta yayi sanyi bata san da cewa akwai ranan da MD zai iya kallon idanunta ya furta mata tsadaddun kalamai irin wannan ba musaman idan tayi tunanin yadda suke da shi.
“Bross muje na tsaida bawan Allah yanata jira” tayi maganar cikin sanyin jiki dan kalaman sa sun mugun kashe mata jiki sai da ya sumbaci goshin ta da idanunta da suka fi komai d’aukan hankalin sa kafin ya saketa ya tada motar suka k’arasa gidan su Maryam d’in.
A mota ya tsaya ta shiga kamar yadda ta zata Abban yana nan yana jiranta kamar yadda ta nema Umma ce tayi mata shimfid’a ta kawo mata ruwa da lemo, sai da ta gaida su sannan ta sanar musu ai tare suke da yayanta Abba yace “kuma kika barshi awaje kai wannan yara Allah ya shirye ku da rashin wayo”
Ya fita ya shigo da MD duk da kasancewar basu dashi amma yayin gidan kad’ai zai nuna maka mutanen gidan suna da tsananin tsabta, sosai suka gaisa da su kafin Maryam tayiwa Abban bayanin dalilin zuwansu, hakan ba k’aramin dad’i yayi wa Abban na ya zauna yayiwa MD bayanin duk abinda aka sai mata da kud’ad’en da take kawowa harda shanu da yaje can garinsu yasai mata da yake shi ba d’an garin bane.
Yanayin sa kawai yasa MD yaji hankalinsa ya kwanta da shi dan haka suka d’anyi shawarwari akan abubuwan nata yace “tunda shanun sun kai har guda goma kuma duk Yan k’anana wanda basu fara haihuwa ba kawai asai na mijin sa kamar guda biyar a had’a sai abada kiwo ga wanda ya amincewa.sannan gidajen kuma anemi yan haya masu mutunci da amana asaka su aciki”
“Nima tun farko shawaran da nayi da ita kenan tace in dakata tukun” murmushi MD yayi yace “kasan yar k’auye ce babu abinda ta sani sai k’auyanci” shima Abban murmushin yayi yace ” banda abinka d’ana ai k’auye tushen kowa ne shima MD murmushin yayi suka ci gaba da tattanawa, sun jima a gidan har sanda Maryam ta dawo suka suka shige d’aki dake sanda sukazo bata nan Umma ta aike ta.
Umma ce ta lek’a tacewa Maryam ta fito zasu wuce sai da zasu tafi sannan Maryam ta kawo k’udin da Ammey ta bata ta mik’ewa Abba tace
“Abba gashi nan ka nemi wata sana ar ka fara Allah ya taimaka.