BA JINI NA BA CE Page 41 to 50

Tsabar mamaki Abba kasa magana yayi gashi kuma ta toshe duk wata hanya da zai mata godiya sai addu’ar da yay ta zuba Mata har suka bar gidan
MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
???? BA JININA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 36
Suka shiga mota ya tada suka bar wajen saida suka d’an yi nisa da tafiya kafin ya d’an juyo ya kalleta ” enye enye ashe yarinyar tana da hankali, to nima aban jarin mana”
Murmushi kawai tayi tasan tsokanar ta yakeyi dan haka ta d’auke kanta suna cigaba da chat da Halima wacce take zaman jiranta a gida.
“Ko bazaki baniba?” Ya sake tambaya, hararan wasa ta d’an yi masa ta dauke kanta tana d’an murmushi.
Haka dai yai ta janta da hira har suka koma gida kai tsaye d’akin ta ta wuce shima fat d’in sa ya nufa dan duk sun gaji.
Ita kam tana shiga falon ta tadda Halima tana zaman jiranta hararar wasa tayi mata tace ” to hajiyata shanyar taki ta bushe Allah badan gobe zan koma ba da tuni nayi tafiyata”
“Sorry dear gidan su name sake mukaje bamu tadda taba har sai da muka jira ta dawo”
“Naji kina jam u kedawa?”
“Tare da bross mana” wani irin waro ido Halima tayi tace “kedawa?”
Kunsan fa Halima bata da masaniyar shirin Maryam MD domin bata da yawan surutun mara dalili.
“Ai kinji abinda nace kema neman zance ne kawai irin naki”
“Ai abunne dole yabani mamaki yadda baku shiri da bross kuma kice tare kuka fita ai kinsan dole mamaki yamin illah”
“Humm wai kinsan ma wani abu kuwa?”
“A’a”
“Wai sona yake karkiga yadda yakemin naci kamar bashi ba duk ya wani susu ce”
“Ke dan Allah dena fadaymin dama ba babanku d’aya ba?”
Ta fad’a duk idanunta awaje tsabar mamaki
“To ni tsabar tsorata ranan da yace yana sona ihu na dinga zunduma masa nayi tunanin kwakwalwan sa ne ya tab’u wallahi”
Jinjina kai Halima tayi tace “haba wallahi wani lokacin nakan zauna nayi tunanin yadda Ammey take ba wata babba ace ta haifi kamar bross da ace kece akace yarta babu wanda zai yi mamaki ammafa bross abin yana d’aure min kai, ke amma kinsami dami akala wallahi na miki murna bross ai miji ne na yaw……..
“Ke dalla rufewa mutane baki zaki fara halin naki babu fullstop ba qommer nace miki ina son sane da zaki wani fara yyyyyyyy murya kamar ta yan China”
Harara Halima ta galla mata tace “ank’i a rufe banza mara mutunci ai dama inka shekara dubu bakaga mutum ba tambaya halinsa ni zakiwa iskanci koda yake ni na kawo kaina bari nay tafiyana”
“Jeki mana seme dama duk kin isheni kin saka min ciwon kai”
Sai da sukayi halin naau da suka saba duk had’uwa kafin su daidaita su hau zance na gaskiya da gaskiya, wannan halin nasu tun suna yara suka taso fashi Halima surutu ratata Maryam kuma fad’a.
Sun jima sosai Maryam ta fad’awa Halima gaskiya itafa bata son MD Halima tace “karki damu yar uwa wata rana zakiso shi har kiyi kishin sa kawai dai mudage da addu’ar Allah ya zab’a mana abinda yafi alkhairi amen”
Sosai Halima tabawa Maryam shawarwari masu kyau yayin da sukayi sallama dake hutunsu ya kare zata koma schl itama Maryam d’in sati mai kamawa zata koma.
Tsakanins Maryam da Halima akwai so da k’auna akwai yarda da amana akwai shak’uwa mai tsanani wanda yasamo asali tun suna yan yara alokacin basa rabuwa kullum suna tare ay fad’a a shirya kullum basa gajiya da dambe da f basa b’oyewa junanau duk wani abu har kawo wannan lokacin.
Name sake d’in ta kuwa k’awance ne irin na makaranta sannan babu abinda tasani akanta banda mahaifinta da tasan mai k’udi ne dan har yanzuma bata bata damar zuwa gidansu ba dan Maryam bata jan mutum ajiki sai ta gama karantar waye shi, itama dai bata da wani aibi tana da kirki ga kamewa wanna neyasa Maryam k’ulla kanwace da ita har takai ga tafara temakonta.
Bayan tafiyar Halima Maryam tayi wanka ta fito duk a dining room ta samesu har Baffa sai mama da har wannan lokacin bata dawoba, kujeran kusa da Baffa ta jawo ta zauna suka sakashi atsakiya ita da Nassar yayin da Ammey tata kujerar ke kallon ta Baffa “ke uwar taki bata fad’a miki inda ta tafi ba yau gashi har anyi issha?”
Dan yamutsa fuskar ta tayi itama yawon na mama yana mugun damunta tace “zai wuce gidan waccen haj. Zakiyyar ni bata fad’a min inda zata”
Kwafa Baffa yay cikin b’acin rai kafin yace komai MD ya shigo wanda gaba d’aya kamshinsa ya cikasu kujeran dake kallon ta Maryam ya ja ya zauna ya wani kafeta da ido ko kunyar su Baffan bayaji.
Tana ganin haka ta wani tsare gida yayin da Baffa yace “zamu yi magana daku keda Sailuba idan ta dawo a yawon nata”
Had’e rai Ammey tayi amma bata tanka ba yayin da Maryam ta sunkuyar da kanta k’asa tak’i yarda koda wasa ta kalli inda MD yake shikam ko ajikinsa ya fitineta da kallo yana cin abincin sa, bata wani ci abin kirki ba saboda yadda ya takurata ta mik’e , Ammey ta dubeta tace “ya haka baby banason fa zama da yunwa”
Had’e rai tayi tana hararan MD k’asa k’asa tace “k’oshi nayi ne” daga haka bata jira cewar suba ta bar wajen, duk suka bita da kallo, shima MD kad’an ya k’ara ya mik’e direct d’akinta ya wuce ilai kuwa ya sameta tayi d’ai d’ai asaman gadonta da ice cream tana faman sha sam bai ma kula da abinda takeyi ba sai da ya buga uban sufa ya fad’a kusa da ita sannan ya kula da kayan sanyin da take sha k’ala bai ce mata ba ya zare robar a hankali ya kai saman frich ya aje ya dawo ya kuma kwanciya tareda d’ora kansa saman kafafunta a wani firgice ta kai idanunta saman fuskar shi idanunsa ma shi a lumshe suke take jikinta ya kama wani irin rawa cikin tsantsar tashin hankali da rawan murya tace me mey meye ha ka ni fa ban a son is Kan ci tayi maganar a rarrabe tsabar tashin hankalin data shiga, wani muskilin murmushi ya saki yace
Muje zuwa daga
MAMAN ISLAM
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
???? BA JININA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Gaisuwa ta musamman gareku hazikai kuma jajurtattu a kungiyata
Princess Aisha
Miss flower
Maryam H
Allah ya kara muku juriya da hak’uri. Allah ya kara had’e kanmu first class mu dad’e muyi k’arko ????????????????????????????????
Page 37
“Nine d’an iskan princess?” Ya fad’a yana kallonta ko k’ibtawa bayayi had’e rai tayi tareda fashe wa da kuka maimakon ya saketa kamar yadda take buk’ata sai kawai ya rungumeta take zuciyar ta yayi wani irin mahaukacin buga ta fara k’ok’arin tureshi amma ina k’arfin ba d’aya bane.
“Na tsaneka” ta fad’a cikin kuka sakinta yayi a firgice yace “ni d’in baby ni Muhammad dinki kike cewa kin tsana?”
Harara ta galla masa da idanunta da suka koma launin ja ta murgud’a masa baki ta fice daga d’akin tayi d’akin Ammey wacce itama bata d’akin ta fat d’in Baffa.
Bata jima ba Ammey ta shigo hannunta d’auke da Leda da kaya aciki Nassar na biye da ita yana mitar ta hana Baffa siya masa ways.