BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 41 to 50

Da kallo tabi Maryam wacce ta takure waje d’aya asaman gadonta, kana kallonta kasan akwai abinda yake damunta “Ammey zoki zauna dan Allah muyi magana” tayi saurin katse Ammey tun kafin tayi mata tambayar da bata da amsa,

A hankali Ammey ta tako kusa da Maryam tasamu ta zauna ita kuma tayi saurin d’ora kanta ajikinta tana sauke ajiyan zuciya sannan tace “Ammey zan iya auren MD?” ta fad’a kamar yadda ta tab’a jin m Bash ya kirashi da sunan

Gaban Ammey ne yai masifar fad’uwa a d’an razane ta dubeta tace “waye kuma hakan?” Ganin yadda tayi saida tai mugun bata dariya kafin tace “Muhammad dinki nefa MD nima abokansa naji suna fad’a shine na d’ana” ta fad’a tana b’oye face d’inta ajikinta.

Wani irin sanyi Ammey yaji har batasan sanda ta rungumeta ba tace “zaki iya mana baby me zaihana ai bazaki tab’a samun kamar saba kamilin mutum managarci wanda yasan darajanki”

“Oh ji Ammey saboda shi d’in na wajen kine kike irin wannan zuzuta shin?”

Dariya Ammey tayi ta lakace mata hanci tace ba haka bane baby ai d’ana d’aya ne tamkar da dubu nasan shi nasan halinshi yana da halin kwarai zakiji dad’in rayuwa da shi domin yana da kyautawa”

“Shikenan Ammey tunda kema kin amince da nagartar sa naji na amince zan aureshi kamar yadda ya buk’ata amma fa na sanar dashi cewa bana sonshi hasali ma ni ban tab’a jin sonsa araina ba kamar yadda babu son kowane d’a namiji a zuciyana, to yace yaji ya amince shikenan magana ya kare” daga haka ta mik’e dan fita daga d’akin Ammey ta bita da kallo har ta fice ba k’aramin farin ciki ta tsinci kanta aciki ba duk da cewa maganar ta na k’arshe bai mata dad’i ba.

Ba k’aramin mamaki tasha ba ganin har lokacin MD yana d’akinta akwance ya wani yi mata d’are d’are asaman gado kafeshi tayi da ido tana k’arewa baiwar ubangiji kallo MD ba k’aramin mai kyau bane ta ayyana hakan cikin ranta.

A hankali ta k’arasa rufe k’ofar ta tafi cikin sand’a tana lek’a fuskar shi ya kuwa fisgota da k’arfi ta fad’a kanshi ta bud’a baki zata zunduma ihu yayi saurin toshe mata bakin da hannunsa, tashi yai ya zauna itama ya zaunar da ita suna kallon juna yadda tayi wani tsuru tsuru da ita abin yaso bashi dariya sai kawai ya murmusa baice komaiba ba sai faman kallonta yake.

Yadda yake faman kallonta ba k’aramin takura ta yayi ba ta wani had’e rai tana tura baki bakin ya sumbata ta wani zaro idanu tana kallonsa da k’yar tace “Allah saina fasa aurenka idan kanamin irin wannan abun”

“Yi hak’uri my happiness na daina, amma kisani iya hakan ma ba k’aramin kokari nake ba princess sonki yamin illah bansan lokacin da sonki yayi min irin wannan kamun ba yabi jinin jikina ya mamaye JININA ba dan Allah ki zauna dani koda bakya sona zanfi samun nutsuwa idan kina kusa dani” daga haka bai jira cewar ta ba ya sumbaci goshin ta ya sauka yafice daga d’akin, binsa tayi da kallo kafin ta saki murmushin dabata san ko na menene ba asarari Kuma tace “maye kawai” sai kuma ta shek’e da dariya tana buga cinya.

Cikin sauran kwanakin hutunsu ba k’aramin hanata sakat MD yayi ba tun tanajin haushin sa har ta fara sabawa ya masifar nanuk’e mata duk inda zata sai ya bita matuk’ar yana gida idan ya fita office kuwa kafin ya dawo tana samun kiransa fiye da ashirin tun tana jin haushin sa har ta daina saima wani mugun shak’uwa da yafara shiga tsakaninsu sosai ta fara kamuwa da son MD batare da tasan hakan ba ita dai tasan cewa muddun yana nesa da ita ta rik’a kewar sa in yana kusa da ita kuma tana samun nutsuwa da farin ciki bata gajiya da daddad’an kalaman shi masu sanyata nishadi.

Cikin haka hutunsu ya kare suka koma makaranta karatu suke babu sauk’i kasancewar suna shekaran su na k’arshe hakanne yasa Maryam bata da sukuni har rama ta somayi duk da kasancewar tana samu temako daga MD dan shima idan baku manta ba saida ya fara karatun likita kafin ya koma ya zama soja.

“Na fad’a miki kiyi hak’uri ta k’arasa karatun kafin na tarwatsa komai”

“Bazan iya ba boka itace fa ta wargatsa min shirina na shekara ashirin da d’aya shirina na tundaga ranan haihuwar ta har zuwa yau boka badan ina tsoron rayuwar kurkuku ba da wallahi da hannuna zan kashe ta kamar yadda ta kashe min farin ciki na”

Shi kenan tunda kince haka amma kada kiyi kuka dani duk abinda yafaru ki kuka da kanki kasancewar idanunta sun riga da sun rufe tace taji ta gani kuma ta amince.

“Boka ana gama mata aikinta nima nawa yasamu kamar yadda muka alk’awarta”

“Ke zakiyya burinki zai cika kuma Deedah bata da irin halin ki gaskiya tana da wankakken zuciya amma fa wannan buri naki ba makawa zai cika sannan kuma komai zai wargatse”

Maguguna ya had’a musu tare da fad’a musu yadda za ayi kamar yadda aka saba sosai taji dad’in shirin su na wannan lokacin.

Suna fitowa haj. Zakiyya ta dubeta tace “maganar mu na zuwa India?”

“Yana nan amma ba yanzu ba sai komai ya kammala sai kawai nayi b’atan dabo aneme ni arasa koya kikaga?”

Suka shek’e da dariya haj. Zakiyya tace Allah k’awata kinsan takan tsiya kina ta sha’aninki hankali kwance”

“Inafa kwanciyar hankali buri bai cika ba ai CIKAR BURINA shine kwanciyar hankali na”

Haka suka tafi suna hiransu na mugun abu har suka cimma inda suke faking idan sunzo

Wannan karon zuwan bazata Baffa yay musu sai ganinsa kawai sukayi ranan ma Sailuba taje yankan busa dan tafiyar su yana ta matsowa kai ranan Baffa ba k’aramin ruwan tujara ya zubar ba ya addabi Ammey da fitina wai duk laifin tane da bata sanar masa abinda ke faruwa.

Cikin b’acin rai Ammey tace “kaga malam kada ka isheni ni nake aurenta da zan samata ido?

Tsayama da zakace haka naga agaban kama ficewar ta takeyi kataba cewa dan me saini daka raina zakasa agaba da bala i wallahi nagaji kar ka k’ara sakani a shirgin ku da matarka matuk’ar kana son zaman lafiya a tsakaninmu idan Kuma tashin hankalin kake so nima na iya”

Daga haka ta bige zaninta tabar masa wajen cikin b’acin rai, shima yasani k’ureta yayi shiyasa ta zage yau take mayar masa da martani.

Muje zuwa

MAMAN ISLAM CE

بسم الله الرحمن الر حيم

*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

   FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*________________________

???? BA JININA BACE????

2021

                  NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 38

“Dad dan Allah ka taimaka min na rasa yadda zanyi na fad’awa yarinyar nan irin son da nake mata gashi saura sati biyu mugama karatun mu kasan tare zamu gama dan Allah dad kayi min rai”

Wani mugun kallon Abba AL HASSAN ya jefawa d boy kafin yace “kaga Kamal ka fita daga idona na rufe karaba ni da wannan shed’anin yaron dan wallahi ko mata sun kare a duniya bazan bari ka auri wannan yarinyar ba yayanta da kake gani ba k’aramin aljanin mutum bane bashi da mutunci ko kad’an d’an iska kamar mai gani har hanji duk sanda kayana suka shigo saya yajamin babbar asara”

Fashewa da kuka d boy yayi dan har ga Allah yana masifar son maryam ga Dad d’in sa idan yakafe akan abu shegen taurin Kaine dashi.

Mahaifiyar sa ya kalla yana kuka sosa yace “mammy dan Allah kisa baki dad ya barni da wacce nake so”

“Uwata ce ita da zatasani yin abinta banga dama ba dagakai har Maimunan wallahi sai na had’a ku naci kaza kazanku” ya antayo musu wani zagi mai rai da lafiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button