BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 41 to 50

Take ran haj. Maimuna ya b’aci ta kasa daurewa tace “ka daici naka uban me na maka kaji nashiga maganar ku bare ka dagamin hankali tsabar neman fitina kasan bazaka tab’a min in k’yale kaba wallahi tunda kai mutumin banza ne mara mutunci kawai”

“Iyayen kine marasa mutunci yar marasa tarbiyya wadda batasan girma da martaban na gaba da ita ba”

“Iyayen kadai sune iyayen banza suna kallon d’an su yana hark’allar miyagun k’wayoyi amma basa iya tab’uka komai tur da iyaye irin naka wallahi, ni kuwa iyayena sun bani tarbiyyan da har ka gani ka yaba kuma ka aure”

Nanfa rigima ta balle harda mare mare dan haj. Maimuna bata ragawa Abba AL HASSAN ko kad’an tunda ta fahimci tantirin d’an duniya ne ga zagi nacin mutunci.

Cikin fushi d boy ya fice yabar musu gidan yana hawayen bak’in cikin wannan halin na iyayen sa wanda ko kunyar idanunsa basaji idan fitinar su ya motsa.

Tun bayan da ta shige d’akin ta Baffa bai karajin d’uriyar taba ya tabbatar da fushi tayi, maganar gaskiya yana mugun tsoron fushin Amina dan bata iya fushi ba idan tayi masa fushi yana matuk’ar shan wahala.

Yana shirin tashi yabita har d’akinta haj. Sailuba tana shigowa fasa tashin yayi ya koma ya zauna ya kafeta da ido, ganin irin kallon dayake binta dashi yasa ta d’an sha jinin jikinta sai ta wayance da fad’in

“La Baffa yaushe ka dawo irin wannan dawowa haka babu sanar wa? sannu da zuwa” nan dai tahau masa borin kunya.

Shi kam k’ala baice mata ba kafeta kawai yay da Ido hukunci yake mata da haka, yayin da ta rasa yadda zatayi, sai da ya tabbatar da yagama sanyaya mata jiki sannan yace.

“Waye naki agarin nan da har kullum bakinan me kike fita yi ko me kike nema wanda baki sameshi anan gidan ba?”

Shiru tayi ta kasa magana sai faman rarraba ido take yayin da Baffa yaci gaba da cewa “maganar gaskiya Sailuba wannan shegen yawon gantalin naki ya isheni haka idan kuma baki gyara ba zan d’auki mummunan mataki akanki”

Hak’urin munafurci taita bashi har da kukan k’arya kafin yace ya hak’ura sannan ya d’ora da fad’in “tunda gobe weekend ne ki sanar da Maryam ta shirya zamu wajen Inna” 

A mugun firgice ta d’ago tana duban Baffa yayin da maganar boka yafara kara kaina cikin kunnen ta kamar yanzu yake fad’a mata kar ta sake ta yarda Maryam ta had’u da Inna domin akwai babbar matsala ga had”uwar ta tasu domin Inna zaya ruguje musu komai ta yadda har abada bazasu tab’a nasara akanta ba kamar yadda har yau har gobe suka kasa akan Nassar domin akwai dafa in datake bashi yake sha.

“Lafiya wai me kike nufine Sailuba da hana maryam kusantar mahaifiya ta idan ke kin gujeta so kike yata ma ta guje rabon Maryam da taje garin nan tunda aka yayeta sai dai idan Innan ce tazo ta ganta so kike ki raba yata da mahaifiyata be?”

Cikin dauriya da k’arfin hali tace “a a Baffa ni wacece da zan raba baby da Inna naga nima Innan nan uwatace dan Allah ka daina yimin irin wannan bahaguwar fahimtar”

Nan dai ta kalalleme shi da dad’in baki har ya sauka daga fushin daya dauka sannan ta wuce d’akinta da tarkacen da tazo dashi daga wajen bokanta.

Karfe shida daidai ta dawo daga makaranta a mugun gajiye ga d’an banzan yunwar da ta kwaso tsabar yunwar har wani jiri jiri take gani ta fito a motar ta tana had’a hanya, shima MD shigowar babu dad’ewa wanka yai ya fito ya hango ta tana takawa kamar mai koyon tafiyar murmushi ya d’an yi kafin ya taka a hankali zuwa inda take ya d’an hura mata iska a fuska a d’an tsorace ta juyo dan bata ji zuwansa kusa da itaba tsabar bata nutsuwar ta jarrabawan yau ya azabtar da su fiye da tunanin mai tunani.

Kallonsa tayi da lumsasun idanunta wanda tsabar yunwa yasa suka wani d’an shige “me yafaru happiness naganki haka?”

“Yunwa” tace dashi tana dafe cikin ta da ya isheta da k’ugi “ayya baby muje ciki maza Ammey tagama tuwon dare” da sauri ta kalleshi “Allah tuwo tayi? kasanfa ina son tuwo sosai” d’an murmushi yayi danshi tsokanar ta yakeyi yayi zaton irin Nassar ce itama batason tuwo kamar sa.

“Tsokanar ki nake Baffa kawai Ammey tayima”

” Ai kuwa nima tuwon zanci yasin” ta wuce kanta tsaye dining room d’in, saida ta fara had’a ruwan zafi ta gasa cikin ta kafin ta bud’e tuwon Baffa da Ammey tagama shiryawa gwanim ban shi’awa ta d’auki malmala tasa aflat ta zuba miya ta soma ci a nutse, duk da bak’ar yunwar dake damunta hakan baisa ta rud’a kanta tayi irin cin yunwar nan ba, Ammey da ta shigo dan daukar abincin Baffa tsayawa tayi tana kallon Maryam dake aikawa da tuwo batare da tasan cewa Ammeyn tazo wajen ba, sai data k’arasa wajen Maryam ta ganta tayi wani wuri wuri da ita can kuma tace “wallahi Ammey bross ne yace kinmin tuwo”

“Na tambaye kine?”

Ta fad’a tana wurgawa MD harara wanda yake gefe yana d’an murmushi wayarsa a hannu yana faman daddannawa, bata k’ara magana ba ta d’auki d’an kwandon data jera abincin tayi waje MD ya dungure mata kai yace” da so kikai ki had’a ni da uwata ko?”

Bata ce komai ba sai harara data galla masa taci gaba da cin abincin ta sai data jita daidai kafin ta mik’e tana hamdala tawuce kai tsaye d’akinta ta nufa wanka tayi ta yo alwala tayi sallar la ‘asar da ya k’wace mata tun a hanya ta jima tana addu’o’i kafin ta kama karatun Al qura ani mai girma da fita tasoyi d’akin Ammey ganin lokacin magriba ya karato yasa bata fitan ba ta jima tana karatun kafin a kira magriba tayi addu a ta tashi kawo sallar magriba bata bar wajen ba saida tayi issha Nassar ya shigo da murnan zasu gidan yayar Ammey wacce take sonshi “Adda zaki?” 

Harara ta aika masa tace “bazani ba d’an rainin hankali da dani kuke zuwa?”

Nan dai ya fitineta da hiran anty shamsiyya wacce suke kira da momma har dai ya ja arayinta tace itama zata cikin farin ciki ya daka tsalle yay waje kaiwa Ammey labari, itama ba k’aramin dad’i hakan yayi mata ba ko ba komai anty shamsiyya zatasan cewa ansami cigaba kenan.

Ita ko Maryam Nassar yana fita ta mik’e ta wuce d’akin Mama mamaki ne ya kamata ganinta cikin damuwa ta k’arasa ta kwantar da kanta saman kafad’ar ta tace “Mama lafiya na ganki cikin damuwa ko baki da kud’i ne?”

Wani k’ululu ne ya tsayewa haj. Sailuba jin tambayar da Maryam tayi mata, amma sanin cewa ita ce silar d’ora ta akan hakan yasa tace mata “eh kina dasu ki bani?” Girgiza mata kai tayi tace “ai tunda naga yanzu Baffa ya bud’e miki bakin aljihu fiye da kima yasa na daina tambayar sa k’udi domin nasan cewa idan kina dasha nima inada shi kuma wanda kike bani ma yanzun baya isana saboda wani saurayi danayi d’an talakawa ne sosai shi nake kashewa” da gayya tayi mata wannan zancen dan son gane asalin gaskiyar batun MD dayace wai maman ta uwar ta bata ki taga ta saida mutuncin ta ba,kimar tafa tak’amar kowacce budurwa mai ji da son kara Martaba da kimar ta har zuwa gidan aurenta.

Ga mamakinta ta kuwa bud’ar bakin mama sai cewa tayi “ni dai duk abinda Zaki aikata kada kisake ki kwaso ciki ki rik’a amfani da matakan kariya”

A matuk’ar firgice Maryam take kalloan haj. Sailuba jikinta har rawa rawa ya soma dan tsabar mamaki kasa magana tayi saima tunanin da ta soma aranta na “anya wannan uwa tace kuwa?”

Da k’yar ta iya ce mata daman nazo ne dan Allah Mama ki barni naje garin da momma take Nassar yace kwana d’aya kacal zasuyi dan Allah……katseta Mama tayi cikin sauke ajiyar zuciyar samun mafita na kaucewa tafiyar ta da Baffa zuwa wajen wannan jarababbiyar tsohuwar tace “sai kun dawo” mik’ewa tayi k’udin da takawo mata sai da ya girgiza ta ta amsa yau ko godiyar batayi mata ba ta fice kai tsaye d’akin Ammey ta nufa har MD ma yana can ta mik’ewa Ammey k’udin ta fashe da kuka tace “wai mama ce take cemin duk abinda zanyi kada na d’auko mata ciki anya uwata ce kuwa dan Allah Ammey ki fad’a min itace ta haifeni?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button