BA JINI NA BA CE Page 51 to 60 (The End)
Gaban ta ne yay wani irin fad’uwa jin Ammey na kiran mutuwa sai take jin kamar mutuwar zatayi ta d’an dubeta a sanyaye tace “Ammey bangama jin d’umin ki ba ban gama sabawa dake ba insha Allah bazaki mutu yanzu ba sai mun tsufa kin ga ‘ya’ya da jikoki na”
“Kayya’yar nan ita mutuwar ai intazo bata sallama sai dai kawai kiji tayi wuf da mutum fata dai Allah yasa muyi kyakykyawan k’arshe”
Jiki a san yaye tace “amen” duk sai taji hiran yafita daga ranta dan haka ta lumshe idanunta kamar mai bacci yayin da k’irjinta yake d’an bugawa sai ta kasa nutsuwa daga hiran da sukai da Ammeyn.
Ba k’aramin farin ciki momma tayi da ganin Ammey da maryam ba lallai ta ga sauyi tattare da ‘yar uwar tata rungumeta tayi tsantsan a jikinta duk k’arfin zuciya irin na momma sai da tani hawaye ya cika mata idanu ta d’ago Maryam a jikinta ta manna mata kiss a goshinta da gefen fuskar ta tana jin wani irin farin ciki da k’aunar ‘yar k’anwar tata.
Tana rike da hannun maryam suka shiga k’aton falon momman wanda ke d’auke da wasu had’ad’d’un kukeru masu kyau da numfashi.
Shigar su yayi dai dai da ahigowar yaran mamma ‘yan mata guda biyu saiga k’aramar sun nanma ta shigo tana kukan wai sun barota amota babu wanda yabi ta kanta suka shige da gudu suka rungume maryam dan sun santa sosai a hoto duk da cewa tun tana yarinya ne irin wanda Ammey take fakar idon haj. Sailuba tayi mata, amma Kuma ai ga kama nan domin babu ta inda Maryam tabar Ammey.
Ita kanta Maryam tayi matuk’ar farin cikin had’uwar ta da su yayinda wani irin so da k’aunar su yayi ma zuciyar ta kamun farat d’aya.
Nanfa falon ya gauraye da hayaniyan su dan maryam dama can bata da bak’unta dan haka ta sake a cikin su suna kwasar shafta sannan Kuma duk wanda yay mata ta mangare shi kunsan babyn ba hak’uri????????
Hakan ba k’aramin nishad’i yasaka momma ba hatta abinci ita ta rik’a bata a abakin ta da k’yar su mardiyya sukayi nasaran janye maryam zuwa dakinsu.
Haj. Shamsiyya yayar Ammey ce inajin nayi muku wannan bayanin tun farko itama mijinta babban d’an kasuwa ne yana da rufin asiri mai yawa dan shima Allah yayi masa farcen susa
Yaran ta biyar na farkonta ‘yan biyu ne duk maza Abdul Malik, da Abdul jabbar, dukan su sanyi aure da yaransu, sai Fadeela itama yanzun haka yaranta biyu dan tun kafin auren Ammey aka haifesu da wayon suma akayi bikin Ammey da Baffa.
Daga bayan sun fidda rai da sake samun haihuwar ne kuma Allah ya sake bata wasu ‘yan biyun duka mata Mardiyya da Fauziyya sai autar su Hanifa wacce itama ak’alla su mardiyya sun bata kusan shekara goma dan duka yanzune suke shirin zana jarrabawan su na shiga jami’a.
Suna barin gidan Ammey ta dubi haj. Shamsiyya sai hawaye shar shar haj. Shamsiyya ta dubeta tace “a yada haka Kuma?
Memakon ki farin ciki ki godewa Allah ‘yarki ta dawo gareki” rungumeta Ammey tayi tace anty sai kuma ta kuma fashewa da kuka.
Sai da taci kuka sosai kafin ta d’ago daga jikin’yar uwar tata kafin tace “anty dan Allah idan na mutu kada kibar Nassar a hannunta zata gur b’ata masa rayuwa” K’are zancen cikin zubowar wasu sababbin hawayen.
Had’e rai haj. Shamsiyya tayi tace me kuma ya kawo zancen mutuwa ana zaune kalau kadama ki sake wannan maganar insha Allah tare zaku girma da yaronki har kiga auren shi”
“Karki ga yadda ta tsaneni tana yarinya karkiga halin dana shiga akan ta naci wuya anty yau zan fad’a miki abinda baki sani ba, INA DA CIWON ZUCIYA, duk a sanadin halin danake ganin’yata a ciki kuma bani da ikon magana yarinyar tayi wata irin rayuwa ne mara dad’i mara ma’ana.
Sosai haj. Shamsiyya ta kafe Ammey da ido jikinta yana rawa sosai tace “CIWON ZUCIYA Amina wannan wane irin mugun hali Allah yayi miki na barin abu arai bazaki fitar dashi kiji sanyi ba haba Amina” ta karasa maganar cikin fashewa da kuka sosai, taci gaba da cewa “ashe duk fad’an da nake miki na ki janye ‘yarki bakiyi hakan ba kikayi tasa abu aranki har ya zamar miki ciwo arai, kar kimin haka Amina dan Allah” momma take maganar cikin gurshek’en kuka dan tasan tunda har Ammey ta furta tana da ciwo to abinne ya girmama.
“Ki yafemin dan Allah anty bana son sakaku adamuwa ne banda ke babu wanda yasan ina da ciwon dan Allah kar ki bari su Baffa suji hankalin su zai tashi”
Rungumeta momma tayi cikin tsantsar tashin hankalin da tausayin ‘yar uwar tata yayin da Ammey kuma taci gaba da bawa yayar tata labarin irin rayuwar da maryam tayi tare da irin halin da ta rik’a kasancewa a ciki a duk lokacin da Baffa ya juya mata baya, akarshe kuma dad’a jadaddawa antyn tata take ta kular mata da yaranta idan ta mutu, nan kuma ta kuma bata labarin irin mugun mafarkan da takeyi mara dad’i wanda tasawa ranta akwai abinda wannan makirar matar take shiryawa.
Sosai hankalin haj. Shamsiyya ya tashi amma sai ta danne nata damuwar ta rik’a tausar ‘yar uwar tata har sai da taga ta samu nutsuwa, anan take sanar mata Baffa ya tsaida lokacin auren Maryam d’in da Muhammad, ai kuwa ba k’aramin dad’i hakan yayi mata ba dan ta jima tanayi wa Maryam d’in shi’awar auren MD saboda nutsuwar yaron.
Acan d’akin da su Maryam suka bajakolin hirar su kuwa Fauziyya ce ta dubi Maryam tace “dan Allah sis ki rik’a biyo Ammey kuna zuwa wallahi munji dad’in zuwanki ke d’in fa JININ muce” murmushi Maryam ta sakar mata tace “shikenan sis zan rik’a zuwa dan nima naji dad’in kasancewar mu tare Allah ya bar k’auna.
Acan gida kuwa MD ji yai hankalinsa yayi wajen Maryam kamar ya bita sai dai yana binta Ammey zata gane saboda Maryam ne hakan kawai yasa ya yanke shawaran yakai ma m Bash ziyara.
Kar ku manta Baffa bai sanar da MD maganar aurensa da Maryam ba hakanan haj. Sailuba bata sani ba, bawai kuma saboda wani abu yak’i sanar da ita ba sai dan b’ata masa ran da tayi na barin Ammey ta tafi da maryam d’in alhalin yana son zuwa da ita wajen Inna wanda dama zai jene dan sanar da ita maganar auren Maryam da MD d’in ne.
Ku muje dai masoyana
Ina alfahari daku duk inda kuke a fad’in duniya
MAMAN ISLAM taku ce mai matuk’ar k’aunar ku
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
???? BA JININA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 42
Bayan ya gama shirin sa ya fito cikin k’ananan kayan da suka matuk’ar amsar sa,ya fito yana baza k’amshin sa mai kwantar da zuciya.
Yana sako kai haj. Sailuba na fitowa daga lambum kusa da Pat dinsa cikin wani irin sauri tana wage wage gudun kar wani ya ganta da ganinta ba abin arzik’i ta shuka a wajen ba, wani mugun kallo ya bita dashi cikin tsana sannan ya yaja wani uban tsaki ya shiga lambun dan haka nan yaji yana son ganin meta aikata awajen.
Da kallo ya rika karewa wajen kallo har idanunsa suka sauka kan wajen da aka hak’e da alama wani abun aka bunne awajen, gabansa ne yai mugun fad’uwa ya taka a hankali cikin nutsuwar sa ya karasa yana nazartar wajen kafin yayi Bismillah ya durk’usa dan tsabar saurin da take hatta abin hakar bata d’auke ba ta manta da shi a wajen.