BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 51 to 60 (The End)

A firgice duka suka juyo suka kafeta da ido yanayin sa ba karamin firgita ta yayi ba tayi saurin k’asa da kanta jikinta yana wani irin masifaffen rawa,bata san sanda ya k’arasa kusa da itaba yace adaidai kunnen ta yace “ajiyar ki tananan acikin lambun na bar miki”

A firgice ta d’ago tana kallonsa kafin tayi wani luuuuuu ta zube awajen tsabar tashin hankalin jin abinda yace mata

Plss manage

MAMAN ISLAM CE

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*

FCWA

*Home of qualities and trusted writers of the nation*

https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?type=3&source=45&refid=17

______________________________________

???? *BA JININA BACE* ????

 *2021* 

        NA

 *HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI* 

 *MAMAN ISLAM* 

PAGE 44

Da sauri Maryam ta nufeta, yay saurin tareta yana kallon cikin idonta da kallon kar ki soma.

“Mama nace fa” ta fada a raunane “maman naki ban lamunta ba kibar ta zata tashi ga Ammeyn ki cen ciwon zuciyar ta ya tashi” da sauri ta kafe shi da ido gabanta yana wani irin dokawa tace “ba yanzun muka dawo daga unguwa ba?”

“Eh kinsan al’amarin ubangiji babu yadda baya juyawa bawa kuna shigowa bayan shigewar ki ciki ta yanke jiki ta fad’i, yanzun ma magani zan amso mata na gama dubata.

A hankali ta juya ta kafe mama da wani irin kallon tuhuma da tsoro tace “kece ko?” 

Mama da tun da ta fad’i take wani irin kukan zuci mai azabar radadi tayi saurin girgiza kai, alamun babu ruwanta.

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tare da kwafa ganin yaja hannunta sun fice,. 

“Sai naga bayanka wallahi Muhammad tunda kayi sanadin rusamin shirina saikayi nadamar yin hakan dan haka nice ajalinka wallahi saikayi nadamar shiga rayuwana da kayi” ta mik’e tashige d’aki tana sakin kukan bak’in ciki.

Yanayin da taga Ammey yasa ta k’arasa da sauri ta rungumeta tareda fashewa da kuka tace “Ammeyna me ya sameki daga dawowar mu?

Kodai akanki ne naji mama na waya?”

Kafeta da ido Ammey tayi batare da tace mata komai ba yayin da zuciyar ta yake mata wani irin fitinannen suka, batasan lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba mai mugun cin rai.

Ita ma maryam fashewa tayi da kuka tare da k’ara k’ank’ame Ammey tana fad’in “sannu Ammey yana miki zafi ko zai daina kinji dan Allah ki bar kukan nan haka yana Kona min rai.

Wani mugun kukanne ya kuma taho mata tayi saurin toshe bakinta da hannun ta tana jin wani mugun tausayin Maryam yana kamata, ta sani rayuwar Maryam yana cikin gagarumin matsala, tasan Sailuba tasan wacece ita muguwa ce azzalumar matar da batasan Allah ba babu d’igon tsoron Allah a tareda ita makira ce ta ajin k’arshe bata da imani ko k’ank’ani.

“Maryam kiyi hak’uri da rayuwa ki gyara d’abi’unki duk da kasancewar naga sauyi mai yawan gaske atare da ke, amma ina so kisani rayuwa bashi da tabbas, idan yau mune gobe ba mu bane, dan Allah zan rok’eki duk halin da kika tsinci kanki, ki kasance mai yawan godewa Allah, ki kare Martaba da kimar ki na d’iya mace k””””””””’ya isa dan Allah ya isa Ammey ki daina min irin wannan zantukan masu kama da wasiyya, daga kinyi d’an zazzab’i sai ki kama wasiyya kamar mai shirin barin duniya yanzu yanzu, insha Allah sai kinga jikoki na” ta fad’a cikin matsanan cin rawan jiki ga kukan da take ya kasa tsayawa tsabar tashin hankalin da kalaman Ammey suka saka ta a ciki.

Wani irin murmushi tayi mai ciwo sannan hawayen ta basu bar zuba ba, sannan bata fasa yiwa Maryam nasiha ba akan rayuwa da zaman takwar mutane tare da fad’a mata yau da gobe kai ranan dai babu wani jin dad’i a wannan gida.

Acan k’auye kuwa bayan Baffa ya isa ba k’aramin farin ciki Inna tayi da ganin tilon d’an nata ba, sai dai shi kad’an sa ta ganshi babu maryam kamar yadda yadda ta buk’ata, hakan bai wani bata mamaki ba tunda tafi kowa sanin halin Sailuba “kai wannan yarinya Allah dai ya shirya, Allah kanaji kuma kana gani na fita hakkinta na bata tarbiyya gwargwadon iyawa ta Allah karka kamani da laifin gurbacewar halinta dan alfarmar fiyayyen haltta (S A W).

Nan falon ta tayi masa shimfida ya zauna takawo masa ruwan randa mai sanyi da fura wacce taji lafiyayyan nonon shanu zuryan, kasan cewar tasan da zuwan sa.

Sai da suka gama gaisawa sannan ya soma furar kasancewar yana sonta sosai yana sha suna d’an tab’a hirar duniya da Inna wanda duk rabin sa nasiha ne da shawarwari cikin hikima.

Bayan ya kammala ne ta dubeshi tace “kaje kasamu kawun Muhammadu dan a tsaida daidai lokacin da za a d’aura auren Maryama da shi Muhammadun dan insha Allahu jibinnan za’ayi babu jinkir tawa”

Da sauri Baffa ya dubeta yace “jibi kuma Inna?” 

K

“Ko ban isa zartar da hukunci akan jika ta bane?”

“A haba Inna kin isa har kinyi yawa”

“To katashi kaje ka dawo kazo ka amshi naka iv da zaka rabawa ‘yan uwa da abokan arzik’i, saboda nasan shiriri tarka shiyasa nasa aka buga har kai, sannan magana tagaba Baffa koda wasa Sailuba kar tasan jibi daurin auren Maryama domin na fahimci ita d’in fitina ce arayuwar Maryama, kai wannan yarinya Allah dai ya ganar da ita”

Daga Baffa ya fita zuwa gurin yan uwan marigayi aminin shi Hassan

MAMAN ISLAM CE

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*

FCWA

*Home of qualities and trusted writers of the nation*

https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?type=3&source=45&refid=17

______________________________________

???? *BA JININA BACE* ????

 *2021* 

        NA

 *HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI* 

 *MAMAN ISLAM* 

PAGE 44

Da sauri Maryam ta nufeta, yay saurin tareta yana kallon cikin idonta da kallon kar ki soma.

“Mama nace fa” ta fada a raunane “maman naki ban lamunta ba kibar ta zata tashi ga Ammeyn ki cen ciwon zuciyar ta ya tashi” da sauri ta kafe shi da ido gabanta yana wani irin dokawa tace “ba yanzun muka dawo daga unguwa ba?”

“Eh kinsan al’amarin ubangiji babu yadda baya juyawa bawa kuna shigowa bayan shigewar ki ciki ta yanke jiki ta fad’i, yanzun ma magani zan amso mata na gama dubata.

A hankali ta juya ta kafe mama da wani irin kallon tuhuma da tsoro tace “kece ko?” 

Mama da tun da ta fad’i take wani irin kukan zuci mai azabar radadi tayi saurin girgiza kai, alamun babu ruwanta.

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tare da kwafa ganin yaja hannunta sun fice,. 

“Sai naga bayanka wallahi Muhammad tunda kayi sanadin rusamin shirina saikayi nadamar yin hakan dan haka nice ajalinka wallahi saikayi nadamar shiga rayuwana da kayi” ta mik’e tashige d’aki tana sakin kukan bak’in ciki.

Yanayin da taga Ammey yasa ta k’arasa da sauri ta rungumeta tareda fashewa da kuka tace “Ammeyna me ya sameki daga dawowar mu?

Kodai akanki ne naji mama na waya?”

Kafeta da ido Ammey tayi batare da tace mata komai ba yayin da zuciyar ta yake mata wani irin fitinannen suka, batasan lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba mai mugun cin rai.

Ita ma maryam fashewa tayi da kuka tare da k’ara k’ank’ame Ammey tana fad’in “sannu Ammey yana miki zafi ko zai daina kinji dan Allah ki bar kukan nan haka yana Kona min rai.

Wani mugun kukanne ya kuma taho mata tayi saurin toshe bakinta da hannun ta tana jin wani mugun tausayin Maryam yana kamata, ta sani rayuwar Maryam yana cikin gagarumin matsala, tasan Sailuba tasan wacece ita muguwa ce azzalumar matar da batasan Allah ba babu d’igon tsoron Allah a tareda ita makira ce ta ajin k’arshe bata da imani ko k’ank’ani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button