BA JINI NA BA CE 1-END

BA JINI NA BA CE Page 51 to 60 (The End)

“Maryam kiyi hak’uri da rayuwa ki gyara d’abi’unki duk da kasancewar naga sauyi mai yawan gaske atare da ke, amma ina so kisani rayuwa bashi da tabbas, idan yau mune gobe ba mu bane, dan Allah zan rok’eki duk halin da kika tsinci kanki, ki kasance mai yawan godewa Allah, ki kare Martaba da kimar ki na d’iya mace k””””””””’ya isa dan Allah ya isa Ammey ki daina min irin wannan zantukan masu kama da wasiyya, daga kinyi d’an zazzab’i sai ki kama wasiyya kamar mai shirin barin duniya yanzu yanzu, insha Allah sai kinga jikoki na” ta fad’a cikin matsanan cin rawan jiki ga kukan da take ya kasa tsayawa tsabar tashin hankalin da kalaman Ammey suka saka ta a ciki.

Wani irin murmushi tayi mai ciwo sannan hawayen ta basu bar zuba ba, sannan bata fasa yiwa Maryam nasiha ba akan rayuwa da zaman takwar mutane tare da fad’a mata yau da gobe kai ranan dai babu wani jin dad’i a wannan gida.

Acan k’auye kuwa bayan Baffa ya isa ba k’aramin farin ciki Inna tayi da ganin tilon d’an nata ba, sai dai shi kad’an sa ta ganshi babu maryam kamar yadda yadda ta buk’ata, hakan bai wani bata mamaki ba tunda tafi kowa sanin halin Sailuba “kai wannan yarinya Allah dai ya shirya, Allah kanaji kuma kana gani na fita hakkinta na bata tarbiyya gwargwadon iyawa ta Allah karka kamani da laifin gurbacewar halinta dan alfarmar fiyayyen haltta (S A W).

Nan falon ta tayi masa shimfida ya zauna takawo masa ruwan randa mai sanyi da fura wacce taji lafiyayyan nonon shanu zuryan, kasan cewar tasan da zuwan sa.

Sai da suka gama gaisawa sannan ya soma furar kasancewar yana sonta sosai yana sha suna d’an tab’a hirar duniya da Inna wanda duk rabin sa nasiha ne da shawarwari cikin hikima.

Bayan ya kammala ne ta dubeshi tace “kaje kasamu kawun Muhammadu dan a tsaida daidai lokacin da za a d’aura auren Maryama da shi Muhammadun dan insha Allahu jibinnan za’ayi babu jinkir tawa”

Da sauri Baffa ya dubeta yace “jibi kuma Inna?” 

K

“Ko ban isa zartar da hukunci akan jika ta bane?”

“A haba Inna kin isa har kinyi yawa”

“To katashi kaje ka dawo kazo ka amshi naka iv da zaka rabawa ‘yan uwa da abokan arzik’i, saboda nasan shiriri tarka shiyasa nasa aka buga har kai, sannan magana tagaba Baffa koda wasa Sailuba kar tasan jibi daurin auren Maryama domin na fahimci ita d’in fitina ce arayuwar Maryama, kai wannan yarinya Allah dai ya ganar da ita”

Daga Baffa ya fita zuwa gurin yan uwan marigayi aminin shi Hassan

MAMAN ISLAM CE

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*

FCWA

*Home of qualities and trusted writers of the nation*

https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?type=3&source=45&refid=17

______________________________________

???? *BA JININA BACE* ????

 *2021* 

  

        NA

 *HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI* 

 *MAMAN ISLAM* 

Masha Allah kungiyata kungiyar albarka ce kungiyar da babu irin ta d’aya tamkar da dubu ina matuk’ar alfahari da first class tare da dukkan ‘yan uwa masoya na cikin ta Allah ya k’ara had’e kanmu

Allah sarki islamiyya ta Allah ya k’ara shiryamin ke ya sanya miki nutsuwa da jin tsoron sa Allah ya tsarkake min zuciyar ki tareda kullum yayan musulmi baki d’aya

D’an auta na Al’mustapha d’an rikici na yanzun an girma ya kamata a daina rigimar banza da wofi.

PAGE 45

Bai wani jima ba ya dawo haka ma Inna yana dawowa tace ya koma gida yaci gaba da shiryen sa ita tagama nata haka nan gobe zata iso da tawagar ta, sannan ta kawo wani rubutu ta bashi tace yana shiga get d’in gidan sa kafin yakai ciki yayi Bismillah ya sha daga tsaye, ta jaddada masa hakan sau ba adadi har ya daga yana mamakin wannan wane irin rubutu ne me muhimmanci haka.

Sanda ya isa sai da yafara zuwa gidan malam lokacin yana tare da bak’i ganin Baffa yasa ya sallami bakin yace “k’araso mana Baffa kamar wani bak’o zaka tsaya daga nesa”.

K’arasa wa yay yana d’an murmushi yace “barka da yamma malam”

Yauwa Baffa, ya kuma na ganka fasa zuwa wajen Innan kayi?”

“Naje malam sai dai bata barni na kwana ba saboda tace auren Maryam jibi ne, gama iv ta bayar wai araba tun yau tunda abin ya kure”.

Cikin madaukakin farin ciki malam yace ” a a to Abu yayi kyau gaskiya naji dad’in hakan sosai Allah ya tabbatar mana da alkhairi” amen amen sun dan jima da malam suna tattaunawa kafin ya sallame shi ya taho gida.

Kafin ya shiga gid saida ya kira Halima dake yar abokansa ce Kuma makocin sa na amana yabata iv na daurin auren masu dan dama yace ta kaiwa Abban ta sannan ya bata na ‘yan mata yace dan Allah yau ta fara rabawa k’awayen saboda Maryam bata nan su sosai tayi mamakin auren na Maryam yadda yazo musu babu shiri yadda sukaci burin wannan ranar, take ta kira Maryam k’awar Maryam ta jami’a suka sha mamakin su kafin su sannan suka fara rabo tunda lokaci ya riga da ya k’ure.

Wannan tsaye tsaye da Baffa yayi shi yasa ya manta da rubutun da Inna tace lallai lallai yasha kafin ya shiga gida

Dake yau Ammey ce da girki kuma yasan yadda suka rabu akan sai anbata ‘yarta dan haka d’akin ta ya fara nufa sai dai yadda ya tadda ita ba k’aramin d’aga masa hankali yayi ba ya k’arasa kusa da ita yana tambayar Maryam abinda ya faru shida ya fita basa nan.

Cikin kuka tace itama bata sani ba bayan sun dawo MD ya kirata yace tazo ta kula da ita kafin ya kawo magani, daga haka ta fice ganin yadda Ammey take kalloan Baffa tasan akwai abinda take son fad’a masa.

Tana fita sukayi kicibus da MD wanda da k’yar ya samu maganin da Ammey take sha yace “ya kika fito?”

“Baffa ya dawo yana ciki”

Da mamaki yake kallon ta yace “bai kwana ba?”

“Inaga ya fasa ne”

Ta bashi amsa tana wucewa ciki saboda jin ana kiran sallar isaha, dan haka shima ya nufi part d’insa dan yayi tasa alwalar dan kar ya rasa jam i.

A b’angaren Mama kuwa tunda ta shiga d’aki ta kasa nutsuwa sai zarya take daga k’arshe ma kai tsaye bokanta ta kira ba aminiyar tata ba ta sanar masa duk halin da ake ciki,

Yace “kin lalata komai Sailuba dole ne abinda kike gudu zai faru, sannan bazaki samu komai da kike buk’ata ba, idan kina son cikar burinki dole ne kizo nan mu kadaice dake na kwana biyu dole nayi kwana biyu ina saduwa dake da wannan maniyin da zai fita a jikin ki zan miki aikin da zai baki mamaki bayan haka banida wata hanya ta samun nasarar ki”.

Idanunta ya rufe,

Zuciyar ta ya toshe

Tunanin ta ya b’ace

Imanin ta ya barta

Bata da wani buri ko fata illah tarwatsa rayuwar yarinyar da babu abinda tayi mata wanda ya wuce yi mata biyayya da gwada mata k’auna irin na uwa mahaifiya da ‘ya mai mutukar biyayya agareta. 

Hakkan ne yasa Baffa yana shigowa ta fice dan boka yace kar ta bari su had’u dama dakon dawowar sa take wannan kenan.

Bayan Maryam ta idar da sallar tana shirin komawa b’angaren Ammey kiran name sake d’in ta ya shigo wayar ta ta d’aga tana fad’in ‘yar halak wallahi jikin Ammey ne ya hanani kiranki”

“Eh kyace haka mana saboda rainin hankalin da kika saba, yanzu sahiba ace jibi jubi daurin auren ki amma sai yau muke sani kin kyauta ai”

Dakatar da ita Maryam tayi ta hanyar cewa ” dake yar tsana ce ni shiyasa aurena zai kasance jibi har na kasa sani, ko shirin film ko kuma a littafi wanda suke shirya abu nan take”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button