BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 29

29

……..“Sannu da zuwa Yaya”. Ta faɗa har yanzu mamaki shimfiɗe akan fuskarta. Idanunsa ya ɗauke daga kanta batare daya amsa ba duk da ba gane hakan ake ba saboda idanun nasa na sakeye a cikin gilashi. Taji haushin yanda yay mata ɗin, sai dai yanayin tsukewar fuskarsa ya sata jin shakka da ƙara ganin kwarjini da fresh daya ƙaro. Muzzaffar ya ƙaraso wajen fuskarsa da murmushi shima yana masa sannu da zuwa.

Shima ɗin akan laɓɓa ya amsa masa, koda ya miƙo masa hannu dan suyi musabaha kuma kamar bazai karɓa masa ba, sai kuma ya miƙa nasa shima da ƙyar. Anam ta taɓe baki cikin takaicin shan ƙamshin nasa tana kallon Khaleel da shima yanayin Yayan nasu ya sashi kama kansa, sai dai a ƙasan ransa yana mamakin komawarsa haka dan cikin nishaɗi da farin ciki suka baro gidansu daya fara sauka, kuma da farin cikin ya ɗakkosa a airport.
        Dai-dai suna shigewa ya zare gilashin fuskarsa ya watsa mata wani shegen kallo mai cike da gargaɗi ya wuce. Tai tsamm a waje ɗaya zuciyarta na bugawa da dauri-sauri, amma dan ƙarfin hali sai ta murguɗa masa baki. Muzzaffar kam da kallo ya bisa yana sakin murmushi zuciyarsa na cuɗa masa abubuwa daban-daban duk da ba yaune karon farko daya fahimci wasu abubuwa a idanun Shareff ɗin ba. Numfashi ya sauke a hankali yana nuna mata suje. Itama ajiyar zuciya ta sauke a hankali, jiki a sanyaye ta bisa suka koma wajen zamansu.

       A ciki Aysha da ke kitchen tana girkin dare ita da mai-aiki ce ta fara leƙowa saboda jin sallamar Khaleel, ta wani zaro ido waje da sakin ihun murnar daya saka Fadwa fitowa zumut daga bedroom. Itama idanu ta zaro na mamaki, dan sam bata san da batun dawowar mijin nata ba. Ya ALLAH, ai tama manta da kowa na falon ta fasa ihun murna da kwasowa da gudunta garesa. Baiƙi bata dama ba, dan shima yayi missing ɗinta, ya ware mata hannaye tako shige jikinsa tare da ɗanesa.


     Dariya Khaleel ya saki yana kauda kansa gefe, hakama Aysha da gudu ta koma kitchen tana dariya ita da mai aiki. Acan waje kuwa Muzzaffar ƙoƙarin yima Anam hira yake yi cike da kulawa amma sam sai ya fahimci hankalinta baya tare da shi, yay murmushi da miƙewa yana faɗin, “Bara na barki madam gobe idan ALLAH ya kaimu da dare maybe zan shigo sai mu ƙarasa, ya kamata kije kema ayi murnar dawowar Yayan dake”.
      Murmushin yaƙe ta ɗan masa, dan duk suna jiyo ihun Fadwa. Ya miƙa mata ledar da yazo da shi tare da mata bye-bye. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali lokacin daya fice a gate ɗin baki ɗaya, ta ɗan kalla ledar daya bata sannan ta nufi ciki. Har shigowarta Fadwa na ɗane jikinsa, ya wani rungumesa tsam tana hawaye da faɗin wai tayi missing ɗinsa. Sosai ƙirjinta ya ƙara ƙarfin bugun da yakeyi, tai azamar dafe kujera dan jitai kanta ya fara juya mata kamar maijin hajijiya, amma sai tai matuƙar dakewa fuskarta

ƙawace da murmushi. Shi kaɗai da idanunsa ke a ƙofar dama ya ganta, ya sauke sassanyar ajiyar zuciya da har sai da Fadwa taji, cikin jin daɗi ta ƙara maƙalƙalesa tana raɗa masa yanda tai tsananin kewarsa a cikin kunensa. Karon farko tun shigowarsa falon ya saki siririyar dariya, a hankali ya ɗan kaima wiyanta sumbata idanunsa na kallon Anam ƙasa-ƙasa. Sai akai sa’a itama dai-dai ta ɗago nata idanun da hasken cikinsu

gaba ɗaya ya kore duk da a cikin gilashi suke. Ɗauke idanunta tai tana taɓe baki da juyasu cikin salon ko’a jikina. Numfashi mai ɗaci ya saki da ƙoƙarin dakatar da Fadwa dake ɗan jan hanunsa.
       “Shiiii!!”
    Ya faɗa cikin wani salo yana ɗaura yatsansa akan bakinta da kashe mata ido ɗaya wanda komai ya ƙara faruwa akan idon Anam data ɗago. Wayarta dake ring ta ɗaga da kaiwa kunenta ta sakin murmushi da ajiye ledar hanunta ta nufi hanyar bedroom ɗinsu cikin ƴar sassarfa.


     Khaleel da sai yanzu ya lura da ita ya ƙara sakin ƴar dariya dan duk zatonsa shi kunyace itama ta sakata yin hakan. Ledar data ajiye a wajen ya ɗauka yana faɗin, “Ƴar ficikar nan mi kika samo mana haka ne?”. Maganar tasa ce ta saka Fadwa saurin juyowa dan itama bataga Anam ɗin ba, a yanzu kuma har ta shige abunta. Ta buɗe baki zatai magana Aysha ta fito daga kitchen ɗauke da tray. Kai tsaye gaban Shareff da yakai zaune cikin kujera ta dire.
     “Yayanmu sannu da zuwa kazo lafiya? Ya hanya?”.


   Kanta ya shafa kawai batare da yace komai ba. Hakan ya sakata sakin murmushin jin daɗi, ruwan data tsiyaya a kofi ta miƙa masa. Ya karɓa idonsa akan Fadwa da ita sam bata da niyyar hakan ma a garesa… Khaleel daya fahimci kallon da Shareff ɗin yay mata ya dubeta shima. “Madam kina tsaye Aysha ta kwashe ladan daya kamata ki samu, anya kuwa bazamu ƙaro amarya ba a gidan nan dan ba’ai mana tarbar data dace ba”.


      Har ƙasan zuciya maganar Khaleel ta soki Fadwa, ta kalli Shareff dake shan ruwansa tamkar baya jinsu dan hankalinsa na kan tv ne, kallonta ta maida ga Khaleel cikin haɗe fuska. “Yaya Khaleel wane fatan tsiyane wannan dan ALLAH da yammacin nan?”.


         Zama yay yana faɗin, “Naga kamar haka ya kamata muyi ne ai hajjaju, idan kuma baki son amarya sai ki gyara kurenki da wuri”. Da gaske magana ya faɗa mata a kaikaice, amma kuma cikin wasa da murmushi Aysha na tayasa da dariya. Hararar Khaleel ɗin tayi, a karo na farko taji tsanarsa, sai dai batace komai ba taje kusa da mijinta ta zauna fuska a ɗaure. Kofin hanunsa ya ajiye yana miƙewa, bedroom ɗinta ya nufa yana faɗin, “Haɗamin ruwan wanka, ke kuma Aysha kuje ku gyaramin side ɗina”.
      “To Yaya”.


Aysha ta amsa cike da girmamawa. Matar gidan kam takaicin Khaleel ya hanata amsawar, sai dai ta miƙe cike da isa tana gallama Khaleel ɗin harara tabi bayansa. Daga Aysha har Khaleel sunga harar, tana shigewa Aysha tai dariya. “Yaya Khaleel ka sakama Aunty Fadwa jin haushin maganarka fa”. Cikin halin ko’in kula ya ɗage kafaɗa da taɓe bakinsa irin I don’t care ɗin nan. Ƴar dariya Aysha ta ƙara saki da mikewa zata nufi waje dan kiran Anam ya sanar mata tana ciki ta shigo…


        “Tabbas na kusa fara shukama Khaleel rashin mutunci a gidan nan in har yana min wannan maganar banzar”. Ta faɗa a fusace tana shigowa ɗakin, dai-dai Shareff na ajiye agogonsa daya cire saman mirror ɗinta idonsa akan wayarta dake maƙale a ɗan sama. Video take ɗauka zatai posting a tiktok ihun Aysha ya sakata fita, ALLAH yasota wayar ta gaji ta rufe kanta. Jin bai tanka mata ba ta ƙara maimaita abinda ta faɗa tana kallonsa. Yanzu dai ya juyo ya kalleta sai dai baice komai ba ya ɗauke kansa yana ƙoƙarin jan necktie ɗin wuyansa.


      “Soulmate kanaji fa ina magana”. Ta faɗa a shagwaɓe da rungumesa ta baya. Kamar bazai tanka mata ba, sai kuma a taƙaice yace, “Miye nawa, maganarku ce”.
      “Hakama zakace?”.
   Ta faɗa tana juyowa gabansa. Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe akan lips ɗinta, sai kuma yay ƙoƙarin kaudawa amma ta riƙo fuskar tasa, bai samu damar cewa wani abuba ya haɗe bakinsu…..

        Aysha ko koda ta shiga ɗaki sai ta samu Anam duƙunƙune cikin bargo, tana taɓata taji zafi sosai a jikin nata zazzaɓinta ya dawo. Sannu tai mata, ta maida mata bargon ta lulluɓa mata. Ita kaɗai taje tai gyaran, hakan ya sata jan lokaci bata gama ba duk da babu datti sosai saboda sukan gyara lokaci-lokaci. Tana cikin saka turare Shareff ya shigo sanye cikin jallabiya fara tas. Sannu ta masa, ya amsa mata da kai yana bin falon da kallo. Baiyi magana ba dan komai ya masa yanda yake so, ya wuce bedroom ɗinsa baifi mintuna uku ba ya fito ya sake ficewa. Itama kammalawa tai a gurguje ta fito dan kiraye-kirayen salla aketayi.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button